P22

1.4K 72 2
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO_* 😍

This page is specially dedicated to my dear sister *maman* *muhammad* saboda tsananin k'aunarki ga littafinnan gashinan kiyi yanda kike so dashi nabaki kyauta.


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*



🅿 *22*

Zuwa yanzun satin Abbas uku agidan su Teemah inda adaidai wannan lokacin  yaci kimanin rabi da quarter daga cikin hutun da ya samu na aikinsa.

Shikansa yanzun ak'age yake ya koma ya fara aikin,har ji yake zaman gidan yafara isansa dan dama bak'aramin so yake yiwa aikin nasa ba dalilin hakan ne yasa yafara k'irga ranar tafiyarsa.


*****
Mummy ce zaune akan kujera Teemah kuwa na gefenta sai zun6uro baki takeyi gaba tana guna guni k'asa-kasa, mummy kuwa ko kallon inda take ma batayi ba kanta na gefe.

Teemah data ga mummyn bata da alamun sak'k'owa sai ta k'ara risina ta had'iye miyau tare da daidaita bakinta sannan tace " mummy dan Allah kiyi hak'uri ki barni naje mana Allah idan naje bazan dad'e acan d'in ba"
tana kawo wa nan sai zamo daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyinta tayi kalan tausayi agaban mummyn nata,  mummyn ma sai tak'i ko kallon inda take balle ta san tanayi.

"mummy please"
ta k'ara fad'i kamar zatayi kuka.

Sai a sannan mummy ta juyo ta kalleta, suna had'a idanu sai ta k'ara rausayar da kanta gefe alamar rok'o.

Sai kuwa taji mummyn tace "zan barki kije Teemah amma kuma cikin 2hours zakije ki kuma dawowa, idan kika kuskura kika wuche hakan wallahi ni da ke ne agidan".


Wani tsallen da Teemah ta buga ta fad'a jikin mummyn har sai daya firgita ta.

Sai tace " haba Teemah miyeh hakan kuma kin kuwa san yanda kika tsoratar dani?

Dariya Teemahn tayi sannan tace "duk murna ce kawai  mummy"

"Hmm Allah ya shirya minke nikam Teemah"

"Ameen mummyna"

"Ki zauna kina min iyayi anan yarinya duk cikin lokacin ki ne ai ni babu abinda ya dameni"

Dawuri ai ta mik'e dataji abinda mummyn ta fad'a sai tace
"Banaje in dubo Habibu in fad'a mar zai kaini unguwa in bayanan kuma sai ki k'iramin shi awaya dan kar yayi nisa yamin cikas"
Kai mummyn nata ta d'aga mata alamar taji.

Har ta fara tafiya sai mummyn ta dakatar da ita da fad'in ta k'yale  habibun kawai dan ita bata yadda Habibun ya kai Teemahn ba , domin tariga da tasan halin Teemahn tsab, acewar mummyn wai Teemah tariga ta raina Habibun kuma koda sun fita ba bin maganarsa zatayi ba sai dai nata.

Duk mummy tayi maganar ne Teeemah na tsaye a inda tatsaya tun sanda mummyn ta dakatar da ita.

Sai da taji k'arshen maganar mummyn kafin tafara tafiya ta dawo ta zauna a kusa da mummyn.

"Toh mummy idan bashi d'in wa zai kaini?
ta jefawa mummy tambayar.

Amsa mata mummyn tayi da fad'in " zan rok'i Abbas ne ya kaiki kuma zai jira ki idan kin gama zai dawo dake "

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now