💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated to u my lovely fans.....Allah ya bar min ku_.🥰
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Failure is only a temporary change in direction to set you straight for your next success. Only_ _those who dare to fail greatly can ever achieve greatly_ .
🅿 *68*
Abbas ma porthacourt ya koma ya 'dan huta tukunna sai da yayi kwana biyu kafin yakoma Abuja.
Daddyn Abuja yaji labarin abinda sojoji suka aikata a Borno akafan ya'da labarai amma be ta6a zaton 'dansa Abbas bane ya jagoranci abin har se da Abbas ya dawo gida yake sanar dasu 'karin girman da za'a yi masa.
Mamaki sosai Daddyn Abuja yayi har yake tambayarsa dama haka akeyine, daga shigan mutun sai 'karin girma yabiyo baya.
Anan Abbas yayi masa bayani atakaice akan abinda yafaru, ai kuwa anan Daddyn Abuja yafara masa masifa akan abinda ya aikata 'din yake cewa yanzu badan Allah yarufa asiri ba inda sun kashe shi awurin fa, yace shi sam baya son rigima da tashin hankali yace shiyasa tun farko ni hankalina be wani kwanta da wannan aikin ba in ban dama Yayah Kabiru ya sa baki da wallahi bazaka yi wannan aikin ba ballantana har kaje kana rigima irin wannan, 'karin girman banza da wofi salon cuta, aidan sunga kana bada rayuwarka ne shiyasa inda bakayi hakan ba da bawani girma da sazu 'kara maka"
Shiru Abbas yayi yana sauraronsa sai da yaji yayi shiru kafin ya fara bashi
ha'kuri amma kamar 'kara zugashi yakeyi sai sake 6allewa yakeyi yana bu'de sabon salon masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, shi tsakaninsa da Allah yaji haushin
abinda yafarun.Abbas dayaga haka sai yayi shiru kawai yaci gaba da sauraransa.
Allah sai ya taimaki shi ya kawo masa Daddy Babba dayake shi be baro wajen ta'aziyar Mahmud ba sai yau kasancewar Abbah babban abokinsa ne dole ya kasance dashi a kowani irin hali.
Yana shigowa kuwa yaji me suke tattaunawa akai sai da yaji Daddyn ya kasa fahimtar Abbas ne kafin ya jefo nashi da fa'din
" _haba Hassan, ya zakayi haka kuma? dama ya shiga aikin ne dan ya zauna yaga ana abinda bashine ba_ _ya kuma sar'ke hannuwa yana kallo?_
" _Ai kamata yayi ka 'kara masa 'karfin gwiwa tare da godewa mahallici daya sanya ya tsira da ransa, bawai kasashi agaba da bambami irin haka ba, da wanne zaiji?_ "Shiru Daddyn Abuja yayi ya kauda kai gefe, hakan yasa Daddyn Teemah 'karasowa ya zauna shima.
Dan ya fahimci ran 'kanin nasa a matu'kar 6ace yake tunda har ya nuna halin ko in kula da zuwansa.Da 'kyar yasamu yashawo kansa ya sassauto.
Amma be wani saki jiki sosai ba, duk lokacin dayaga Abbas 'din sai kawai ya tuna da abubuwan da yayi taji a labarai sai yaji ransa ya 6acida hakan.
Kusan kwana uku da dawowar Abbas amma maganar bata wuce ba, su daddy suka koma Dubai da Mummy sai daga baya da ya samu Daddyn nasa yayi wata tafiya kafin yasamu ya 'dan sake a Abujan.
Sai da su Mummy sukayi kwana biyar da tafiya kafin yasamu suka zauna da su Ummah har suka 'dan tattauna akan rasuwar Mahmud wanda dukkansu abin ya ta6a rayukansu ciki harda Hannah ma da ita bataje ba kuma ma bawani sabo tayi dashi ba, amma yanda Ummah ta ke basu labarin yasa duk takejin tamkar tana gurin akayi komai, dataji batun saka Teemah ta aikata lesbian da Anty taso yi da wata mata wacce bama musulma ba ce yasa tunanin Hannah yayi saurin kawo mata cewa waccen matar ne data ganta ranar da suka kai Teemah gidan uwar mijinta dan taga yanda matar take kallon Teemah alokacin tamkar zata cinyeta 'danye bata ta6a raba 'dayan biyu itace.

KAMU SEDANG MEMBACA
CAPTAIN ABBAS
Fiksi UmumMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...