Page 18
...............“Wannan shine kuskure mafi girman da zaki aikata a rayuwarki inhar hannunki ya sauka kanta!!”.
Kakkausan furuci daya karaɗe illahirin office ɗin da kunnuwan Rose kenan a lokacin da hannunta ke gab da kaiwa jikin Bilkisu da batasan Rose ɗin na kantaba ma, dan barci take cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, harma ta manta a inda take kwance.
A firgice Rose ta janye hannunta tare da ɗago idanunta da juyowa domin tabbatar da abinda take zato, ilai kuwa shine fuska a murtuke babu alamar wasa tattare dashi balle sassauci, ya saki hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa yana cigaba da watsa mata wani mugun kallon daketa tsitstsinke jijiyoyin jikinta da hanjin cikinta, “Mi kike shirin yi da?” ya faɗa muryarsa cike da tsanarta irin wadda bata taɓa ganiba a gareshi. Da ƙyar Rose ta haɗiye ɗan yawun data tattaro a maƙoshinta, tace, “Ni babu abinda zanyi, kawai dai na shigone na ganta anan kwance____” “Shine zaki tada ita saboda a kanki take kwance?”. Yay saurin ƙarasa mata zancen data ɗakko yana tsatstsareta da idanu. Fuska ta sake tsukewa cikin tsananin kishi tace, “Ni wlhy yarinyarnan batai minba”. Wani banzan kallo sama da ƙasa yay mata ya ɗauke kansa yana faɗin, “Saiki kasheta ai”. Kamar zatai kuka tace, “Amma boss wai miye haɗinka da ƙwailar yarinyarnan? dako mace bata gama zamaba ma”. Tsaki yayi ya juya zaibar wajen yana faɗin, “Duk abinda ke ranki shine tsakaninmu, kozaki hana?”. Tamkar rose zata fasa kuka tabishi da kallo, yana zama Su Hafiz na shigowa da sallama, hannun Aliyu ɗauke da leda mai tambarin gidan abinci, duk kallon Rose sukai ganinta tsaye tamkar gunki tana kallon Jawaad da tamkarma baisan da itaba, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure alamun zuciyar na kusa, mai tsautsayi ya taɓa a fashe masa ita. Hafiz ne ya fara janye idanunsa daga kan Rose ya sauke akan Bilkisu dake kwance tana barcinta lulluɓe da rigar Jay, har yanzu ko motsi bataiba dukda ihun da yayma Rose ɗazun, kafin suma su Jabeer su lura da ita. Babu wanda yace komai a cikinsu, shi kuma Jay baiko ɗago yama kallesuba balle su saran zai tanka.
Aliyu ya matsa inda Jay yake ya ajiye ledar yana faɗin, “Ga abinci, kasa munje munata jiranka a wajen ashe kai kanama nan ka manta damu Boss”. Ɗago ido Jay yay fuska a yatsine ya harari Aliyu batare da yace komaiba, shi dai Aliyu zama yay abinsa bai kulashiba, Jabeer ma yaja kujerar kusa da Aliyu ya zauna yana haɗiye dariyarsa, dan ya lura Rose suman tsaye tayi a wajen kokuma ta samu gushewar hankaline na wasu mintoci.
Hafiz yay guntun tsaki yana harar Rose, “Ke kuma lafiya kika wani tsaya ƙiƙam kamar wata dogariya?”. Numfashi Rose ta kawo cikin dawowa hayyacinta, ta watsama Hafiz harara kafin ta nufi ƙofar fita batare data tankama kowa a cikinsu ba, jikinta sai rawa yakeyi. Tana fita Jabeer ya kwashe da dariya, duka Hafiz yakai masa ya duƙe, Jay ya galla masa harara da faɗin, “Dilla malam miye haka?”. “Me nayi ni?” cewar Jabeer dake rama harar da Jay yay masa, ya cigaba da faɗin, “Kai ka dace da wannan tambayar baniba boss, sai neman haukatar da yaran mutane kake kana wani cijewa, gwara idan son yarinyarnan kake kafito ka sanarma duniya ka kuma shiga cikin ƴan takara ko Rose ta dawo hankalinta, kuma ka kwana da sanin Qaseem son yarinyarnan yake, yasin ka tsaya kallon ruwa ƙwaɗone zaima ƙafa, saboda gida ɗaya suke kwana suna tashi, dan a ruwa kake kusa da kada malam”. A fusace Jay da dama kaɗan yake jira ya miƙe, ƙofa ya nunama Jabeer yana huci, “Tashi ka fita a office ɗinan Jabeer kafin nama rashin mutuncin da bazaka taɓa mantawaba, banason wasan banza kaima ka sani ko”. Miƙewa Jabeer yay yana taɓe baki, yasan fitar tasa shine mafi alkairi dan Jawaad a wuya yake, shikuma idan yay zuciyar da har ɓacinta ya fito a muryarsa kai nesa dashi yafi komai alkairi, idan ya huce da kansa zai nemeka yay maka bayani harma daban haƙuri idan yasan yamaka abinda bai daceba. Ficewa Jabeer yay yana murmushi da girgiza kai. Jawaad ya koma ya zauna yana ƙwafa, sai kuma ya miƙe ya nufi toilet yabar su Hafiz dake binsa da kallo.
A sanyaye Aliyu yace, “Sonta yake amma kamar shima bai fahimci hakaba Hafiz”. Cikin damuwa Hafiz ya bama Aliyu amsa da cewar, “Na daɗe da fahimtar haka Aliy, ba fahimtace baiyiba kuma shima, sarƙaƙiyar dake cikin al'amarin yarinyarne yake sakashi ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai kuskuren daya kasa tunawa shine, ba kowanne irin SO bane yake haɗiyuwa lokacin da ake buƙata, wani koda ka korashi da ruwan haƙuri dana juriya a maƙoshi yake tsayawa ya tsaida dukkanin muhimman al'amuranka wucewa cikin zuciya da ƙwaƙwalwa, ni kaina na waiga ta kowacce kusurwa bashi da wani magoyin baya akan al'amarin yarinyarnan sai sashe ɗaya, shi kuma baida wani ƙarfin iko akan hakan”. ajiyar zuciya Aliyu ya sauke mai ƙarfi yana dafe kansa, sai kuma ya ɗago ya kalli Hafiz dake kallon inda Bilkisu take, yace, “Minene mafita yanzu Hafiz? Jay yana buƙatar mace a kusa dashi sosai ta kowanne ɓangarema kuwa, yarinyarnan kuma tanada mafi yawan nagartar data dace ta zame masa abokiyar rayuwa, mizai hana mu bashi shawarar ya sanar mata ABINDA KE RANSA”. Numfashi Hafiz ya sauke yay shiru na wasu sakkani yana nazari da bubbuga yatsansa akan baki, ya kalli Aliyu yana kaɗa kai, “Aliyu ita kanta yarinyarfa bamuda wani ƙwarin gwiwar samun goyon bayanta, dan tayi nisa wajen son ɗan uwanta, sannan bana tunanin zata iya barin Qaseem kodan halaccin mahaifinsa a rayuwarta ta ɗauki waninsa, shiyyasa nace maka akwai sarƙaƙiya takowacce kusurwa, Kasan Jabeer yanada fiƙira akan irin waɗannan al'amuran, sai dai shi matsalarsa saka wasa a dukkan lamarinsa, bansan lokacin da zai dinga kallon abu mai muhimmanci a muhallin daya dace ba, amma mubari zuwa weekend sai muyi zamana musamman akan maganar”. Cikin gamsuwa Aliyu yace, “Shikenan ALLAH ya kaimu”. Fitowar Jay daga bayi fuskarsa jiƙe da ruwa ya sakasu yin shiru, babu wanda yace dashi komai yazo ya zauna a kujerarsa, Hafiz ne ya fara miƙewa yana faɗin, “Bara muje zuwa anjima ma dawo muyi maganar idan ka samu lokaci”. Kai kawai jay ya ɗaga amma baice uffanba.

BINABASA MO ANG
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...