💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* * *MUKE TUNK'AHO*_Dedicated to_👎🏻 😍
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
When people walk away from you, let them go. Your destiny is never tied to anyone who leaves you, and it doesn’t mean they are bad people. It just means that their part in your story is over.
🅿 *30*
Koda Anty chideh taganta murmushi kawai tayi, daman tasan dolene zata dawo kodan yanda sukayi sabo sosai ma.
Haka Anty ta kora mata bayanin abinda yafaru tare da nuna tsantsar farin cikinta afili.
Dama tun asali tafison ita taza6awa Mahmud matar aure da kanta sai kuma akayi sa'a fad'uwa tazo mata daidai da zama Munira ta nuna tana ra'ayinsa.
Munira y'ar k'awar Anty ce dasuka had'u sanadiyyar maganin mata.
Domin duk wani nau'i na magani da suke anfani dashi ita da Anty chideh Mahaifiyar Munira ke musu order daga sokoto kuma sunajin dad'in maganin shiyasa suke shiri sosai.
Anty tana gani kamar samun Munirah amatsayin matar d'anta wata dama zata samu dazai sa zumuncinsu da mahaifiyar Muniran ya d'ore sosai.
Anty chideh ma sai tayata murna tare da k'arfafa mata gwiwa akan hakan.
*****
Mahmud kuwa koda yakoma bai wani dad'e agidan ba yawuche inda aka turashi awani d'an k'auye ne zaiyi bautar k'asan.Da farko Teemah murna takeyi sosai data ga yadawo d'in dan azatonta yanzun agida zai zauna amma sai yace mata ai shi tafiya zaiyi take sai murnar tata ta koma ciki.
Dayaga haka sai ya mata alk'awarin zuwa duk weekend yana dubata sai da taji haka kafin tad'an sake fuska.
Haka sukayi ta dashi aranar daya sauk'a d'in kuma duk hirar bata wuce ta Abbas ba.
Shima sai ya ringa biyeta ganin hakan tafi buk'ata.
Harda yayi niyyar k'ira mata Abbas d'in su gaisa amma sai ya fasa daya tuno cewa Abbas d'in yanzu yana bakin aiki ne.
Haka suka gama hirarsu suka rabu, yana komawa d'akinsa kamar Abbas d'in yasani sai ga k'iran sa ya shigo.
D'auka Mahmud yayi yana murmushi yace " d'an halak"
"Allah ko"?
Cewar Abbas d'in slowlyMahmud ne yaci gaba da fad'in wallahi nake gaya ma yanzu muka gama hirarka da lil sis harfa da zan k'ira layinka in had'a ku sai kuma nayi tunanin ko kana aiki ne"
" hmm ai gara ma baka k'ira ba, bayanzu zanyi magana da ita ba tukunna da sauran lokaci"
Mahmud na dariya yace
"Kai oga Abbas hukunci ne wannan ko kuma ra'ayine?" duka biyun" Abbas ma yafad'a atakaice.
Kafin Mahmud yasakeyin wata magana sai Abbas d'in ya k'ara fad'in yaushe ma kadawo ne bansani Mahmud?
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...