P85

3.2K 139 31
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

I _dedicated this page to my fellow *FANS* all over media, Ha'ki'ka *SALMERH*_ _najin da'din kasancewa tare daku, wannan page 'din kyautar kune_ 🥰

*Bismillahir rahmanir raheem*

 
 
_Don’t let anyone’s ignorance, hate, drama or negativity stop you from being_ _the best person you can be_ .

🅿 *85*

Ko da Ummah ta yi masa magana akan hakan sai yace mata ai yana sauri ne zai wuce Ekiti state shiyasa bai tsaya ba.

Ummah kam dalilin nasa be gamsar da ita ba koka'dan sai ma sake cewa dashi tayi
" _Tashi dai ka koma gidan ka bana Abbas bafa nasan son kai da rashin adalci, ni ban san ranar da zaka daina wannan miskilancin ba wallahi, ace kabar yarinya_ _tsawon wata guda hakanan amma kuma ka zo ma bazaka tsaya ka ko duba lafiyar_ _ta ba sai ka wani ce kana sauri_ ? _Ko uzurin ta idara da sallah ma bazaka iya yi mata ba Muhammad? To ni 'din daka zo gaishe ni har da zama min a'daki 'din bamu a saurin ne?_

Ummah tana sababin tasa shi agaba har gaban mota jakar shi na hannun ta haka ta tisa 'keyar sa tare da driver dan ya sau'ke shi sannan ta koma ciki.

A hankali yake tafiyar kansa a 'kasa kamar bazai yi ba har ya isa kofar dazata shigar dashi parlourn gidan nasa, yanzun kam shigan sa kawai yayi dan 'kofar babu lock.

Ciki-ciki yayi sallamar dan daga shi kansa babu wanda yasan yayi sallama agidan balle Teemah da can cikin bedroom take.

Teemah tana bedroom tana 'dan murzawa fuskar ta powder a hankali, kunyar tambayar Ummah da tayi akansa gaba 'daya yasa ga6o6in ta yin sanyi saboda jin nauyi, atamfah tasa ajikin ta mai fulawa ja riga da skirt ne sun kuwa amshi jikinta sosai.

Har ya shigo 'dakin bata sani ba dan hankalin ta gaba 'daya ya tafi ga tunani, duk da tasan cewa zai zo shi kamar yanda Ummah ta fa'da 'din zai dawo amma duk da haka sai ta tsinci kanta cikin matsanciyar damuwa.

Tana gama shafa powder 'din ta 'dauko jambaki kenan ya shigo cikin 'dakin bata ji shigowarsa ba 'karan ajiye jaka kawai taji daya ajiye yana daga tsaye hakan yasa ta waigowa a 'dan firgice tare da mi'kewa tsaye.

Kallon juna suka tsaya yi na 'dan lokaci tsawon mintina biyu batare da kowa ya furta komai ba.

Abbas kam gani yayi ta masa mugun kyau na fitan hankali tayi 6ul-6ul da ita he wish data ganshin ace farin ciki tayi da kuwa yau sai ya nuna mata yanda nasa farin cikin ya zarta nata, amma sa6anin hakan daya samu daga gare ta yasa sam baiji da'din hakan ba.

Yaso da bata 'kira Ummah ba da kuwa yau 'din nana da taga halinsa na asali, dan tafiyar sa zaiyi Ekiti ba zai dawo ba har sai ya kammala abinda ya kaishi, dan kuwa sai ta 'kara lafiyayyan 1month koma fin hakan kafin tagan shi.

A hankali yafara takawa zuwa inda take batare da ya 'dauke idanun sa daga kanta ba.

Teemah kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah sai da taga ya kusan iso ta kafin tafara ja da baya itama ganin hakan sai Abbas ya fara magana inda yace " _wato ke duk duniya ni kadai kika  raina_ _ko_ ?

Teemah da sauri ta jijjiga masa kai alamar " _ah ah_ " dan yanda ta ganshin sosai yabata tsoro, ko 'yar fara'an da take 'dan gani akan fuskar tasa ma yau babu ita.

CAPTAIN ABBASDonde viven las historias. Descúbrelo ahora