40

17K 1.2K 657
                                        

Page 40

...............Sosai Nabeelah ta waro idanunta da suka cika da hawaye tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, “ALLAH yayanmu ni babu abinda zan faɗa, dan ALLAH kayi haƙuri”.
          “Kinsan ALLAH idan kika bari harna miƙe kanki sai jikinki yay masifar yin tsami”. Yay maganar muryarsa babu alamun wasa. A mamakina sai naga Nabeelah ta fashe da kuka tana ɗanja baya, na kallesa da nufin bashi haƙuri duk da nima a tsoracen nake sai na ga ya miƙe, ai kafinma nace wani abu sai hango Nabeelah nai ta kwasa da gudu ta fice. Yanda yaja birki tare da riƙe ƙugu yana kallontane ya sakani kasa danne dariyata, hannu nasaka na toshe bakina tare da saurin kauda idanuna ganin ya kalloni.
           Jawaad yay ƙwafa yanabin Bilkisu da kallo, “Ke kuma dariyan na miye to?”. Kallonsa nai da sauri ina ƙoƙarin haɗiye kayata amma na kasan, dan fuskata kawai zaka kalla kasan dariyar taƙi haɗiyu wa, harar daya ballo mince tasa nai niyyar barin masa falon naje nai dariyata a ciki. Caraf naji an cafkomin hannu da faɗin, “Dariya ko? To bara na huce a kanki”. Tsaf na haɗiye dariyar na koma zare idanu, cikin marairaice fuska nace, “Nifa ba dariya nayiba”. “To mi kikayi?”. Yay maganar da tsatstsareni da mayun idanunsa. Sosai kunya ta lulluɓeni nai ƙasa da kaina ina ɗan waige-waige, nima na Nabeelah nake tsarawa na fece kawai. Kamar ya fahimci abinda nake tsarawa a raina yace, “Kema guduwar zakiyi? Itama ɗin ba ƙyaleta naiba zan sameta har gida sai naci ƙaniyarta na gasa mata baki tunda ita magananniyace”. Murmushin da ban shiryaba ne ya suɓucemin, nace, “Yi haƙuri to niba baƙuwar zafi bace wlhy”. Kafin yace wani abu wayarsa ta shiga ring, kallon wayar duk mukai da mamaki, da alama ma anan ya mantata ta kwana ko?, hannuna dake cikin nasa na janye na ɗakko masa wayar da rabinta ya shige ƙasan filon kujera. Ban tsaya kallon ko wanene ba na kawo masa cikin.
       Amsa yayi yana zama, ni kuma na juya na ɗauki basket ɗin da Nabeelah ta kawo wanda ko ba'a faɗaba kasan breakfast ne a ciki. Harna nufi D/table naji ya kirayi sunana, juyowa nai ina amsawa da “Na'am”. Dai-dai zai saka wayar a kunnensa alamar wancan kiran ya katse shi ya sake kira. Yace, “Kawomin tea, karki saka suga da yawa”. Da “to” na amsa kawai na ƙarisa na ajiye basket ɗin saman dani. Kicin ɗin na nufa ina ɗan murmushi da yaba ƙoƙari da sadaukarwa irin ta waɗanan bayin ALLAH, babu dangin iya babu na baba suka kashemin waɗanan kuɗin? Ba ƙaramin mutsuwar tsaye naiba da ganin yanda kicin ɗinan yay mugu-mugun haɗuwa, ni balki ɗiyar baba makaho ce da wannan gidan matsayin matar cikinsa? Sai kawai naji ƙwalla sun cikamin idanu, na shiga maimaita kalomin Alhmdllh a zuciyata ina hawayen zuci. Fasalta muku yanda kicin ɗinan yake ai ɓata lokacine, abin mamaki da al'ajab harda kayan abinci da malam bahaushe ke kira da gara, dai-dai da magi wannan sakarai an ajiye min shi. Sai dai kuma babu kayan tea ɗin da yace na haɗa masa, iya dubana banga koda lipton ba sai kayan ƙamshi kawai da abinda ba a rasaba, komawa nai da niyyar faɗa masa ban ganiba amma na iske yana waya da ransa a ɓace. “Uncle Please ka ƙyalesu ni babu abinda zanzo na musu, ina ƙoƙarin danne duk abinda suke son takalata dashi kawai amma na kula neman kaini maƙura sukeyi akan shirmensu”. Yaɗanyi shiru alamar saurare, hakan yasa na juya zan koma dan na bashi damar gamawa amma sai naji takunsa a bayana, baimin maganaba yazo ya wuceni, ganin hakan yasani bin bayansa, drawer saitin fridge ya buɗe ya nunamin. Kaina na jinjina masa na ida shiga ciki shi kuma ya fice yana cigaba da wayarsa. Bani da matsala da kayan ƙamshi dan duk gasunan a robobi harma da ganyan shayi masu daɗi da Umm-Aban dama tace zata haɗa min saboda ta lura inason shayi. Tukunya na ciro da dama an fiddata a kwalinta na ɗauraye na zuba duk abinda zan buƙata na ɗora saman gas da dama an haɗashi shima. Komawa nai na ɗauki plate da flask da kofi na ɗaurayesu tsaf, cikin mintuna ƙalilan na kammala na fito da komai na ajiye a dani ɗin, sannan na koma na ɗakko tea ɗin dana haɗa a kofi na ɗaura saman ƙaramin tire na kai masa falon dan har yanzu wayar yakeyi. Yanda yake kallona harna ajiye tiren a centre table duk sai naji na takura, nuni yaymin da in bashi, ɗauka nai na miƙa masa, ya ɗan lumshemin idanu alamar “thanks”. Bance komaiba nabar wajen dan sonake nai wanka.
          Saida na gyara gadon yay tsaf sannan na shiga wankan, wanka nai haɗe da wankan tsarki dan mai jar motama ya ɗauke tunkan azhar ɗin da nake hasashen, zaton babu mai shigominne ya sakani fitowa daga ni sai guntun towel ga gashi a jiƙe, sai dai inata ƙoƙarin tsanesa da ƙaramin towel dake a hannuna. Ina ƙarasawa gaban mirror yana shigowa da sallama ciki-ciki alamar ransa a ɓace yake har yanzun, saida naji tamkar na ƙwala ihu, na ɗan wawwaiga banga wani abu dazan iya ja na rufe jikina da shiba, haƙura nai kawai na ɗan ɗago na kallesa cikin dauriya ina faɗin, “Nazo na baka abincin ɗinne?”. Shirun da naji yayi bai amsaba yasa na ɗago kaina na dubesa, idanunsa nakan gashina ko ƙyaftawa bayayi. Sake maimaita masa tambayar nayi. Ya janye idonun nasa da juyawa zai fita yana faɗin, “Ki gama nima zanyi wankan ne”. Binsa kawai nayi da kallo dan na lura ransa a ɓace yake, ‘Komi akai masa kuma?’ na faɗa a fili batare da inada mai bani amsata ba. Gudun karya sake shigomin yasa nai shiri a gaggauce cikin sket da riga na shadda orange color. Ni kaina nasan sunyimin ƙyau dan kamar an haliccesune a jikina sunmin ɗam dan telan ya iya ɗinki, kaina nakeson busarwa amma abin haushi babu wuta, a haka na gyarashi bayan na tsanesa sosai babu ruwa, ɗauresa nai da tunanin ƙila su kawo wutar anjima tunda naga anguwar kamar suna samunta sosai. Bawata kwalliya nai da yawaba amma fuskata tayi fayau, na saka ƙaramar sarka sannan na feshe jikina da turare sosai, kowa ya ganni yaga amarya da gaske, farin gyale na ɗauka shima na saka turare sannan na yafa na fito falon. Gidan tsaf yake babu wani datti, hakan yasa kawai na ɗauki fresheners da turare mai ƙamshi haɗin gida na fesa iya falon nan kawai. Ina cikin fesawar ya fito.
         Jin Motsinsa a bayana ya sakani waigawa, kwalliyar tasa ta sakani shagala a kallonsa batare dana fargaba, shaddace ƴar ubansu golden color ya saka, sai maiƙo take da ɗaukar ido, ta samu nutsatstsen ɗinki na zamani da ya fiddo cikar zatinsa mai tabbatar dashi jinin hausawan usul harda su hula......
            Saukar iskar da naji a cikin idanuna da ƙamshi Mouth freshener ɗin da ya saka ya sani dawowa hayyacina daga sakin layin da nayi, nai ƙasa da kaina dan naji kunya.
          “Gulmammiya kinaso kina kaiwa kasuwa, na miki ƙyaune?”.
        Ɗan kallonsa nai na juya ƙeya nace, “Kaɗan”. Murmushi ya saki har inajin sautinsa, ya ɗaura hannunsa saman haɓata ya maido fuskata inda yake, “In har da gaske kike ki kaleni cikin ido kice kaɗan nai ƙyau”. Hannu nasa na rufe fusa da sake juya masa baya ina murmushi. “Baki da gaskiya kenan”. Yay maganar kusa da kunnena yana zame gyalen dana yafa. “Malama niba surukinki bane ai, muje kiga gidanki”.
           Shine yaymin rakkiya lungu da saƙo na cikin gidan har ɗakinsa da harabar gidan, gaba ɗaya gidan ya canjamin tamkar ba wanda na taɓa zuwa ɗin nanba, an gyarashi sosai ya canja kamanni. Sai da muka gama zagaye ko ina muka yada zango a wajen cin abinci. Nidai kasa sakewa nai naci saboda yanda yay mugun tsatstsareni da idanu, duk sanda zan ɗago sai naga idonsa a kaina. Da dai na gaji saina kumbura masa fuska, “Nifa wlhy ba television bace ba”. Bakinsa ya taɓe baice dani komaiba bai kuma bar kallon nawaba har muka gama. Ɗakinsa ya koma nikuma na tattarr wajen, na fito masa da abincin maigadi da tunkan mu fara cin namu ya sakani na zuba shima ya fito, agogonsa da links ya miƙomin tare da miƙamin hannunsa. Dukda inajin kunya haka na saka masa links ɗin sannan na saka masa agogon. “Thanks” ya faɗa a hankali yana ɗagemin gira ɗaya.
         Kafin nace wani abu maigadi ya doka sallama a ƙofa, kallon ƙofar mukai gaba ɗaya amma shi ya amsa masa, ya amshi kular hannuna tare da nufar ƙofar ya buɗe.
    Maigadi ya gaidasa da faɗin, “Alhaji kanada baƙone”. Da ɗan mamaki Jawaad yace, “baƙo kuma malam gambo?”. “Eh Alhaji, harzan masa ƙaryar baka tashiba saina fahimci amatse yake da son ganinka gaskiya, kuma kamar baƙon mai muhimmanci ne”. “Okey, to ga abincinka ina zuwa”. Amsar kular yay dayi godiya ya koma, Jay kuma ya maida ƙofar ya rufe ya dawo inda yabar Bily tsaye tana kallonsu. Wuceta yay ya ɗauka key ɗin motar dake kan centre table, “Bara naje na gaida Alhaji Babba daga nan na leƙa asibi wai Hudah aka kwantar”. “Ya salam” na faɗa cikin damuwa, “Miya sameta kuma? Dan ALLAH kaje dani”. Kaɗan ya kalleni ya ɗauke kansa, “Kimata addu'a daga nan ya isa, kokin taɓa ganin amarya ta fita”. Cikin shagwaɓar da bansan inada itaba nace, “Toni tsoro nakeji wlhy”. “Tsoro kuma?” ya faɗa yana kallona. kaina na ɗaga masa batare dana yarda mun haɗa ido ba. Jin yaƙi magana yasa na sake kallonsa, sai naga niɗin yake kallo ashe shima. “ALLAH na kula kinma rainani” yay maganar yana matsoni, baya nai saurin ja, amma duk da haka saida ya riƙoni. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “Ke komai abin tsorone a wajenki halan?”. Nace, “To inason naje naga aunty Shahudah ne”. “Uhhyim shine zakimin ƙarya? to babu inda zakije, ki jira ƙawayenki na nan zuwa zan dawo bazan jimaba dan zanyi magana da ku”. Saurin kallonsa nai da mamaki nace, “Su Ummie?”. Kansa ya ɗagamin. “Miya faru?”. “dan na dawo zakiji ai, ana jirana yanzun”. Ya ƙare maganar da ɗaura bakinsa saman nawa babu zato. ‘Ya salam’ na ambata a zuciyata tsigar jikina na tashi ga yanayin da nakeji na neman tasomin dukda dai yanzuma da sauƙi sosai ba kamar da ba. Sai da yaja kusan minti biyu kafin ya saki bakin ya sumbaci goshina. “Saina dawo”. Kaina kawai na jinjina masa dan na kasa kallonsa. A hankali na furta, ”ALLAH ya tsare”. Inajin yana murmushi. Nidai ban kallesanba har ya fice.
     Sassanyar ajiyar zuciya na sauke tare zubewa a kujera daɓar na dafe kaina, wlhy abun mamaki yake ban, boss fa! Kai rayuwa bata rabo da abubuwan al'ajabi. Naja kusan mintuna biyar a haka kafin na miƙe naje ɗakinsa dan na gyara. Sosai ɗakin yake ƙamshin turarensa daya fesa yanzun, tsaf na gyarashi na saka fresheners sannan na koma kicin na ɗauraye kwankina da mukaci abinci shima naɗan gyara abinda bai minba.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now