P74

1.2K 89 2
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated 2 my_ ❤

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Silence is the best answer of all questions nd Smile is the best reaction in all situations............ Unfortunately both never help in VIVA & INTERVIEW_ .

🅿 *74*

Anty taji da'din hakan sosai tace kamar an shiga ranta anga ni, dama ita ta jima da ganin dacewar hakan, tace ai kuwa zama be kama ta ba, shiri ne gagarumi ya kusanto ta dan ma abin yazo a 'kurarren lokaci ne in ba dan haka ba ai da bikin sai ya zama bikin 'yar gata wanda aka da'de ba'ayi irinsa ba, duk da haka de tace bazatayi 'kasa agwiba dole ne tafitar da 'yarta yanda zata zama abin kwatance.

Ummah ce ta dakatar mata da tunaninta ta hanyar shigo da 'korafi akan rashin sanar da Fateemah da Daddy be yi ba inda tace da Anty
" Sai de ina ganin kamar fa ba'a kyautawa yarinyar ba, saboda bada yaddan ta mahaifinsu ya yanke wannan hukuncin ba, ina tsoron kar a shiga hakkinta sosai dan kinsan yanzu tana da daman da zata za6i miji da kanta ba sai an za6a mata ba musulunci ne dakansa ya bata wannan damar, duk da cewa za6a matan ma ba haramun bane amma naso da an nemi yardan ta tukunna"

Murmushi Anty tayi tace " karki damu da wannan dan Allah, ni nan nasan halin Fateemah bazata ta6a yin musu ba, shima mahaifin nasu yana da tabbaci akanta ne shiyasa kika ga ya yanke hukuncinsa kai tsaye batare da wata fargaba ba saboda yasan dukkan su zasu yi masa biyayya shiyasa be damu ba, kuma yawanci idan kinga mace tayi jayayya da iyatenta akan maganar aure toh already zaki samu tana da wani me daban, Fateemah kuwa ai nasan bata da wani manemi daban ko akwai?
Anty ta ta'karasa maganar tata da tambaya.

Jijjiga kawai Ummah tayi tace "
Bana tunanain haka gaskiya"

"Toh kin gani, insha Allahu bazata damu koda ta damun ma zata sakko da yaddar ubangiji"

Shiru Ummah tayi tana tunani aranta, ita aganinta duk da haka ya kamata Teemah tasan me ake ciki, kafin lokaci yazo ya 'kure yakamata aji nata ra'ayin, ita Ummah 'daukan alhaki ne take tsoro shiyasa ma ta damu sosai, wanda tunanin nan yayi mata karan tsaye a zuci ya hanata sakat dan haka sai ta yanke shawarar samun mahaifin nasu da batun.

Anty kuwa baruwanta da'di
taji dajin wannan labarin sai de kuma wani 6angaren tana tunawa da marigayi Mahmud, amma bata bari hakan ya nuna afili ba sai kawai ta takaita tunanin da ro'ka masa addu'ar dacewa wurin mahalicci.

Sai da ta koma 'daki sannan tasha kuka har ta godewa Allahn ta, babu wanda yasani, dan haka da kanta ta ha'kura tayi shiru.

Ayanda akasa ranar  bikin Abbas 'din zai kasance kwana 'daya tsakaninsa da na Abban Mahmud domin shi nashi ranar Saturday ne sa6anin na Abbas daya kasance ranar Friday.

Da yamman ranar Mummy ta iso su Hannah murna kamar zasu ha'diye ta baran ma Teemah da tayi matu'kar missing 'dinta sosai kuka ta sanya ta rungume ta da 'kyar Anty ta lallashe ta tayi shiru.

Mummy kam dataji labarin bata wani damu ba dan ta riga da taji abakin Daddy tun a Dubai, sai de tana tunanin ko shi Abbas 'din baze amince ba tunda yanzu Teemah matsayin ta daban, bazawara ce ayanzu.

CAPTAIN ABBASTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang