P89

2.7K 147 7
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_This page is specially dedicated_
_to my hard&die fans 👇🏼
*Mar-yerm, Mum Haidar, 🌹Tamama🌹, Mom inteesar(mai ku6ewa), Ummin Diga, Faateemaah🥰, Ummy Aliyuu, Nanerh, Hassan Adam Kagadama ('dan Nigeria* 🇳🇬 *)Fatee Duguri,  Nusaibateey, Maamah love, Khadija Hussain,i Fiddausi, Bebin soo, 💅🏻Zulaihart💅🏻,Ayshah🍃 Humaira,* *mj, mom Ansar, A.S, Mum Khady, Maman Muhammad, Mumyn Minal, Aneesa, Zb, Teemah baby, Fatima2(, AMINA, Maman Arfat, Maman* *Nawwara, 💋Sheerdert💋, Khadeja Abdulhameed, Baby on top, Ummu Zahra, AbdullahiZainab, Maman Zahra, Oum Farhan, Hauwa Gulumbe, HafsatJabyr, Asma'u Usman, Maryam Wakili, Mommy F's, Zainab Bala Abubakar..........anya zan iya kuwa?🤔Allah yawa ne da ku sosai, ha'ki'ka 'kauna ta da ku ta musamman ce, daku* *dama wa'danda ban fa'de su anan ba inaso kusani cewa ur COMMENTS nd* *DU'AHS na matu'kar faranta raina, Allahu ya bar* ' *kauna ya kareku ya haskaka rayuwar ku a ko'ina kufi 'karfin ma'kiyanku......INA MATU'KAR YIN KU MUTANE NAH...........IRIN UN LIMITED 'DIN* *NAN🤞🏻.* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 
_We are all here for some special reason......Stop being a prisoner of ur past..... Become d architect of ur future_ .

🅿 *89*

Anty Leesah nada mutunci sosai dan ko ka'dan bata sanyawa ranta 'kiyayyar Teemah ba sai ma 'kara janta a jiki da tayi tana kula da dukkan al'amuran ta tamkar sistern ta na jini, Abbas kansa najin da'din yanda take bi da Teemahn sosai hakan ya 'kara mata fada awajen sa kuma dalilin kenan daya sanya shima yake girmama zumuncin dake tsakanin nasu.


*****
Satin sa biyu da dawowa Abuja sai ya 'kira layin Umar sukayi magana akan zuwa katsina da ke gabansu, har suka shirya batun tafiyar ma bai sanar da Teemah ba Coz da farko be yi niyyan tafiya da ita ba amma da kansa kuma daga baya sai yaga dacewar zuwa da itan ko dan cika niyyar marigayi Mahmud ma tunda da ita uayi planning zuwa kafin rasuwar sa.

Duk da haka sai ana jibi tafiyar sannan ya sanar da ita, Kwana biyu kacal yace zasu yi acan dan haka bata sha wani wahalar shirya musu kaya ba da kanta ta za6a musu harda shi ma kayan da zai yi amfani dasu har su dawo gida.

Washe gari gidan Ummah suka wuce inda suka yi mata sallamar tafiyar ta su da yamman ramar Umar kuma ya iso Abuja inda yazo wa Teemah da tsarabar sirri daga Maman Amal, Abbas binta da idanu ya rin'ka yi Teemah kam idan sun ha'da ido sai ta murgu'da baki ta yi kamar bada shi take ba, duk yana kula da ita, kuma itan ma tasan kallon na menene shiyasa take ta kakkauda kanta gefe.

Kamar jira suke Umar ya wuce sai Abbas yace dole sai ta nuna masa abin yagani dan bai yadda da wannan sabon salon 'kawancen ba, haka ya dage akan shi bai yadda ba sai yaga menene abin da aka kawo mata.

Teemah kam tashi tayi da sauri ta koma daga bayan kujera tare da yin baya da hannun ta ta 6oye laidan sai 2seatern dake parlourn yazama atsakanin su, tana tsayen itama tace ai kuwa ba zai gani ba ai sirri ne aka kawo mata kuma babu kyau gulma da sa ido"

Abbas najin tace gulma da sa idon nan sai ya zabura da sauri zai kamo ta ai kuwa tayi 'dakin ta da gudun gaske tana dariya ta shike dayake shine akusa da ita bai kamata ba kuwa, tana shiga sai ta datse 'kofan harda murd'a lock sanna tafara maida numfashi sama-sama.

CAPTAIN ABBASTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang