Page 11
...............Tafiyar da batafi mintina talatin ba muka iso inda ya bani mamaki, bandai cema oga Jabeer komaiba har aka buɗe mana gate muka shiga. A dai-dai sashen da mukai salla ranar rasuwar Uncle Usman yay fakin, ya kashe motar yana faɗin, “Muje ko”.
Bance komaiba na buɗe murfin na fita kamar yanda shima yayi, yana gaba ina biye da shi har zuwa ƙofar falon, sai kalle-kalle nake ina ƙara jinjina girman wannan gida, koba'a faɗaba kasan an narkar da dukiya wajen ginashi, Oga jabeer ne yay knocking, babu jimawa akazo aka buɗe ƙofar.
Cikin murmushi Nabeelah data buɗe ƙofar tace, “Yah Jabeer sannu da zuwa”. “Yauwa Nabeelah” ya amsa yana mata murmushi shima. Sai da ya shige sannan ta ganni, cike da mamaki ta waro idanu alamar ganina a bazata da tai, kafin ta daka tsalle ta ɗaneni tana dariya, “Lah ƙawata dama rai kanga rai?”. Murmushi nayi ina mai jinjina wautar Nabeelah a raina, cikin surutunta tace, “Dama kinsan Yah Jabeer?”. Amsa na bata da cewar, “Eh, wajen aikinmu ɗaya”. Zata sake jehomin wata tambayar Jabeer ya katseta, “To Akku mai bakin magana kaimu ɗakin da yake”.
Yanda tayi da fuskane ya sakani yin murmushi, ita a dole taji haushin ance mata Akku, hannuna ta kama tana tuttura baki gaba tai mana jagora har sama, bansan minene ya kawomuba balle tunanin wajen wa mukazo, ni dai kawai inabin Umarnine. ‘Tabɗi’ na faɗa a raina saboda ganin yanda falon saman ya haɗu matuƙa shima, sai sassanyan ƙamshi ke tashi, muryar kamilar mace ta amsa mana sallamar da mukai tare da faɗin, “Jabiru sannunku, ku shigo mana”.
Oga Jabeer ya amsa da “Yauwa Umma, ashe kema kina nan?”. Tace, “Eh muma bamu jima da zuwaba, nazo na sakema Hajiya Zainab gaisuwane sai Gimba ke cemin basu fita Office ba, yanata jiran Jawaad ya fito bai fitoba, shinefa na shigo na iskesa kwance rijif cikin zazzaɓi”.
“Ya salam, wlhy muma a office tun ɗazu muke zuba idon ganinsa amma shiru, mun kirasa bai ɗaukaba hakama Gimba, tomu tunaninmu koma wani wajen sukaje tunda munga jiya lafiya lau yabar office, sai daga baya ne gimba ya kira yasanar mana ai baida lafiya, ko sallar juma'a ma da ƙyar in zai iya fita, shinefa nace bara mu sakko massalaci nazo naga jikin nasa, tunda su Hafiz sun fita wani aiki”.
Sosai gabana ya faɗi da jin sunan Boss a zancensu, harda ƙarin furucin rashin lafiya, banji amsar data bama Jabeer ba saboda tunanin dana tafi.......Hannuna da aka riƙone ya katse mani tunani, na kalli Ummah data riƙonin nai ƙasa da kai ina faɗin, “Ina yini”. Ummah tace, “Lah kece Auntyna? Aini bamma ganekiba da farko wlhy nama zata Maman Areef ce (Matar Jabeer). “A'a Umma nice” na bata amsa kaina a ƙasa, kafin ta samu damar yimin tambaya Jabeer ya bata amsa da cewar, “A'a Umma ba Fannah bace, Mom ɗinmu ce, da alama ma kin santa kenan?”. Ummah tai murmushi tana zaunar dani a kujerar kusa da ita, tace, “Nasanta Jabiru, ƙawar Nabeelah ce ai, ina ka samo mana ita ne haka? Ko dai ta biyu ce?”. Yanzun kam ƙaramar dariya Jabeer yay yana girgiza kansa, “Wai Ummah ta biyu kuma? A wannan marrar ɗayarma ya aka ƙare, sai dai idan zaki nemarwa ɗanki ne, shine gwauro, wajen aikinmu ɗaya da Mom ɗinmu” ya ƙare maganar idonsa a kaina.
Dariya tayi tana sake riƙo hannuna, cikin sigar tambaya tace, “ɗiyata kina son ɗana?”. Kasa cemata komai nai sai ƙasa dana ƙarayi da kaina, a raina ina faɗin, ‘Ni inada Yah Qaseem ɗina’. Jin bance komaiba ta maida kallonta ga Jabeer,
Cike da mamaki tace, “Waima tsaya Jabiru, kana nufin itama irin aikin naku takeyi?”. “Sosaima kuwa Ummah” ya bata amsa cike da karsashi. Haɓa ta riƙe tana sake damƙe hannuna, “Oh ni ɗiyata, kekuma abinda ya burgeki kenan? To Nabeelah kinji fa jaruman mata, ba irinki matsoraciya ba” Nabeelah da mamaki ya kashe tace, “Wai dan ALLAH da gaske?”. Hararta Jabeer yay yace, “Da gaske mana”. Nabeelah tace, “Tab, wlhy bari Yah Jay ya warke nima ƴar sanda zan zama”. dariya Umma da Jabeer sukai mata, nidai na murmusa ina kallonta da faɗin, “Dakin burge kuwa, kinga ƙawata ta dawo kusa dani”. Da sauri ta cafe da faɗin, “Karki damu ƙawa ina nan tafe, kam Nabeelah ƴar sanda, ashe zan ragargaji ƙattai”.
Jabeer yace, “ko kuma ke su ragargajeki ba”. Ɓata fuska tai da tura baki, “A'a wlhy Yah Jabeer kar kai min baki tun yanzu”.
![](https://img.wattpad.com/cover/220260947-288-k27914.jpg)
YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...