P7

1.8K 101 2
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕


By
*Salmerh MD*

 
Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Dedicated*
*2*
_my family_ 😍

🤙🏻
Masoya ina godiya nima da soyayyar ku ga littafinnan Allah ubangiji ya barni daku.Ameen👏🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🤞🏻🤞🏻🤞🏻
Being quiet and gentle doesn’t mean you’re weak. Such people show deep, inner strength that’s under control. It’s knowing when to speak and when to listen; when to take action and when to wait. Don’t underestimate such people. *They walk* *the earth with the* *greatest strength!*


🅿 *7*

  Tana fita daga d'akin nasa waje tayi tana haki,taje tasamu k'ark'ashin wata bishiyar mango da ke acan bayan d'akunan gidan tayi zamanta dayake akwai abin zama agurin,aranta take ta tunani wai daman wannan neh yah Abbas d'in,?

Wannan ai babba ne,wata zuciyarta tace ta ce mata amma fah yah had'u,mtssew taja tsaki afili ,toh sai a gidanmu zai zauna neh,ni bana sonshi wlh, nafi son yah Abbas d'ina na dah,don mummy tace har makaranta yake rakani da islamiyah harda yawo muke zuwa,amma wannan dagani mugunta zai yi.

Haka ta zauna ita d'aya agurin tana ta tunani batare da ta je tafad'awa mummy sakamakon aiken ba.

Daddy da mummy neh kad'ai suke zaune a cikin parlourn sanda ya shigo,cikin hikima yad'anyi yawo da idanuwansa acikin ilahirin  d'akin ta yanda babu wanda zai lura da abinda ya akaita ko kuma manufar yin hakan,amma bai ganta ba,ya k'araso inda yakamata ya zauna,harya samu wuri ya zauna mummy bata ga Teemah ba, da farko ta zaci abayansa zata shigo tunda basu shigo tare ba,amma sai taga wayam,hakan yasa ta dube shi sannan tace "ina kuma 'yar aiken ta tsaya?"

"Tun d'azu fah ta taho mummy"
Abbas d'in ya bawa mummyn amsar tambayanta,fuskar sa cike da murmushi.

wayar dataje dashi d'in ya miqawa mummyn
"Harta manta wannan ma"

"Hmm" mummyn tace tare da miqk'a hannu ta kar6i wayar,sannan ta k'ara da fad'in kaga kuwa bata biyo tanan d'in ba,ta fad'a tana me daidaita zamanta, "kode yasar min wayar tayi garin haukarta ko? Mummyn ta tambaya tana kallonsa

Jijjiga kansa yayi alamar a'a.

Daddy kam bai kulasu a maganar tasu ba,don gaba d'aya ya tattara hankalinsa ne akan kallon labarai.

"Yah gajiyar hanya toh?
mummyn tasake tambayar Abbas d'in tana kallon labaran itama.

Da Alhamdulillah ya amsa mata.

Daganan mummyn tamiqe ta isa ga dinning,Bismillah ta musu tana me k'ara shishshirya wajen da kyau.

Abbas ne ya fara mik'ewa tsaye,kallon Daddy yayi sai yaga kamar ma bai san dasu awajen ba gaba d'aya,dan bashi da alamar miqewa,gaba d'aya labarun ne suka d'auke masa hankali,murmushi ya saki sannan ya isa gaban TV d'in ya tsaya k'ik'am ya tare komai,Daddy bazata kawai ya gansa tsaye agabansa,waiwaya wa yayi ya kalli gefensa tukunna kafin ya sawo da kallonsa ga Abbas d'in,dan bai san ma sanda ya bar gefensa ba.

Hannu ya ware ya dan k'wali 🖐🏻Abbas d'in dashi,tare da fad'in "kaci gidanku"

Dariyah Abbas ya k'yalk'yale dashi,yana kallo, daddyn.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now