💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_This page is specially dedicated to my dear fans
Mar-yerm
Ummu Haidar
Meerameen
Ummul Abdul
maman Husna
Ummi
Tamama
Bintu kabir
Nanah
Wash........ idan nace zan k'irgo ku yawa ne dakuHak'ik'a ku na daban ne, kamar yadda soyayyar ga littafin nan yake na daban.
Allah ya bar k'auna.❤😍*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
There’s a story behind every person. A reason why they are the way they are. Think about that before you judge someone.
🅿 *21*
Aikuwa tazauna ta hau cin abincin adole duk da ranta bayaso amma haka ta ta turawa, shikuwa yana kwance abinsa da wayarsa a hannu yana ta aikin dad-dannawa, data ga ta k'oshi sai kawai tafara hawaye.
Allah ya taimake ta adaidai lokacin sai ya d'ago kai ya kalleta da niyar ganin ko tana ci d'in ne ko kuma a a, sai yaga taci ma kusan rabi amma tana kuka, suna had'a idanu kuwa ta sake kukan nata mai sautin sa ya bayyana.
Dariya tabashi shikam amma sai ya tsare bai dara ba.
Tashi yayi ya zauna kafin ya zubo da k'afafun sa k'asa sannan ya sake kallonta.
"Miye kuma na kukan?
Ya tambayeta.Batayi magana ba kawai sai ta cigaba da kukan ta abinta.
Kyaleta yayi kawai yatsaya kallonta tana kukan kusan mintina biyu sannan yasake magana "idan bazaki fad'a min ba kimin shiru inba haka ba Allah makeki zanyi"
Cikin shash-shek'a tabashi amsa da
"nah.........nah......k'oshine..........daga k'arshe taja dogon ajiyar zuciya.Sosai maganar ta d'in ya k'aramar dariya amma sai ya jijjiga kansa kawai"yarinyan na bazaki ta6a girma ba"
ya fad'a acikin ransa sai yayi murmushi agefen bakinsa."Tashi kije"
Yafad'a yana komawa kwanciyar daya tashin.
Ai tana jin haka tayi saurin mik'ewa tsaye ta tattare plates d'in ta fice da sauri, shima bayan ta yabi da kallo aransa yace
"mara kunyan banza kawai, nida kene ai a gidannan".
Tana fita ta wuce kitchen ta ajiye plate d'in sai ta wuce d'akinta,tana shiga kuwa tafad'a kan gadonta taringa kuka mara dalili amma deep down tana tunawa da Mahmud ne dan tasan da yana nan da hakan bai faru ba, da shikam tayata ci zaiyi ya,a bata abaki amma wannan shi sai bala'in mugunta.
Washe gari ma da aka zo cin abincin haka mummy tayi ta kwalla mata k'ira dolenta ta fito tazo tasami mummyn.
Mummyn cewa tayi
"yiwa yayanki magana maza yazo yaci abinci"
Baki ta tura gaba tayi kamar zatayi kuka, mummy kanta ak'asa yake bata ma lura da abinda TEEMAH tayi ba.
Ganin haka yasa Teemah juyawa tanufi d'akin nasa ranta amatuk'ar 6ace.
Knocking tai tayi daga waje shikuwa yana zaune agaban d'an k'aramin madubin d'akin yana jinta ya k'i kulata dan yasan itace inba ita ba babu mai mar irin wannan iskancin.
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...