💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh md*
Luv story😍💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*Dedicated to.....daukacin masoyan CAPTAIN ABBAS😘........ina tare daku masoyana.💔
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *3*
fita suka yi daga 'kofar palour cikin sauri don ma kar mummy tagansu,
cikin sa'a kuwa bata gansu dinba har suka je suka siyo choculate din suka dawo gida,
tarkace dayawa Abbas ya siya mata,sai dai bai hallaka kudin duka wajen siyan choculate din ba dan yana tunanin gobe idan Allah ya kaimu karta qara mar rigima irin na jiya a hanyar,shikuma be so ya sa ke dauko abu batare da kudi awurinsa ba
don gaskiya ya na kunyar sa ke tambayar mummy kudi,
Hakan yasa ya rago kusan #500 yabari a aljihunsa.Duk kayan za'ki Abbas ya siya mata bai ma siyah wa kansa komai ba sai wani sweet guda biyu da basufi #50 ba.
Adakin Abbas din suka yada zango,anan yasata agaba tana ta cinye cinyen ta,daga 'karshe suka fito suka dawo parlour,suka bar ragowan kayan adakin Abbas din.
lokacin ma daf maghrib ta yi,hakan yasa Abbas yace shi kam zai tafi masallaci.Yace itama ta je maza tayi sallah.
Toh"
tace tare da miqewa ta nufi dakin mummy.
Waya ta samu mummyn tanayi,sai kawai ta qaraso wurinta ta zagaya ta bayanta sannan ta kwantar da kanta a kafadun mummyn.
Mummyn bata kulata ba har sai da ta kammala da wayar kafin tace
"Angel din daddy daga ina haka?
Teemar cewa tayi
"Yawo mukaje da yayah""hmmm"
Mummyn tace sannan ta qara da fadin"Lalle teemah,
wato kin samu Abbas kin mnta da ni ko?
Tafada da dan murmushi akan fuskarta"har zaki je yawo ko ki fadamin?
Teeman
Cewa tayi
"sorry mummy munje siyan cho........Awwwn.......tace da wuri tare da kama bakinta ita adole kuskuren fa'da tayi.
Murmushi mummyn tayi sannan ta zagayo da ita ta gabanta
"in qarasa miki?
Tafa'di tana kallon idon teemahJijjiga kai Teemahr tayi alamun "a'a"
Meyasa ?
Mummyn ta tambaya."Yayah yace kar infada miki"
teema tafada da dan fuskar tsoro kadan.
kamo hannunta mummyn tayi ta matso da ita daf da ita,
sannan taceKun fi qarfi na ni kam Teemah ,keda Abbas bakwa jin maganata yanzu,shan za'kin nan ban sonshi kokadan amma keda Abbas baku ji ko.?
jijjiga mata kai tayi teemar tare dacewa
" mummy sorry baza mu sake ba"
Bata kula ta ba mummyn kawai ta miqe tsaye dan ji da tayi anfara qiraye qirayen sallah.
Bayan anyi sallahr isha suka hadu a dinning dan cin abinci.
Abbas yana bawa teemah abakinta tana ci,duk dama kafin ta kar6a sai yayi kusan spoon uku kafin ta kar6i daya.
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...