💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍
In dedication 2 my sisters👇🏼
*Ummie*
*Maijee*
*Zuwairah*
*Ameerah*
and my lil baby sis
*Miemie.* Allah ya barmin ku....(Ameen)
Masoya nagode da addu'o'inku I'm safely arrived,nima ina muku fatan alkhairi gaba d'ayanku,duk wacce tamin addu'a Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi,Allah ya kar6i ibadunmu.👏🏻
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Mathematics may not teach us how to add love or how to minus hate. But it gives us every reason to hope that every problem has a solution.
🅿 *18*
_Back to labari_ ........
Sam Mahmud baiyi wani baccin kirki ba adaren,sai kusan 3:00 o'clock kafin baccin ya d'auke sa bayan yayi sallahr nafila sannan yayi baccin.
Sallar asubah ma da kyar ya yi ta acikin d'akinsa,saboda baccin dake fisgar idansa,yayin da su Abbas suka wuce masallaci dan sunta mar knock amma bai bud'e k'ofar ba a tunaninsu baccin gajiya ce ta d'ebesa basu san cewa kwanan zaune yayi ba shikam.
*****
Washe gari ma Mahmud bai fito ba sai kusan 10:16am
kafin suka ganshi.
Ad'aki ya samu Abbas yashiga da sallamah abakinsa amma bai tsaya jiran umarnin shiga ba ya shiga abinsa.
Abbas na zaune akan cough da system a gabansa sai kawai yaga mutum yashigo,danshi sam baiji sallamar da mahmud d'in yayi ba dan gaba d'aya hankalinsa yatafi ga abinda yake kalla.
Juyawa yayi suka had'a ido da Mahmud take sai mahmud d'in ya mik'o masa hannu.
Shima hannun ya mik'a suka tafa
"Ya ne guy u look bored,meke faruwa ne"?
Abbas d'in ya tambayeshi.
Tsaki kad'an Mahmud d'in yaja sannan yace "kabari kawai gajiya ce wlh"
"Hmm jiya danake koranka kaje kayi baccin ai iskanci kaso yimin sai gashi kuma tun ma ba'ayi nisa ba kana complain"
Abbas ne yafad'i hakan yana d'age gira sama.
Mahmud baiyi magana ba illah tashi da yayi tsaye sannan ya d'anyi mik'a,Abbas d'in sai ya sake binsa da kallo yana murmushi yace "sai wani abu kake fah kamar mace yanzu akan baccin ne kaketa wannan abin"?
"Allah baccin bai isheni ba ne"
"Sai ka koma ai ka cigaba dayi tunda bai isheka ba"
inji Abbas
"Mummy nakeso ingani ne shiyasa in badan haka ba ai ko tasowa ma bazanyi yanzu ba."
Abbas d'in ma mik'ewan yayi jin Mahmud ya ambaci mummy.
Yace "muje toh nima ban shiga ba har yanzu"
Atare suka fito suka isa babban parlour,koda suka isa babu kowa acikin d'akin hakan yasa suka zauna akujera suna d'an hira.
Zaman sun baifi da 7minutss ba saiga mummy tafito,murmushi ta sake data gansu,sai kuwa ta nufosu fuskarta cike da annuri.
Haka tazo ta zauna suka gaisa ta tambayi Abbas ya yanayin garin yace "Alhamdulillah mummy"
VOCÊ ESTÁ LENDO
CAPTAIN ABBAS
Ficção GeralMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...
