💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO**Bismillahir rahmanir raheem*
_If couples who ar in love ar called *LOVE BIRDS,* then couples who always argue should be called *ANGRY BIRDS*..........._
🅿 *77*
Abbas kam ko daya kwanta 'din ma bacci kasa 'daukan sa yayi har kusan 'karfe 12:00 na dare.
Tashi yai yayi alwala ya dinga jero nafilfili tare da addu'o'i sosai sannan ya kwanta.
'Bangaren Teemah kuwa bacci ya mata da'di sosai har bata san lokacin da ta gangaro jikin captain ta shige jikinsa ba.
Har alokacin kuwa baccin be 'dauke shi ba, ganin ta dawo jikinsa ne yasa shi sakin ajiyan zuciya, kanta akan hannun sa ta 'dora, sai hakan ya bashi dama yake sha'kan dadda'dan 'kamshin da jikin ta ke fitarwa da kuma gashinta, a haka bacci yayi awon gaba dasu gaba 'daya.
Da asuba Abbas ne ya rigata farkawa ganin bata motsa ba sai ya sau'kar da kanta dake kan hannun sa ahankali ya mayar mata kan 'karamin sweet design pillow dake kan gadon madadin hannun nasa sannan ya tashi.
Alwala yayi ya wuche masallaci domin gabatar da sallar asubah.
'Karfe biyar da rabi ( 5:30am) Teemah ma ta farka.
A hankali ta bude idanun ta sai taga ita 'daya ce a 'dakin, tashi tayi da sauri ta nufi bayi ta 'dan kintsa kanta a gaggauce sannan ta fito da sauri ko mayafi bata tsaya nema ba ta fice abinta.Allah ya taimake ta kuwa daya fita abu'de ya bar 'kofan hakan sai ya bata daman fita cikin sau'ki.
Har a lokacin gari be gama yin haske ba amma a hakan da duru-duru ta nufi 'dakin su.
Hannah na kan sallaya bayan ta idar da sallan asubah sai taji an turo kofa an shigo, waigawa tayi sai taci karo da ita
kamar an koro ta ta shigo kanta ko 'dan kwali ma babu.Tashi Hannah tayi da sauri ta tareta tana murmushi tare da zaro idanu tace " _Ah'ah amaryar Yayah ya haka da sassafen nan kuma kamar an koro ki_?
Teemah ko kula Hannah batayi ba ta wuce kan gado ta kwanta tare da jan blanket ta rufe jikin ta dashi, tana shirin juya wa Hannah baya sai Hannah ta dakatar da ita da fa'din " _Haba Amarya har da nine a fa'dan amarcin_ ?
Sai yanzu Teemah ta bu'di baki tace
" _Hannah plz ni ki 'kyale ni, Allah bansan damuwa ki barni nayi bacci na, ina kam jiya 'kin_ _zuwa nema na kika yi dagangan kika barni na kwana acan bayan sarai kin san halin Yayah da masifa ba rakoni zaiyi ba_ "!" _Yanzu dana barki kika kwana acan din me yasame ki? Baga shi kin 'debo lada ba, ke dama zaku tafi tare da shi toh miye abin fushi dan kin kwana 'daya awurin sa_ ?
Hannah tace tana kallon ta."Bazaki gane ba ne ai Hannah dan ba ke bace"
" _oh o o'oh barni da Bilalu na ni kam kuje can ku 'karata keda wannan dodon mijin naki_ "!
Hannah tayi maganar tana kokarin tashi tsaye." _ai naje amma Yayah ya hana ni ganinki sai ma ya wani ce dani bacci kike yi irin ke ga me mijin nan.....nima ai barina kika_ _yi anan 'din na kwana ni ka'dai bayan kinsan su Rauda ba kwana zasu yi anan ba_ _amma kika tafi, in hakane nima nayi fushin mana_ "

VOCÊ ESTÁ LENDO
CAPTAIN ABBAS
Ficção GeralMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...