💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
People say, Find good people & leave bad ones but it should be, Find the good in people & ignore the bad in them. Remember No One Is Perfect in This World.
🅿 *31*
Teemah kamar bata ji abinda mummyn ke fad'i ba taci gaba da rera kakanta ahankali kanta akan cinyoyinta.
Da mummy taga kamar Teemahn bazata yi magana ba sai ta sakeyin wata maganar da d'an d'agun murya tace " idan zaki bud'i baki kimin bayani toh inkuma bahaka ba ki tashi kiyi tafiyarki" .
Daga haka mummy bata k'ara yin wata maganar ba illah ido data zubawa 'yar tata tana kallonta.
Ahankali Teemahn ta d'ago kanta suka had'a idanu da mummy, take tausayinta yah kama mummy musamman yanda taga idanun Teemahn sun k'ara girma da jaaa, alamun rashin nutsuwa kaf sun bayyana agareta, sai taji sam bata kyautawa gudan jinin nata ba, bahaka yakamata tayi mata ba tunda bata ta6a samunta da irin laifin ba yakamata tayi mata uzuri, ita kanta sai ta rasa dalilin da yasa ta d'aukewa Teemahn wuta ma, amma yaxatayi, mutunci da darajar y'arta take son karewa bakomai ba.
Kauda kai tayi gefe daga kallon Teemahn, yayinda Teemahn ma tak'urawa hannayenta idanu tarasa me zata ce da mummyn, tanaso tayi mata bayani amma sam tarasa abinda zata fad'a.
Da 'kyar ta daure ranta tafara magana ahankali cikin natsuwa.
" Mum......my kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin , kar kiyi fushi dani, ni bansan wayeshi ba, last week na fara ganinsa nima, kuma duk ranar da.......dana fita saina ganshi, shine dakansa yafara zuwa k'ofar makarantarmu amma wallahi mummy ki yadda dani banta6a sauraransa ba yau d'inma bada son raina bane bayadda zanyi ne shiyasa natsaya.............daganan mummy dakatar da ita daga magana inda tace " saurara yah isa".
Tsawon mintina biyu kafin mummyn ta mik'a hannunta ta kamo na Teemahn yayinda hakan ya matuk'ar haskaka zuciyar Teemah tare da sanyayawa tasan ko ba komai hakan kad'ai da mummy tayi yana nuni mata ne dacewar mummyn nata ta d'an sauk'o daga fushin data keyi da ita........
Mummy ne taci gaba da fad'in " kina jina ko?
Da wuri Teemah ta d'aga kanta alamar " ehhh tanajinta" wa mummyn.
" Waye mahaifiyarki?
Mummyn ta tambayeta tana kallon fuskarta." kece".
Teemah ta bada amsa a sanyaye" waye ya kamata yasan damuwarki da kuma walwalarki?
" kece mummy"
" kina ganin zan iya ganin kin hau hanyar da bata dace ba in kuma barki akanta kici gaba dabinta?
Kai Teemah ta girgiza tare da fad'in " a 'a ".
Toh kin gani ko, ki fahimceni, ba ina nufin k'untata miki ko kuma takuraki bane sam, bani da burin da ya wuce inga kina farin ciki Teemah sannan duk duniya babu wanda zaiso ganin walwalarki sama dani.........amma banda ta wannan hanyar, har yanzu ke yarinya ce, da sauranki, banason tun yanzu ki fara wannan kule-kulen samarin saboda bashi da amfani.

KAMU SEDANG MEMBACA
CAPTAIN ABBAS
Fiksi UmumMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...