50

14K 1.1K 139
                                        

Page 50

.................Shiru kakeji falon ya ɗauka bakaji motsin komai saina ajiyar zuciyoyi dana AC dake aiki. Sai da Abu-Siddiq yay doguwar addu'a kafin kowa ya sake maida hankalinsa ga takawa da yay gyaran murya alamar zai fara magana. Wata gyaran muryar ya sakeyi kafin yay sallama a garesu duk suka amsa, Cikin nutsuwa Takawa ya sake gyara zamansa.
         “Alhamdulillahi ala kulli halin, duk da dai bamu da tabbacin har yanzu Umm-Anum ta gane Jawaad matsayin jininta ina ganin ya kamata na fara warware abinda mu muka sani game da ita kafin muji abinda zai fito daga nata bakin yanzun”. Jinjina kai kowa ya shigayi cikin gamsuwa da jawabinsa.
         “Mun tsinci Umm-Anum a wasu shekaru da zan iya ƙiyastasu da kusan shekaru ashirin da takwas idan ban mantaba, a lokacin nazo gida daga india domin halartar bikin salla babba kamar yanda na saba a duk shekara, saukar dare nayi a ranar, dan sai kusan tara na dare ma na iso, amma kamar ko yaushe na iske sarkin mota na jiran isowata a airport ɗin. A gajiye nake matuƙa gaya dan haka bamu ɗau lokaciba muka bar airport ɗin, tafiyar mu bata wuci ta mintuna goma ba akan titi sarkin mota yaja wani wawan birki. Sosai gabana ya faɗi saboda ƙarar da aka ƙwalla mai nuna tabbacin mun bige wani, daga ni har shi fita mukai cike da tashin hankali. hakama mutane dake ɗan kai kawo a titin harsun fara taruwa a wajen. Ganin mace ce kuma cikin shiga ta kamala duk da babu lulluɓi tare da ita sai muka fara bincikar mutane ko akwai wani nata a wajen?, amma babu wani mai alaƙa da ita. Mun ɗauketa zuwa asibiti, duk da gajiyar da nake ciki bamu bar asibitinnan ba sai da muka tabbatar ta samu dukkan kulawar da ake buƙata a daren sannan muka wuce raina duk a dagule. A dalilin bige baiwar ALLAHr nan gaba ɗaya bikin sallar nan baimin daɗi ba, dan tun bayan farkowarta daga magagin ciwon bugetan da mukai sai muka fuskanci tanada taɓin hankali ma, taɓin hankali irin mai ban tashin hankali, dan duk da cikin halin ciwo da take ƙoƙarinta kawai ta gudu daga asibitin ita dai, dalilin hakan takai har sai da aka saka mata hand corps a hannu da ƙafa sannan aka samu ɗan kwanciyar hankalin ta, a hakanma fisge-fisge take ita kawai a barta ta tafi duk ta jima hannayenta ciwo da ƙarfen ankwa dana gado. Doctor ɗin shine ya faɗamin gaskiya da tabbatar mana cewar matarnan akwai wani babban al'amari tattare da ita, mizai hana mu haɗata da malaman musulinci. Wannan shawara tasa itace ta zame mana haske a kanta, sai kuwa na samu abokina Muftahu akan ya bincika min malamin da zamu kaita wajensa, shine kawai ya bani shawarar mizai hana mukaita Saudia wajensu Abu-Siddiq. Na amshi shawarsa da hannu biyu babu ɓata lokaci mukai duk wani ciku-ciku dagyar muka samu damar fita da ita zuwa nan saudia. A ganin farko dasu Abu-Sufyan sukai mata suka tabbatar mana akwai sihiri tattare da ita, dan kuwa tunda ta buɗe ido daga barcin da take dan allurar barci a kai mata tun da ga can kafin mu taho saboda gudun matsala, sai muka sameta a nutse babu wani bige-bige da takeyi sai dai alamar rashin lafiya na haukan yana tare da ita, alamun hakan na nufin can ƙasarne ba'ason ta zauna kenan ko wani abun daban da bamu da ilimi a kansa. Bayanin da mukaima Abu-Sufyan akanta ne yasa yace mubarta a wajensa na wani lokaci zasu cigaba da kula da ita. Nai masa godiya sosai bayan kwana biyu na koma india nabar Muftahu anan saudia. shima kuma bayan wani lokaci saiya koma. A koda yaushe muna magana da Abu-Sufyan ko Abu-Siddiq akanta da yanayin jikinta, sannan Muftahu nata ƙoƙarin bincike game da ahalinta acan gida, sai dai babu wani haske da muka samu game da samunsu. Bayan wani lokaci jikinta yay sauƙi sosai ta koma normal Alhmdllh, sai dai kuma ta manta komai dangane da kanta, batasan ko itaɗin wacece ba, daga ina ta fito? duk ta manta har sunanta, wannan shine ya ɗarsa tausayinta a zuciyar Abu-Sufyan yace shikam zai aureta har ALLAH ya kawo iyakar komai ta gane ahalinta. Tunda yaymin bayani sai ban musaba, dan uba nike kallonsa bawai yayan aboki kawai ba, na kuma tabbata shine kawai zai iya riƙe amanar baiwar ALLAHr da bata da kowa tunda hatta kanta da sunanta tama manta, ya bada gudunmawa sosai gameda jiyyar mahaifina shima, har kawo yanzu kuma yana badawa a dukkanin al'amurana dana zuri'ata, babu abinda zance a garesu sai addu'ar fatan gamawa da wannan rayuwar lafiya su samu sakamakon aljanna a ranar sakamako”.
       Tunda Takawa ya fara magana hawaye kawai kowa ke faman sharewa, Abbu yace, “Tabbas duk abinda ya faɗa hakane, abinda kawai ya manta bai faɗaba shine ciki dake tare da ita, sun kawota da ciki kwantacce da bamusan adadin wataninsa ba, kamar yanda ya nuna, dan sai da muka dage da addu'oi da magani matuƙa sannan ya fara motsi alamar abinda ke cikin yana raye, da alama dai akwai sharrin jinnu a al'amarin kokuma wata hikimar UBANGIJI daya ɓoye game da cikin wadda zuwa yanzu munga ƙalilan daga ciki shiyyasa ya ɓuya a jikinta, tashin da cikin yayi sai yazam watanninsa ya koma baya, dan saiya koma wata uku, sai da tai wata shida sannan ta haihu Namiji, shine yaci suna Muhammad Anuwar gashi nan, bayan haihuwarsa ne mukai aure da ita ta haifi Anum kuma, ga tanan tana da shekaru ashirin da uku, daga ita dai bata sakeba har zuwa yanzun”.
     Cikin rawar jiki Anuwar ke kallon Jawaad, sai kuma ya kalli Abbu ya kalli Umm-Anum da ke zaune shiru ta zabga tagumi tana hawaye, dan abubuwa da dama ne keta dawo mata cikin rai tun a daren jiya, hatta da sunanta ta manta sai a daren jiya ta tuna shi. Hannunta dake rawa ta miƙama Jay dake kallonta ko ƙyafta idanunsa bayayi,  a hankali ya miƙe ƙafafunsa tamkar an dokesu ya nufota, ta riƙe hannunsa ta zaunar da shi kusa da ita tare da rungumesa ta fashe da kuka, shima Jawaad hawayen yakeyi. A take falon ya ɗauki sabon koke-koke har saida Abbu ya fara musu nasiha akan hakan sannan suka tsagaita. Anuwar ya taso shima ya zauna kusa da Ummu, kafin ya tashi ya koma jikin Jay yana sharɓar kukansa, Jawaad ya rungumesa da ƙyau yana murmushin farin cikin samun ƙanne. Tasowa itama Anum tayi tazo ta zauna ƙasa ta ɗaura kanta saman ƙafar Jawaad, ya sake murmushi da shafa kanta yana lumshe idanunsa da kai hannu ya share mata hawaye itama. Wata irin ƙaunarsu mai tsananice ke ratsa dukkan ɓargonsa da jini, ji yake a duk duniya yau babu kamarsa a cikin masu nasara, jinsa yake tamkarma su kaɗaine a cikin duniyar babu wani mahaluki mai numfashi da ya rage bayansu ɗin, wani sanyi mai sanyaya kuzari na shiga cikin tsokar jikinsa tana ratsa dukkan ɓargonsa da jijiya.
       Cikin dasashshiyar murya Umm-Anum tace, “Tabbas niɗin na taɓa aure, bankuma taɓa tuna hakanba sai a daren jiya, na auri wanda yake matsayin yayana a gidanmu dukda ba iyayenmu ɗaya ba, matar babanmu ce da ya aura bayan rasuwar innarmu ce mahaifiyarsa, itama kuma mijinta ya rasune, shine iyayenmu sukai aure, suka kuma haɗemu suka riƙe tamkar tare suka haifemu, Auren soyayya mukayi da Abdul-aziz, shiɗin mutumne mai himma wajen neman nakansa, sannan mutumne mara hayaniya da damuwa da gudun ƙyale-ƙyalen duniya, mutum ne ma'abocin son noma da kiwo, mai tsananin son ƴan uwa da zuminci, shine auta a gidansu kaf, shi kaɗai kuma mama maryam ta haifa a gidan, baida wa baida ƙani dan haka yay mana gata sosai ni da ƙannena lokacin da mahaifiyarsa ta dawo aure gidanmu. Bayan aurenmu mun samu jarabawar rashin samun haihuwa na tsahon wasu shekaru harma dana abubuwan more rayuwa, kafin na fara haihuwar kuma yaran su rasu, sai daga baya harma mun fidda rai da wata haihuwar sannan ALLAH ya azurtamu da samunsa (ta nuna Jawaad) lokacin da muka samesa Abdu-aziz ya bunƙasa, dan harkokinsa na noma da kiwo sun kaisa har ƙasar turai dalilin zaman mutunci da wasu turawa da sukai aikin dam ɗin ƙauyen garinsu, abinda kawai zan iya tunawa bayan wannan game da rayuwata shine, sunana BILKEESU, sai mahaifina, sai ƙannena uku mata, Mariya, Rahmah, Wasila, sai Mama maryam, saiko shi dana bari, sai Abbansa dana tabbatar ya rasu, wannan shine kaɗai abinda zan iya tunawa game dani da rayuwata ta baya kafin gushewar komai”. Ta ƙare maganar hawaye na ziraro mata.
     Jawaad da shima ke hawayen ya saka hannu ya share mata yana girgiza mata kai alamar ta bari, muryarsa a ɗashe yace, “Na godema ALLAH da yasa kika tunani Ummuna, na kwana da tsananin fargabar kar kice baki tunani ba koma baki sanni ba gaba ɗaya, da hakan ta kasance na tabbata sai dai ku binne gawata a yau Ummuna, na godema ALLAH da yasa kina raye, na godema ALLAH da ya ƙaddara sake haɗuwarmu a duniyar nan, na godema ALLAH daya jarabceni da son wadda ta silarta yau nake a jikinki Ummuna, (yay maganar yana nuna Bilkisu) na godema ALLAH daya haɗa dangantakarta da zuri'ar Takawa har nima nakai ga zuwa garesu, su ɗin shugabannine da adalcinsu yakai kowanne yanki, kowacce ƙabila, suyi fatan zamowa masu mulkinsu Ummuna, mutanen nan uku haskene babba a gareni da suka haskamin hanyata zuwa gareki”.
         Share masa hawayen shima tayi tana miƙama Bilkisu dake kuka hannu alamar itama tazo, da ƙyar BILKEESU ta miƙe zuwa garesu tana haɗa hanya, Umm-Anum ta sakata a jikinta tana maijin ƙaunarta har ƙarƙashin ruhinta, “Ɗiyata ashe ƙaunar da nake miki tun ganinki na farko bata wasa bace, ALLAH yay miki albarka kinji, ALLAH ya ɗaukaka rayuwarki ya saka mata albarka ya baibaiyeki da alkairi da rahamarsa mai tarin yawa”. Gaba ɗaya falon aka amsa da amin.
     Ummu dake murmushi tace, “Haka rayuwa take, ƙanƙanin abu sai yazama silar warware babba, kunga dai yanda aka ɗauki tsahon shekaru wajen addu'oi da neman ahalin Umm-Anum, amma sai gashi cikin sauƙi Wallet ta zama silar komai......” Ta shiga bama su Umm-Anum labarin komai game da haɗuwar Bilkisu da su Safah a Ladies mirror, da dagewar Safah akan saita tafi da Wallet ɗin bilkisu masarauta, har silar komawarta hannunsu...
        Sosai al'ajabi ya kama su Umm-Anum sukaita sake jinjina al'amarin da girmama hukuncin UBANGIJI mai shirya yanda yaso a lokacin da yaso ga wanda yaso cikin hikimarsa.
       Duk godiya suka shiga sake jera ma su takawa da addu'oin fatan alkairi, dasu Abbu ma kansu suma har saida takawa da Abbu sukace ya isa haka sannan. Akwai sauran magana sosai a bakin Takawa dan ya fahimci akwai wasu abubuwan da yawa dake a ɓoye wanda Umm-Anum bata iya tunawa ba, shima kansa Jawaad dai akwai magana a bakinsa musamman game da haukar mahaifiyarsa da abubuwa ma da dama, sai dai yayi shiru ya barma ransa, so yake ya samu nutsuwar zama sake nazari da fashin baƙi akan komai, su kuma keɓe da matarsa su tattauna kozai ƙara samun haske daga gareta dan kowa da irin baiwarsa. To yanda duk tunaninsu yake hakama na Abbu da Abu-Siddiq yake, su kuma sunason su keɓe ne da Jawaad sumasa tambayoyi game da family ɗinsa, dan sunji Umm-Anum bata tambayi komaiba akan komai ma, alamomi da yawa kuma sun nuna akwai abinda ke binne, bazasu fahimci hakanba sai sun sami sanin ainahin tarihin komai tun daga tushe sannan.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now