P66

1.2K 99 13
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


*Bismillahir rahmanir raheem*

_People change, love hurts, friends leave, things go wrong but just remember that life goes_ _on........Love_ is _so strange.......Sometimes it becomes reason to live life and sometimes to leave life._

🅿 *66*

Umar na tsaye jingine da jikin mota, Fateemah kuwa na gefe har yanzu 'kirjinta rungume da kayan Munnira idanunta banda ruwan hawaye babu abinda yakeyi, ita kanta bazata ce ga abinda ke sata kukan ba amma yanayin datake jin zuciyarta ayanzun shi yafi komai 'daga mata hankali, tare da karya mata zuciya.

Abbas ma tsaye ya juya musu baya, sam baya son ganin hawayen Fateema koka'dan hakan na matu'kar soya masa zuciya, baya jin cewa ha'duwar su da Mahmud ze yi kyau koka'dan, jiyake kamar babu wanda ya ta6a 6ata masa rai kamar Mahmud 'din aduk fa'din rayuwarsa ,hannunsa 'daya cikin aljihunsa yayinda 'dayan yake ri'ke da wayarsa bayan ya gama 'kiran Mahmud yaga baya 'dagawa, ransa duk a6ace shi tunaninsa yabashi akan Mahmud ya'ki 'daga wayar ne dagangan dan kawai ya wula'kanta Fateemah .



*****
Cikin 'kan'kanin lokaci mutane suka zagaye wurin kowa na fa'din albarkacin bakinsa, da 'kyar akasamu aka ciro motar Mahmud 'din daga 'kar'kashin 'dayan motar se da ma suka 'daure motar Mahmud daga baya 'dauri sosai yanda ba ze motsa ba, tare da jan babban motar  zuwa baya ka'dan sannan akasamu aka raba tsakaninsu.

Da fitowar Motar Mahmud 'din kuwa sai da kowa jikinsa yayi sanyi wasu ma kauda kansu sukayi dan baza su iya kallansa ahaka ba.

Sai da ambulance yazo kafin aka ciro shi tare da duk wani abu nashi na amfani dake cikin motar aka me dashi cikin ambulance 'din zuwa asbiti.

Tun a cikin ambulance aka fara bashi taimakon gaggawa har zuwa asbitin suna zuwa kuwa aka wuce dashi A&E (Accident & Emergency) likitoci kusan uku ne suka ha'du akansa domin ceto rayuwarsa cikin gaggawa.

Da 'kyar suka samu suka daidaita numfashinsa tare da yi masa dressing 'din raunikan daya samu.

Bayan hakan ne wani daga cikin wa'danda suka taimaka masa har zuwa asbitin da kuma drivern babban motar da wani likita sune suka fara neman wanda zasu 'kira cikin 'yan uwansa.

Misscalled 'din _Oga_ _Abbas_
Suka fara gani da be wani da'de da 'kiran wayar ba dan haka shi suka fara dannawa 'kira.

Abbas na tsaye a inda yake tsayen tun 'dazu be motsa ba, ya dai 'kira layin mahaifinsa yasanar dashi cewa yashigo Lagos sannan ya'kira wani abokinsa ma sukayi magana, daganan yaci gaba da tsayuwa jira kawai yake yi yaga zuwan Mahmud gidan  tunda kam baya office dole ai idan yagama abinda yakeyi 'din gida ze dawo.

Wayarsa ce tafara 'kara alamar shigowan 'kira, yana 'dagota kuwa yaga sunan Mahmud na yawo a fuskar wayar.

Da sauri Abbas ya amsa 'kiran tare da yin shiru danjin wace 'karya Mahmud ze shirga masa.

Ga mamakinsa kuwa sai yaji ba muryar Mahmud bace ke tashi acikin wayar yake fa'din " _hello_ !
_helloo_ !!

Da mamaki da kuma izzah Abbas ya amsa da fa'din " _Yes, who is on the_ _line_ ?

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now