💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*I _dedicated this page to my fellow *Wattpadians and Whatsapp fans* , Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa tare daku comment 'din ku addu'o'in ku, tare da conversation 'dinku na matu'kar 'karamin karsashi, wannan page 'din kyautar kune👌🏻_ .🥰
*Bismillahir rahmanir raheem*
_I learn that life is a book, every day is a new page, every month is a new chapter and every year is a new series._🅿 *84*
Kwana biyu bayan hakan Abbas ya koma Rivers dan dama hutun 1week aka bashi, kafin hakan kuwa sun sha drama da Daddyn Abuja akan tafiyar, Abbas ya so su koma tare da matar sa amma Daddyn Abuja ya hana shi, dan cewa yayi baza'a tafi masa can wata uwa duniya da yarinya ba, salon aji da'din cutar da ita acan ba, shi be yadda da zaman sun ba har yanzu yana ganin kamar Abbas mugun hali zai yi tayi mata, amma idan tana kusa da su toh abin zai zo da sau'ki kuma dole ne ya rin'ka kulawa da ita ko dan ganin idanun su ma.
Daddy gani yake kamar a bayan idanun su Abbas zai na zalintar ta ne kawai, shiyasa yace tukunna sai yaga yanayin zaman nasu kafin ta bishi.
Shi kansa daddyn cewa yayi bazai bar Abbas 'din yaringa daukan tsawon lokaci ba dole zai na zuwa duba ta.
Abbas be iya musu ko jan magana ba dan haka sai ya yi shiru kawai amma ba wai dan ransa ya so hakan ba, ya so ya sanar da Daddy babbah saboda yasan shi ka'dai ne zai sa Daddy amincewa amma kuma nauyin sa yake 'dan ji yanzun kuma ma dan kar Daddyn nasa yaga kamar yana jayayya ne da maganar sa shiyasa kawai ya fasa.
Ya dai 'dora hope 'din sa akan Teemah da tunanin ko zata yadda itan tace zata bishi, amma ko daya zo ya same ta da batun sai ta nuna 'kin amincewar ta sai ma tace zata koma gidan Ummah kawai idan ya tafi.
Bai san dalilin ta na 'kin amincewan ba, amma ba 'karamin haushi yaji ba yasan da ita ta amince toh da Daddy ma zai yi shiru akan lamarin.
Ai kuwa shima Abbas yace babu inda za taje agida zata yi ta zama ita ka'dai tunda bazata bishi ba.
Sosai ta tsorata da zaman da zata yi a gida ita ka'dai 'din saboda tuna baya da tayi, amma sai take ganin da ta bishi 'din gara ta zauna agidan in yaso idan ya tafi sai ta koma abinta ai baze sani ba.
Sosai Teemah ta 'dauki abin wasa.Haka har Abbas ya tafi da haushin ta ha'di da kewar ta da zaiyi azuciyar sa.
*****
Anty ma a cikin week 'din ta bar kano ta koma Lagos, yanzu kam zuciyar ta fes ba wani damuwa, bata da burin cutar da kowa aranta illah taga ta gyara tsakanin ta da ubangijin ta ta kuma gyara lahirar ta, gidan ta ma ba 'daya da kishiyar ta ba amma bayan ta koma Abbah ya kawo amaryar sa har gida suka wuni tare dan Abbah kansa zuwa yanzun ya yadda da cewa Anty ta yi nadama ta gaskiya ta gyara halin ta gaba 'daya ta canja su daga munana zuwa kyawawa musamman daya ga yanda taje har Abuja musamman saboda Fateemah shiyasa ma batare da fargaban komai ba ya bar amaryar sa tare da ita.Anty ma a'dan zaman nasu ne ta fahimci cewa kishiyar ta irin alkahiri ce mai sanyin hali, dangin albarka, tariga ta 'dauri aniyar kar6an kaddarar ta aduk yanda tazo mata, ta yarda cewa zata zauna zaman amana da kishiyar ta, cikin aminci da salama shiyasa ma bata damu ba ta budewa Anty Sadiya zuciyar ta gaba 'daya.
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...