💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO**Bismillahir rahmanir raheem*
_Crushes are more beautiful than affairs because there is no_ _responsibility, no worry_ , _no commitment. Just look at your crush and smile like an_ _idiot_.
🅿 *71*
Abbas kam yanzu girma ya 'karu, ta'kama da izzah sai abinda yayi gaba, Daddynsa ne ka'dai yake 'dan kashe masa gwiwa aduk lokacin da yayi masa zancen aure walau awaya ne ko kuma azahiri, sam bayason maganar auren nan amma yarasa yanda ze 6ullo masa, babban damuwarsa kenan ayanzu shiyasa ya tsani maganar ma kwata-kwata.
*****
Kamar yanda Abbah ya yiwa Alhaji Muhammad al'kawari hakan ne ya faru domin acikin satin ranar wata laraba ya sau'ka garin Kano, Alhaji Muhammad yaji da'din zuwansa dan kuwa ko ba komai yana ganin yanzu ne ze san matsayin da 'yarsa ta take awurin Abbah, dan haka bayan gaishe-gaishe har Abbahn ya huta ma sannan Alhaji Muhammad ya nemi jin salin abinda ke faruwa daga bakin sa, Abbah kam be sanar da shi komai ba yace masa kawai tace ne zata zo ta duba iyayenta shi kuma yace ta bashi lokaci in yayi settling sai suzo tare, ganin kamar lokacin tmya'ki samuwa ne shi yasa ta taho, batun kuma cewa shine yace ta zo 'din bahaka bane, yace wata'kila bata ahirya komawa yanzu bane shiyasa ta fa'di.Alhaji Muhammad kam shiru yayi masa amma bawai dan ya gamsu ba, duba da yayi da cewar tun tsawon shekarun auren su da ita hakan be ta6a faruwa ba, toh me yasa sai yanzun kuma, yana kyautata zaton matsala suka samu amma Abbah yake 6oye masa, Alhaji be tsawaita tunani ba shima ya basar da zancen dan yasan basu ta6a samun matsala har abin yazo gabansa ba sai de lokacin auren marigayi Mahmud da ya kawo 'karar ta, wannan ma Abbah ya kawo 'karan ne dan kawo gyara wa lamarin, kafin da bayan hakan kuwa be ta6a sanin ya yanayin zamansu ba, yanzu kuwa da babu ran Mahmud be san takamam man menene matsalar su ba kuma ya san de baza'a rasa ba dole akwai wani abu, kawai de Yusuf na 6oye masa ne shikuwa ba haka yaso ba, yaso yaji abinda ke faruwa domin ya 'dan gyara al'amarin idan Allah ya bashi dama, dan shi da kanshi wani lokacin Maryam na bashi tsoro duk kuwa dayake 'yar cikin sa ne amma tun lokacin dayaji asalin 6oyayyen halinta gaba 'daya ya tsinke da lamarinta.
Alhaji aikawa yayi akayi masa 'kiran Anty (Maryam), koda tazo kuwa mamaki tayi da ganin Abbah ita kam, domin bata ta6a zaton zuwansa adai-dai wannan lokacin ba.
Sai ma taga ya 'dan murmure yanzun ba kamar da ba, fuskarsa se wani 6oyayyan annuri ke haskawa.
Alhaji Muhammad ne ya nemi jin abinda ya faru daga bakinta karo.na biyu, sanin da Anty tayi cewa yariga yasan komai yasa bata bata 6oye masa ba ta kwashe duk abinda ta aikata da dalilin da Abban Mahmud ke fushi da ita duk ta sanar dashi.
Alhaji Muhammad beyi mamaki ba dan yariga yaji duk abubuwan da yafaru 'din tun a Lagos sai de be san cewa hakan.ne ya kawo sa6ani tsakanin su ba, duk da kuwa cewa yasan ba kowa ne ne zai juri faruwar hakan ba, ko shi kanshi idan hakan yafaru cikin iyalinsa yasan da 'kyar ya iya sake zama da me shi shiyasa sam be ga laifin Abbah ba ko ka'dan sai ma ya jinjina masa da be aikata fiye da wannan ba, sake tambayar Abbah yayi inda ya tambayan ne kawai dan tabbatar wa.
Nasiha dukkan su ya ha'da su yayi musu game da zamanta kewar su, sosai yaja hankalinsu game da tsoron Allah cikin al'amuransu, sai da ya gama nasihar kafin ya baiwa Abbah dama yace yana da ikon za6an duk abinda yaga yayi masa wanda ya dace dashi, yace " _karka damu dani Yusuf, ni tamkar mahaifinka nake bazan takuraka akan komai ba, sannan ina so_ _kayiwa kanka adalci karka dube ni kowani abu daya shafeni, Maryam matar kace,_ _kuma_ _kai ke da ikon za6an sake zama da ita ko kuma akasin haka, duk ra'ayinka_ _ne_ _Yusuf_ ,
_bazan ta6a tilas ta ka dan ka zauna da ita ba dan tana matsayin 'yah agareni, wallahi_ _Yusuf da ace ni ni ke da iko da kai da bazan ta6a barinka kasake zama da Maryam a matsayin_ _mata ba, kuma ko yanzun ma kana da damar za6a ni nawa_ _shawara ne koma me ka aikata ni.kam.ina maraba dashi Yusuf domin kuwa nasan kai 'din'dan halak ne me matu'kar ha'kuri sosai wanda ina zaton da iznin Allah rayuwarka bazata ta6a birkicewa ba Insha Allahu_ ".
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...