11

14K 1K 78
                                        

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn abdull ce👌🏼

Shafi na goma sha ɗaya

.............Mama Atika tsohuwa mai ran ƙarfe dake zaune a falonta tana jan cazbaha ta ɗago tana kallon Shahudah data shigo a guje kamar an korota, ga jikinta harya fara jiƙewa da yayyafin da har yanzu akeyi, sai da ta ƙarema guntun wandon jikin Shahudah da bai gama zuwa koda rabin cinyartaba kallo da riga mara hannu, wadda inda zata ɗaga hannu sai anga cibiyarta.
Janye idanunta tayi daga barin kallonta sannan ta girgiza kanta.
Ƙarasowa Shahudah tayi ta zauna a jikinta tana kumbura fuska ga hawaye na kwarara.
Mama Atika ta shafa addu'a tare da maida hankalinta ga Shahudah.
"Kekuwa Sabirah miya jamiki fitowa a haka cikin wannan ruwan? Ko ɗankwali ma babu fa a kanki, baza dai kibar wannan shigar ta bayyana jikinki ba ko?".
"Ni ki daina cemin Sabirah, idan bazakice Shahudah ba basai kin kira sunanaba, Wlhy hajiya nagaji da abinda Jawaad kemin a gidansa, ni gaskiya ku kirasa kuyi masa faɗa".
Mama Atika tace, "Hummm, yauma tsiyar kuka sakeyi kenan? Waishi wannan yaron wane irine? Ni abindama ke ƙaramin takaici dashi kokin kawo ƙarar tasa an kirasa sai yace shi baki masa komaiba, narasa irin wannan rikitaccen zama naku".
Kuma fashewa da kukan shagwaɓa Shahudah tayi, sai kuma lafewa jikin tsohuwar takeyi.
"K yanzu yasan kin fitone?".
Mama Atika ta tambayi Shahudah.
"Ni ban sani masaba, dan fitowata kawai nayi bayan yamin wulaƙancin".
"Hummm, to shikenan, yanzu tashi ki koma, da safen zansa iyayenku su nemeku".
"Ni dai anan zan kwana, dan inason ya gane kuransa yau"..
Murmushi irin na girma mama Atika tayi tana gyara zama, "Shikenan, tashi kije ki sauya waɗanan shiɗanun kayan ki kwanta muga idan zai biyoki, idan bai zoba ai iyayenki zasuzo gaisheni da Asuba zan sakasu kiransa ayi zama yau, dan bazan yarda da irin wannan halin na wulaƙanciba, sai dai yasan mai yuwuwa".
Jin hakan da Shahudah tayi saiya sake kai kanta sama, ta shige bedroom din ƴar tsohuwar da aka narkama dukiya ta kwanta abunta.

Tun mama Atika na zuba idon ganin ko Jawaad zai shigo a daren harta fidda, dan har tagama cin abinci da duk abinda ta saba yi kafin ta kwanta, har lokacin kuma babu Jawaad babu labarin.

Da safema koda suka tashi bai zoban, harta gaƙaraci mitarta akan Shahudah da bata tashi tai sallaba tai shiru, sai kuma ta koma kan Jawaad.
Da mitar Jawaad ɗin a bakinta su baba Usman suka shigo suka sameta, bayan sun gaisheta take sanarmusu komai.
A take suka aika a kira musu Jawaad, amma sai akai rashin sa'a aka iske ya wuce aiki abinsa.
Takaicin hakan ya hanasu motsi har saida suka fara jiyo kakarin aman Shahudah daga bedroom ɗin Mama Atika.
Itace ta shiga ta isketa duƙe tanata amai cikin banɗaki, mamaki ya kamata, amma saita ajiye mamakin ta taimaketa harta gama sannan ta bata ruwa ta wanke bakinta suka fito.
Sannu taketa jera mata da tambayarta komi taci haka daga tashinta?.
A galabaice Shahudah ke faɗin, "Ni banci komaiba Hajiya, dan rabona da cin wani abu tunma jiya da yamma, bansan miyasaba kwana ukunnan kullum da amai nake farkawa da safe, narasa mike damuna".
Tsiramata ido mama Atika tayi ba tare da ta iya cewa komaiba, tsawon wasu sakanni tana a kanta tana nazarinta, sai kuma ta fice daga ɗakin a hanzarce tare da wani irin ɗoki akan fuskarta.
Shahudah kam kanta ta maida ta kwantar barci ya kuma kwasheta.

Albishir ɗin da tsohuwa takaima ƴaƴan nata ne ya sakasu miƙewa zumbur a wani irin razane.
Kowa na ambaton mama da gaske?.
Dariyar jin daɗi tayi tana zama, "Ƴaƴannan mizaisa na muku ƙarya nikuwa, sam bakwa bina bashin rantsuwa akan wannan maganar haka take. Amma danku tabbatar a kira likita ya gwadata yanzunnan".
Duk da sun yarda da batun mahaifiyar tasu haka suka nemo Doctor domin sake tabbatarwa a aikace.
Jikin Shahudah rijib da zazzaɓi zuwa yanzun, haka dole Mama Atika ta tasheta, tambayoyi likitan yaymata tare da bata tsinken gwaji saboda ba'a buƙatar jan lokaci.
Gwajin farko ya tabbatar akwai ciki, tuni falon ya ruɗe da wani irin murna, kowa fuskarsa a washe saɓanin ta Shahudah dake a rikice.
Ciki kuma? A wannan shekarun natane zatayi ciki? Kai da sakal wai anbama mai kaza kai, sam babu tsarin ɗaukar ciki a gareta a nan kusa, yaushema sukai auren da har tagama morarsa da za'ai batun ciki a jikinta, so ake ta ragwagwgwaɓe da wurima kenan tamkar wata matar Afirika, ina wannan shirmen bamai yuwuwa bane, dolene Jawaad yazo asan abinyi, dan bazata haifi wannan cikinba koda za'a tada yaƙin duniya na ukune.

ƘWAI cikin ƘAYA!!حيث تعيش القصص. اكتشف الآن