*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_**_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*
*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*
*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*
*ALBISHIRINKU KANAWA*
*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*
_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_
*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*
*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*
*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*
08033990209
*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽
Page 51
..................Gidan duk ya ajiye ƙananun ƙura, duk da ko'ina a rufe yake, haka na daure naɗan gyara ɗakinsa dan mu samu inda zamu kwanta, kafin a kira sallar magriba na kammala, shikam wanka ma yayi ya fita tun fara aikin nawa. Bai dawo gidanba har saida akai sallar isha'i, kusan tara sai gashi ya dawo mana da abinda zamuci. Gaba ɗaya banajin daɗin yanayinsa, ya koma min Boss ɗin dana sani a office mara walwala da yawan magana, komai nake sai dai yayta bina da ido kawai, abincinma da ƙyar na samu yaɗan ci yace ya ishesa, nima cire hannuna nai a ciki na ɗauke kaina gefe. “Miye hakan?”. Ya faɗa muryarsa can ƙasan maƙoshi. Ƙoƙarin miƙewa nai tsaye nace, “Na ƙoshi nima...” kafinma na gama rufe bakina naji caraf ya cafko hannuna ya maidoni ya zaunar, kallonsa nai ina kumbura fuska, ya zabgamin harara tamakar idanunsa zasu faɗo ƙasa, “Ina wasa da ke ko?”. Ƙasa nai da kaina dan bazan juri kallon nasaba, “ALLAH nima na ƙoshi to”. Banza yaymin bai tanka ba, ya ɗebo ya kawo bakina, zan ɗauke kaina yay saurin faɗin, “Kinsan ALLAH idan baki shiga hankalinki ba sai na sauya miki kamanin wannan fuskar taki, malama haa”. Idanuna cike da ƙwala na buɗe bakin, ya ko zubamin yana sake zabgamin harara da yin ƙwafa, inaji ina gani yaymin ɗurar dole, shiko yaƙi ya ci, sai yogurt yaɗan sha, hakanne yasa naɗan samu kwanciyar hankali. Kasancewar a gajiye muke ga mai gayya mai aikin baya tare da walwala, gashi zamu koma aiki gobe idan ALLAH ya kaimu sai mukai kwanciyarmu da wuri.
WASHE GARI
Tun kiran sallar farko na tashi, cikin sanɗa na fita daga ɗakin nasa, kasancewar barcin da muka kwanta da wuri sai na tashi jikina babu nauyi sosai, da wannan damar na fara rage aiki. Koda ya fito zai tafi massallaci ya ga ina aikin gyaran babban falo baice dani komaiba ya fice abinsa, ajiyewa nai nima na koma ɗaki nai salla, ina idarwa ban hutaba na sake fitowa na cigaba, ana idar da salla shima bayan wasu ƴan mintuna sai gashi ya dawo, bayan mun gaisa shima sai ya cire jallabiyar jikinsa ya shiga tayani aikin. Duk da na roƙesa ya bari zan ƙarasa tunda na kusa bai saurareni ba, sai da yaga ya rage bedroom ɗina kawai sannan ya barni na ƙarasa.
Ƙurar dana gani tasa nake sharo har ƙarƙashin gado kamar yanda nayi a ɗakinsa da ƙarƙashin kujerun falo ma, abu na sharo a ƙarƙashin gadon, wanda ya sakani dakatawa da sharan nasaka hannu na ida jawosa dan naga minene, wallet ce ƴar karama dan bata kai girman normal wallet dana sani ba, kamar zan buɗe sai kuma na ajiye da tunanin ko tashice, saman mirror na ɗaurata na cigaba da sharan harna kammala komai, ganin lokaci yaja na shiga bayi dan yin wanka sauri-sauri, ban wani ɓata lokaciba na fito. Idanuna ne suka sake sauka akan wallet ɗin nan, duk yanda naso na share a yanzun sai na kasa hakan, na matsa gaban mirror ɗin ina goge fuskata da ƙaramin towel dake a hannuna da hannun haggu, na damar kuma sai na fara ƙoƙarin buɗe wallet ɗin, ɗan ƙaramin hoton dana fara cin karo da shine ya sakani shiga mamaki, na fara fiddo abubuwan cikin wallet ɗin gaba ɗaya, ƙirjina sai wani irin mahaukacin bugawa ya keyi, banma san lokacin dana saki towel ɗin hannun nawa ba jiki na rawa, harda zufa ta fara tararmin a goshi, nagama zazzage komai a ciki, abubuwane masu muhimmanci da daraja dana san maisu bazai taɓa sakaci dasu ba da har zan gansu anan, to wama ya kawosu? Ni dai babu wanda ya taɓa zuwamin nan gidan a kaf mutanen gidan balle nace a mistake wani yazo da su. A fili nace, “To kodai boss ne ya kawo?”. Wannan tambaya na yitane badan zuciyata ta gamsu da ita ba, Duk da sallamarsa da naji a bayana ban iya na waiga ba.
Ƙarasowa yay yana ɓata fuska ganin bama ta shirya ba, ya ajiye ƙaramin tiren da ya ɗoro musu tea a saman table kafin ya ƙaraso inda take yana jan tsaki. Ganin ko motsi bataiba har yanzu tanata juya abu a hannu sai kansa ya sake ɗaurewa, “Wai kina kallon agogo kuwa Miemaa!?”. Ya faɗa a ƙausashe. Ɗagowa nai ina kallonsa, cikin rawar baki da fargabar amsar dazan iya samu nace, “Dan ALLAH kaine ka kawo wallet ɗin nan ɗakin nan?”.
Baice komaiba ya tako gabana tare da riƙo hannuna duka biyu yana kallon abinda ke ciki, cards ne masu muhimmancin gaske, ga sunan maisu kuma ɓaro-ɓaro a jiki da hotunan sa, “Ina kika ganta ke?”. Gado na nuna masa batare da nayi magana ba, ya kafe hannayena da nake sake jujjuya cards ɗin ƙo ƙyaftawa bayayi, nikam ƙirjina sake bugawa ya keyi da sauri-sauri, jira kawai nakeyi yace wani abu, amma yaƙi cewar. Hawaye suka sulalomin ina mai fatan kar abinda keta zomin arai ya kasance hakane, kai banama fatan hakan, sai dai idan anason min yawo da hankaline dan a ɓata masa suna. Muryata na rawar kuka nace, “Kace wani abu dan ALLAH boss”. Kansa kawai ya girgizamin yana mai cije leɓensa na ƙasa, ya saka hannu ya amshi komai dake hannuna ya maida a wallet ɗin ya sakata aljihu, taimakamin yay na shirya ina hawaye, wata gigitacciyar tsawa data nema haukatani ya dakamin, “Ke komai kuku! kuka!! kuka!!!, komai abin kukane a gareki, ya isheni haka banason ji kuma, malama ki sharemin waɗanan banzayen hawayen kafin nai miki bugun kayan wanki wlhy a gidan nan!!!”. Na matuƙar tsorata da yanayinsa, na koma jikin madubi na maƙure ina ƙoƙarin haɗiye kukan, gaba ɗaya kamanninsa sun masifar sauyawa, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, baice dani komaiba ya juya ya fice daga ɗakin. Sake fashewa nai da kuka ina faɗin, “Ya ALLAH ka bani haske akan wannan al'amarin”. ƙarar takunsa dana jiyo ya sakani saurin goge hawayen na juya ina saurin ɗaukar soson hoda nahau shafawa. Bayana yazo ya tsaya yace, “Agogon wanene wannan?”. Da sauri na juyo gabana na faɗuwa na zubama hannunsa idanu, kusan mintuna biyu na ɗago na kallesa, Kaina na girgiza masa alamar ban sani ba. “Kin tabbata?”. Na ƙara ɗaga masa kaina. Bai sake cewa komai ba ya koma bakin gado ya zauna tare da ɗaukar kofin tea ɗaya ya fara sha yana cigaba da kallon agogon kafin ya ajiyesa gefensa. Ganin ya kafeni da idanu nai sourin ƙarasa kimtsawa zuciyata nata kaikawo da tunane-tunane kala-kala waɗanda gaba ɗaya sake zurma zuciyata suke a firgici. Tea ɗin ya ɗauka ya miƙamin, babu musu na amsa dan a yanda yake ɗinnan zai iya mammakeni idan nai masa gardama. Ni nafara fita daga ɗakin nakai kofunan kicin na ɗauraye da sauri-sauri na fito, a falo na iskesa jikkata na gefensa ajiye. Ɗauka nai tare da briefcase ɗinsa, baice dani komaiba nai gaba ya bini a baya, shine ya kulle ƙofar sannan muka ƙarisa inda Sadiq ya goge motar ƙal yana jiran fitowarmu shi da maigadi, mun gaisa dasu cike da girmamawa, suka buɗe mana motar muka shiga bayan kowannenmu ya karanto addu'ar fita daga gida.

VOUS LISEZ
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...