P80

2.3K 105 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_My 'kungiya on top_ 🤞🏻
_This page goes to u *DBWA* i heart u mutane na._ 🥰

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Anyone can make u happy by doing something special, but only someone special can make u happy without doing anything._

🅿 *80*

Hankalinsa da idanunsa ya mayar kanta ya tsaya 'kare mata kallo, yau riga da wando ta sanya ajikin ta, yariga yasan zancen daya kawota amma duk da haka sai ya jefa mata tambayar
" _ya akayi_ ?

" _Babu komai_ " itama tace masa atakaice.

Cewa yayi
" _Toh me ya hana ki bacci har yanzu? ko rigimar da saura ne bata 'kare ba_ ?
Yasake jefa mata wata tambayar.

Goshi ta ha'de tawani yi kicin-kicin da fuska tace dashi
" Ni bana wani yin rigima.....kuma ma ai baccin nake ji ne yanzun shiyasa nazo dan inajin tsoron 'dakin can 'din"

Ido ya zaro waje akanta yace
" _Kullun ne wai ke kike jin tsoron_ ?
_Come on... go back to ur room kiyi addu'ah ki kwanta_ "

'Kafa ta fara bubbuga masa cikin shagwa6a take cewa " _ni wlh tsoro nake ji ni ka'dai_ ....

Yatsan sa 'daya ya 'dago ya nuna ta dashi yace " _bafa na son iskanci ...da 'din da wa kk kwana da zaki tsiro min da wannan iyayin yanzu_ ?

Kuka ta sanya mishi yanzun tana 'kara maimaita " _ni wallahi tsoro nake ji kuma ai ko da ma bani ka'dai nake kwana ba_ _da Hannah ne_ !

Kwafa yayi yana kallon ta kamar an matsi bakin sa sai ya sake fa'din " _kafin itan kuma fah_ ?
Shi adole tsare ta zaiyi da fa'din hakan.
Teemah kuwa cikin kwanciyar hankali ta bashi amsa da fa'din
" _ni da Yayah Mahmud_ "!

Take Abbas yaji wani mugun bugu azuciyarsa, ransa gaba 'daya yaji ya 6aci atake sai ya rintse idanun sa, wani mugun kishine yataso masa a zuciyarsa ga wani tunani na daban daya 'dar su aransa,  sai ma yake ganin kamar da gangan ta ambaci sunan Mahmud 'din dan ta 6ata ransa.

Sam shi beyi tunanin zata ambaci Mahmud alamarin ba, he thought da can baya  zata yi magana akai dan shima tunanin sa yatafi ne a lokacin datake gida a Damaturu, wancan lokacin kam yasan ita 'dayan ta take kwana kuma dashi yaso kama ta.

Be iya jura ba sai da ya dafe kansa tsabar yanda yake sara masa, 'kasa yayi da kansa ya sauke idanun sa akan system 'din dake gaban sa, tamkar wanda yaga abin tsoro aciki ko kuma system 'din ne yayi masa laifin sai ya rufe ta da 'karfi.

Kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke tsaye bai ko sake kallon inda Teemah take tsaye ba ya shige bathroom.

Teemah kam binsa  tayi da idanu domin bata san me yasa shi canjin mood cikin 'kan'kanin lokaci haka ba, amma ganin har ya shige be kula ta yasa ta tafi a hankali tayi kwanciyar ta.

Abbas haka da kayan jikin nasa bai ko rage ba yaje ya kunna shower akansa, zuciyarsa, nutsuwarsa da tunaninsa duk suka caku'de suka dagula masa lissafin sa gaba 'daya. 

Banda emergining rayuwarta da Mahmud babu abinda ke zuwa ransa alokacin, rayuwarta na baya agidan Mahmud yake tariyo wa har sai da ya kasance shine babban damuwar sa alokacin, shi kansa yasan ba dai-dai yake aikata wa ba amma zuciyarsa ta kasa yadda da cewa 'kaddarar su kenan bayan yariga yasan hakan ne nd he can't change it, he cant even erase d fact that ta ta6a zama gidan wani da sunan aure, kishin hakan ne ya hana zuciyarsa sakewa, shai'dan yariga ya yi masa mugun hu'dubar da ba za ta amfane shi da komai ba.

CAPTAIN ABBASحيث تعيش القصص. اكتشف الآن