P11

1.7K 96 4
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Wannan page d'in_ _naku ne ku_ _d'ai_ 👌🏻' _yan_ *CAPTAIN* *ABBAS FANS* *2* , _inajin_ _dad'in comment_ _d'inku har_ _6argona......__ 😍


*Bismillahir* *rahmanir raheem*


Worry is a total waste of time. It doesn’t change anything. All it does is steal your joy and keep you very busy doing nothing.

🅿 *11*

Da saurinta ta isa gurin motar,alokacin ma mummy hankalinta harya fara tashi da rashin ganin Teemahn,tana k'ok'arin fitowa kenan ta duba ta dakyau,sai taji muryarta ta k'ira ta

"Mummy"

Da sauri mummyn ta d'aga kanta ta kalleta kana tace

"Haba Teemah a ina kika tsaya fisabilillahi?

Karkata kai Teemahn tayi gefe tayi kalan tausayi,
Mummyn kuwa tacigaba da fad'in

"Wato dama haka kike wa Habibu idan yazo d'aukarki ko kisashi yayi ta jiranki ko?

"Ahh fah mummy ni na _d'auka_ wannan yayan ne shiyasa fah nak'i zuwa"

Haushi mummy taji dajin abin nan data fad'a d'in,gata gwanar fad'ar gaskiya bata fiye 6oye al'amarinta ba ita.

Cikin jin haushi mummy ta bata amsa da " toh ai sai ki _ajiye_ da kika ga bashi d'in bane kuma"

"Sorry my mum"
cewar
Teemh ta fad'a tana zagawa d'ayan b'angaren ta inda zata shiga motar.

"Wato ke bazaki bar raini da mugun halinkin nan ba ko?

Mummyn ta ce bayan Teemah ta shiga motar

"Shiru tayi bata yi magana ba.

"Inda Abbas d'inne kenan haka zaki shanya shi?
Waini sa'anki ne shi d'in?
"Kalli time fa Teemah kusan 1:30 amma sai yanzu zaki taho,kinsan tun yaushe nake anan d'in inaji ranki?

"Allah mummy bansan ke bace kika zo da bazan dad'e ba.

"Hmm"Allah ya shiryeki "

Kawai mummyn tace tare da yiwa motar key,sun iso daf wad'ancan friends d'in Teemahn sai Teemah tace "mummy sabon pegi" tafad'a tare da nuno su.

Tsayawa mummyn tayi,Teemah kuma tayi musu magana suka shigo dan har yanzun basu samu abin hawa ba.

Gaida mummyn suka yi ta amsa musu cikin sakin fuska daganan ta d'auki hanyar sabon pegin,ba hanyarsu bace amma haka sai da ta kaisu har k'ofar gidan su da taimakon kwatancen da suke mata,har suka isa,godiya sukayi mata sannan suka shiga ciki dan dukkan su 'yan gida d'aya ne.

Daga nan mummy ta juyo ta nufo hanyar gidansu dake Nyanya Quaters gujba road Damaturu.

"Allah mummy gwanda da kika zo,d'azu da wannan yayan yamin wani tsawa har sai da naji fitsari.

"Wataran ma ai har dukan ki zaiyi inde kika ce juninki rashin jine"

"nifah babu abinda namasa mummy"

Bata kulata ba,dan tasan koma me zata ce toh 6ata bakinta takeyi abanza kawai dan Teemah baji takeyi ba.

CAPTAIN ABBASOù les histoires vivent. Découvrez maintenant