Shafi na ashirin da uku
BARKAN KU DA JUMA'A
..........Tunda aka buɗe mana katafaren gate ɗin makarantar muka shigo nake baje idanu da hanci ina kallon wannan tsararren gini da tamkar ba makaranta ba.
Yanzu nan ni Bilkisu ɗiyar malam Ado makahoce cikin wannan makarantar? Abu kamar mafarki kamar kuma almara. Niko tayaya zan manta da Dad a rayuwata.
Ƙwallar data cikamin ido na share ina fitowa daga cikin motar, ɗalibai duk suna cikin aji, hakan yasa security kawai kake iya gani na shawagi sai malamai.
Mun samu tarba ta musamman ga wani malamin da nakeda tabbacin yazo garemune bisa umarnin Dad, na gaishesa cikin girmamawar da naga nuna jin daɗinsa saman fusakarsa.
Bisa jagorancinsa muka isa har Office ɗin shugabar makarantar, bayan an bani wani form na cike aka haɗani da malamai uku sukaimini interview, duk da karatun bai kasance ɗayaba sun yabama ƙoƙarina.
Na sauke nannauyan numfashi da naji cewar komai yayi, duk da dai ba ɗari bisa ɗari na ƙoƙartaba amma sun amsheni, to dayake kuma abun ya haɗa da harkar kuɗi sai babu wata matsala aka kammala komai tsaf.
Malamin nan dai yana tare dani muka fito, sallama mukai da driver ya tafi domin shi ya gama aikinsa, sai kuma naji hawaye sun cikamin ido, a gaban idona ya wuce.
Malamin ya kalleni yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai kinji, alkairin Alhaji a gareni bazaisa na zuba ido kiƙi nasara ba, sai dai idan ALLAH ya ƙaddaro hakan, akwai yarinyata anan makarantar insha ALLAHU zan haɗaki da ita, zata taimaka miki sosai kafin ku fara zana jarabawar, tunda akwai tazarar kusan 5weeks yanzu haka insha ALLAHU”.
Cikin girmamawa nace, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi, ya kuma bada ladan zuminci”.
“Amin” ya faɗa yana maijin daɗin addu'ar yarinyar da yaba tarbiyyarta, dan kuwa yakuma tabbatarwa ba'a gidan Alhaji ta tashiba, saboda sanin da yayma yaransa da sam tarbiyya bata gama wadatar da suba.
Security ɗin dake kusa ya kira, shine ya kwasar min kayana muka nufi inda yace min Hostel ɗinmu kenan, dan lokacin an tashi Ɗalibai duk sun shige ciki.
Mun iske hostel ɗin shiru babu wata hayaniya a cikinsa, sannan ɗalibanma ɗai-ɗai muke gani suna shawagi, kowa kuma harkar gabansa yake babu ruwan wani da wani, a ƙofar wani ɗaki mukaja birki, security ɗin ya ƙwankwasa ƙofar, babu bata lokaci aka buɗe.
Budurwa da bazata gaza sa'a taba ce ta fito, sai dai shigarta zai tabbatar maka da wahala ta kasance musulma.
Ganin malamin dake tare danine yasakata juyawa da gudu ciki tana dariya, ko minti biyu bata rufaba sai gata sun fito itada wata mai tsananin kama da malamin.
“Daddy baƙuwar harta iso?” ta faɗa cikin zumuɗi tana ɗan tsalle a gabansa.
Murmushi yayi mata, ya jinjina kansa tare da faɗin “Eh Ummie na ta iso, gata nan ma sunanta Bilkisu Adam”.
Juyowa tai gareni cikin ɗoki tace, “Barka da zuwa Bily cikin makarantarmu”.
Haɗiye hawayen farin cikin da suka cikamin ido nayi ina amsa mata, banyi zaton zanje waje a karbeni lokaci gudaba kamar yanda Ummie tai mini yau, gata dai da gani itama ƴar gatace amma sam babu fuskar wulaƙanci a tare da ita.
Ta kama hannuna cikin nata tana sauraren bayanin da daddynta ke mata a kaina cikin nuna zaƙuwa da ɗoki, ya maida dubansa gareni yana faɗin, “Bilkisu wannan itace ɗiyata kamar yanda na sanar miki, karkiji komai ki saki jikinki da ita, insha ALLAHU zakiji daɗin zama da ita kamar yanda nima nake ƙyautata mata zato a kanki, komai na tsarin makarantar zata fahimtar dake, karkuma ki cutama kanki, duk abinda ya shige miki duhu ki tambayeta kinji”.
Kaina na ɗaga masa ina risinawar girmamawa a garesa, nace, “Insha ALLAHU Daddy, ngd sosai da karamcinka a gareni”.
“Karki damu Bilkisu, Alhaji Aliyu ya wuce hakan ma a gareni, ALLAH ya bada nasara ni bara na wuce”.
Sallama yay mana Ummie nata masa shagwaɓa ya wuce ya barmu.
Itako ta rungumeni tana sake min barka da zuwa, ta shiga ƙwalama wasu kira da nake ƙyautata zaton ƙawayentane, dan kuwa daga cikin ɗakin suka fito harda wadda ta leƙo ɗazun, su uku ne, kuma duk bazasu wuce sa'anni naba.
Biyu a ciki sun amsheni hannu biyu, ɗaya kam dai sai yamutse fuska takeyi, ban damuba dan na saba ganin irinta tun shaiɗan na yawo da ɗan kanfai cikin duniya.
Sune suka kwasar min kaya har cikin ɗakin dake da gado biyar kacal a cikinsa, sannan komai tsaf tamkar ba makaranta ba.
Zaunar dani Ummie tayi a gado na ƙarshen ɗakin tana faɗin, “Wannan shine gadonki, akwai mai shi da, amma ALLAH ya mata rasuwa hutun da mukaje ɗinnan, yaya tace, tanada ciwon sikila ne.
Nace, “ALLAH sarki, ALLAH ya gafarta mata, kukuma ya baku haƙurin rashinta”.
“Amin” Ummi ta faɗa tana sharar hawaye.
Tace, “Sunana Sumayya Sadik, amma anfi sanina da Ummie saboda sunan Momy na aka saka min”.
Murmushi nayi mata, nace, “Nice name, nima zance Ummie ɗin tunda sunan Momynmu ne”.
Ƴar dariya tayi tajin daɗi, ta nuna sauran su ukun, “Waɗanan ƙawayenmu ne, mu biyarne a guruf ɗinmu kafin rasuwar ƴar uwata, mu ƙawayen junane, ajinmu ɗaya, abu ɗaya muke karanta, kuma burinmu ɗaya. Wannan sunanta Nazifa Sulaiman, wannan kuma Rebecca Emanuel, sai Zuhrah Abbas”.
“Masha ALLAH, sunayenku masu daɗi dukan ku”.
Duk Dariya sukai am ma banda Nazifa da tun farko ta Nuna bata ra'ayina, yanzunma dai tana kwance a gadonta sai latse-latsen wayama take.
Nima na faɗa musu sunana Bilkisu Adam.
Rebecca tai saurin faɗin, “Bilkisu muna fata zaki cike mana gurbin guruf ɗinmu da muka rasa a yanzun”.
Murmushi nai bance komaiba, dan bazance zanyi saurin aminta da suba tunda banga halayyarsu ba........
Zuhrah ta katse tunanina da faɗin, “Please Bily karkice a'a, muna buƙatarki a cikinmu dan mudai kin mana”.
Nanma murmushi nayi dai, a raina ina mamakin ni da kullum su aunty Shahudah ke kushe munina da ƙyamata ce kuma har suke iƙirarin na musu su kuma?.
Magiya suka shiga min da roƙon karnace a'a, dan haka kawai sainace musu su bari zanyi tunani to.
Murna sukaitayi wadda ni taita bani mamaki, sai dai ina jiyo tsakin da Nazifa tayi kaɗan.
Ban damuba, dan amsar da ƴan uwanta kawai sukaimin ta wadatar dani, da taimakonsu na kintsa kayana tsaf, daga nan muka zauna sunamin lissafin abinda makarantar ta ƙunsa.
Zakuyi mamaki idan nace muku harna kwanta barcin dare ban tuno ko ɗaya daga cikin su aunty Aamila ba bayan Dad kawai da tunda muka iso nake jerama addu'a a zuciyata.

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...