26

11.1K 1K 110
                                        

  Shafi na ashirin da shida

Yau ma dai babu editing😣😫

............Shahudah taɗan samu sauƙi, sai dai fargabar Jawaad ta hanata sukuni sam, gashi a yau ko ƙeyarsa basu ganiba a gidan, tanason kiransa a waya tanajin tsoro.
       Kusan ƙarfe uku na rana sai ga Doctor Tayyeb yazo gidan, lokacin duk suna falo, Qaseem ne kawai babu a gidan dan yana Office wajen aiki.
     Shahudah na kwance ne a kujera doguwa kanta a kan cinyar Mummy, karenta na kwance daga ƙasa kusa da ita, sai Aamilah da Jack da Salma waɗanda shigowarsu gidan kenan.
     Sai da Dr Tayyeb ya bama su Salman hannu suka gaisa sannan ya zauna yana gaida Mummy idonsa akan Shahudah da keta ɓata rai, dan tasan allura yazo yay mata ita kuma batason ta.
      “My patient yaya jiki?” ‘Ya faɗa yana mata murmushin yaƙe’.
      “Fine” kawai tace masa ta ɗauke kanta.
       Bai damu ba yace, “Alhmdllh, yanzu dai babu ciwon marar ko?”.
       Kanta kawai ta ɗaga masa.
          Shima bai sake cewa komaiba ya shiga haɗa allurar da zai mata, ƙasan zuciyarsa yana tunanin ta yanda zai ɓilloma aikin Jawaad.
       Da ƙyar Shahudah ta tsaya akai mata wannan allura, saboda tsabar taɓara harda kukanta.
      Sai da ta koma dai-dai ne ya gyara zama yana mata bayanin yanda zata kula da kanta,  ya fiddo wasu ƴan kwalaben magani, ɗaya ya miƙama Salman dake kusa dashi yana faɗin, “Salman ko kasan wannan maganin?”.
     Karɓa Salman yayi yana dubawa, Dr Tayyeb ya sake ɗibar biyu ya mikama Aamilah da Jack suma, “Kuma ku duba kuga ko kun sanshi”.
     Suma basu musaba suka amsa, itama Mummy da Shahudah duk ya miƙa musu, da farko dai Shahudah kam taƙi amsa, a cewarta karya isheta.
     Mi kuma ta tuna oho mata, sai ta miƙo hannu ta amsa.
        Salman da Aamilah suka fara maido masa da kwalaben suna faɗin sudai bama su gane kan maganinba, kwalayen kwalaben ya miƙa musu duk suka saka da kansu sannan ya amsa ya maida ajikka.
     Jack ya kalli Dr Tayyeb cikin nuna shiɗin ƙwararrene yace, “Wannan ai maganin hana ɗaukar cikine, macen da bata haihuwama akan bata ta gwada shi kamar na wasu wattani kafin ta dakata”.
      Murmushi Dr Tayyeb yayi yana jin jina kai alamar gamsuwa da bayanin jack, ya miƙa masa kwalin shima ya saka yana faɗin, “A lallai kasan magani kam sosai”.
     Jack yaji daɗin yabon da ake masa ya miƙama Doctor bayan ya saka a kwalin yana sake bajewa a kujera, suma su Shahudah duk basu yay suka saka ita da Mummy ya amshe abunsa ya maida duka a jaka, ba tare daya yi musu wani ƙarin bayani ba yay musu sallama ya tafi.
 
      Kaf ɗinsu babu wanda ya kawo wani abu a ransa game da maganin da Doctor Tayyeb ya nuna musu, garama Mummy taji haushinsa sosai, dan ita gani take kawai Doctor ɗin nasu yayi hakanne danya nunama Shahudah hanyar ɗaukar mataki a gaba, itako yanda suka tsara yanzu nanda kwanaki kaɗan Shahudah zata koma ɗakinta ko ALLAH zaisa a dace wani cikin ya shiga.
     Dan jiya dai ta daure taje gida tama Mama Atika da ƴan uwanta bayani akan matsalar Shahudah ɗin.
       Dukansu sun nuna rashin jin daɗinsu da tausayin Shahudah, sai dai kuma hankalinsu ya tashi, dan a ganinsu inhar Shahudah nada wannan matsalar to kenan yaushene ciki zai fara zaman da zasu sami cikar burinsu?.
      Uncle Uwaisu daya kasa haƙuri sai cewa yay, “Anya kuwa kuna ganin bazamu ɗauki matakiba?  Indai hakanefa zaman Shahudah da Jawaad bazai mana wani amfaniba kenan? Ko dai mu sake dubawa cikin yaran nan saimu aura masa wata?”.
     Tsitt falon yayi kowa ya kasa magana, sai dai fuskar Mummy ta nuna alamun ɓacin rai.
     Mama Atika ce ta katse shirun nasu dayin gyaran murya, cikin muryarta ta tsufa tace, “Maganar Uwaisu nakan hanya, hakama shawararsa mai ƙyau ce, sai dai akwai ruɗani a cikin hakan musamman akan ku kanku da zumincin ku”.
       “Gaskiyane maganarki mama, gashi kuma bamu da damar sako wani cikin ƴan uwanmu, duk da na daɗe daji a raina kowa nada nasa burin wlhy, suna ɓoyewane kawai dan ace sunason yaron sosai,  musamman ma Yaya Nasiru da kuke ganinsa nan ko? Humm”.
      Nanma duk shiru suka sake yi, sai Mummy ce a hasale tace, “Amma gaskiya idan akai haka ba aima Shahudah adalciba, ai kamata yay mu nema magani ko mafitar da cikin zaike zama ɗin bawai muyi tunanin mata kishiya ba, sannan ku kunama zaton shi yaron kansa zai yarda da wannan kwamacalar? Shahudah ma da yake so da yaya muka ƙulla auren nasu balle kuma yanzu? Mudai sake tunani amma ba wannan ba”.
       Kowa ya gamsu da bayaninta, duk da dai ta nuna akwai nuna taya kishin ɗiyarta a ciki.
       daga ƙarshe dai sun yanke shawarar nemawa Shahudah magani, sannan su maidota ɗakinta da wuri ko ALLAH zaisa a dace ciki ya shiga da wuri🤫🥴.

ƘWAI cikin ƘAYA!!حيث تعيش القصص. اكتشف الآن