P58

1.1K 75 2
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_NO matter how talented you are, not everybody is going to like you, but that’s life, just_ _stay strong and always be your self_ .

🅿 *58*

Washe gari ma haka Anty Chideh tazo wurin Teemah bayan Mahmud yatafi office.

Yau ma daurewa Teemah tayi ta kar6eta hannu bibbiyu ba yabo ba fallasa ta 'dan saki fuskarta, sai de yau 'din Anty Chiddy cewa tayi da Teemah wai zata na zuwa kullum tana tayata hira tunda ita ka'dai take wuni agida, Teemah murmushi kawai tamata batare da ta bata kykakkyawar amsa ba, dazata tafi yauma Teemah iya 'kofar parlour tayi mata rakiya amma duk da haka Anty Chiddy kasa ha'kuri tayi har se data 'dago hannu ta shafi fuskar Teemah tare da fa'din _" I really love u"_ 'kasa-'kasa tayi maganar, Teemah kuwa rintse idanu tayi cikin takaici, sannan ta 6ata ranta afili hatta  Anty Chiddy ta lura da hakan amma itan kuma sai tayi murmushi ta 'kara 'dago hannu da niyyar shafo la66an Teemahn daya ke matu'kar 'dauke mata hankali a kowani lokaci sai Teemah tayi baya da sauri, Anty Chiddy ganin hakan yasa kawai tajuya ta tafi aranta tana kissima ranar da aka ce tasamu wannan yarinyar ahannu, ga dukkan alamu she is hot, tace ha'kurinta yakusan 'karewa akan yarinyar bazata iya jira har se lokacin da sukayi sabo da ita sosai ba sannan tasameta kamar yadda mum Mahmud ta ce da ita, afa'dar ta in har tace hakan zatayi zuciyarta ze kusan bugawa ne abanza, tace gara taje tasamu mum Mahmud su sake shawara dan she is in need of her, she so much love the girl yadda ita kanta batasan yaushe hakan yafaru ba, bata da buri ayanzu daya wuce taga ta samu yarinyar a hannu.

Teemah kan takaicinta na yau na musamman ne dan ita ka'dai tasan yadda takeji azuciyarta , dama akwai damuwar rashin samun iyayenta da bata yi awaya daya matu'kar tsaya mata azuci, ko da ta yiwa Mahmud maganar kuma shima sai ya nuna mata rashin damuwarsa akan hakan, sai ma ya tabbatar mata da matsalar network ne kawai bakomai ba, tana cikin wannan takaicin kuma Anty Chiddy tazo tasake jagula mata lissafi, ita ka'dai sai zuba tsaki takeyi, haushin Anty Chideh da haushin abinda tamata duk yabi yacika mata zuciyarta, wani mugun 'daci takeji aranta, taci alwashin sanar da Mahmud damunta da matar nan takeyi dan ita baso takeyi ba gara ayi mata magana ta daina zuwa gidannan tunda ita bata san girma da arzi'ki ba.

Sai akayi rashin sa'a kuma ranar Mahmud be samu yadawo gida da wuri ba, sanadiyar aiki da ya musu yawa a office, hakan yasa be shigo gidan nasa ba sai kusan 9:01pm ya dawo, alokacin ma Teemah harta fara yin bacci.

Koda yadawo a parlour yasameta kwance tana bacci, da shigowarsa kuwa ta ta shi ta zauna ta na mar barka da isowa.

Zama yayi agefenta tare da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu amatu'kar gakiye yake, Teemah ma bata bu'katan wani 'karin bayani saboda tun da yamma ya 'kirata yayi mata bayanin abinda ya ri'ke shi a office 'din, awa biyu da suka wuce ma ya 'kara 'kiranta yaji lafiyarta hakan yasa bata wani damu ba yin daren nasa, duk dama tana 'dan jin tsoro amma zuwa yanzu dolenta ta'dan fara sabawa da zama ita ka'dai agida.

Ruwa Mahmud yaje ya watso ya dawo parlourn da niyyar yi mata magana akan ta tashi ta koma bedroom ta kwanta, sai yasameta ma harta koma bacci abinta, kyaleta yayi dan shi be fiya son tada mutun ba idan yana bacci dan haka sai yaje shima yakwanta aparlourn akan doguwar kujera bayan yagyara mata nata kwanciyar tare da gabatar da duk wani al'adunsa daya saba yi kafin yayi bacci.

CAPTAIN ABBASDonde viven las historias. Descúbrelo ahora