💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍In dedication 2 my sorority sisters
*Ummie*
*Maijee*
*Zuwairah*
*Ameerah*
and my lil baby sis
*miemie.* Allah ya barmin ku....*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
God does not create a lock without its key & God does not give you problems without its solutions! *TRUST* *HIM* .
🅿 *17*
Da daren ranar da Mahmud ya iso ne mummy takewa daddy k'orafin rashin kammala makarantar Mahmud d'in dawuri tace Mahmud d'in fah sa'an Abbas ne amma dubi yanda Abbas ya jima da kammala karatun degree d'insa amma shi Mahmud sai yanzu"
Daddyn cema ta yayi shima abin ya bashi mamaki da Yah yusuf d'in ya ce masa wai Mahmud zai zo dan yin service a damaturu har hakan yasa shi tambayar dalilin dayasa har ya makara haka!
Yah yusuf d'in ne ya bashi amsa da cewa "wallahi matsalar daga mahaifiyar sa ne.
"Hmm Allah ya kyauta"kawai mummyn tace daga nan tayi kwanciyarta tana mai k'ara godewa mahallici.
*****
Mahmud ma ranar kwana yayi batare da ya runtsa ba tunani kawai yakeyi akan halin mahaifiyarsa.Tun lokacin daya kammala secondary school ta dage wai sai dai an kaishi k'asar waje yaci gaba da karatun acan shi kuma Abbansa yace sam d'ansa bazashi wata k'asa dan yin karatu ba tunda ga makarantu nan a Naija sai wanda ya za6a shi ba zai kashe kud'insa dan zuwa wata k'asa karatu ba, shi bai ma amince wa Mahmud d'in yaje ko'ina ba in dai har ba cikin Nigeria bane toh bada yawunsa ba"
Wannan dalilin ne yasa Mahmud d'in yajima bai cigaba da karatu ba,domin Mahmud d'in kansa da farko ya yi na'am da batun fita abroad d'in amma daga baya daya ga abin kanshi yake shirin cuta sai ya hak'ura kawai,
dan ganin Abbansa bashi da niyyan canja ra'ayinsa kamar yanda Anty ma ta nace akan nata ra'ayin.Ganin hakan yasa ya yanke shawarar cewa shifa zaiyi karatunsa koma a ina ne yafi mishi da wannan zaman banzan daya keyi.
Akan wannan maganar Anty har fushi tayi dashi wai dan yak'i amincewa da batun data zo dashi,kuma aganinta wai taimakonsa takeyi.
Da kyar ya sha kanta ta hak'ura sai da ya bata baki sosai akan hakan kafin ta hak'ura ta barshi.
Cemata yayi ta bari yayi wannan d'in inyaso idan yagama inzai cigaba sai ya nema awajen ai duk d'aya ne.
Ran Anty baiso ba ta hak'ura duk da irin aikin datasa akayi mata akan al'amarin amma wannan karan batayi nasara ba.
Koda Mahmud yajewa Abbansa da batun zaiyi karatunsa a Naija ba k'aramin dad'i Abban nasa yaji ba har hakan yasa ya bud'i baki yayi ta sanbad'o masa albarkatai gwanin birgewa.
UNILAG mahmud ya nema ya fara karatunsa kamar wasa sai gashi kuwa ya kammala lafiya k'alau.
Toh gurin cika service ne yayi abinsa batare da shawaran kowa ba,dan abin Antyn shima yafara damunsa gani yayi kokad'an bata son yayi ma zancen Antynsa Khadija balle yayi zancen zuwa wurinta.
Hakan yasa ya cika service d'insa da Yobe dan yana da labarin Anty Khadijan nasa a Damaturu jihar Yobe take da zama kuma abakin Antyn yaji hakan.

VOUS LISEZ
CAPTAIN ABBAS
Fiction généraleMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...