P39

1.2K 72 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Control your _Anger_ ,  it is one letter away from _Danger_ .

🅿 *39*

*BORNO STATE*

Motar su Abbas na fita daga wurin graduation 'din hanyan Maiduguri suka 'dauka basu tsaya ko'ina ba sai a wani gidan mai, koda suka sha man kuwa hanya straight suka kama batare da ya sake komawa gida ba.

Hakimce yake a seat 'din baya inka ganshi zaka zaci wani basareka ne musamman inkayi duba da yanayin zaman dayayi, yawani hakimce baya fa'din komai sai in lokacin da zai yi magana da driver ne kafin zakaji muryarsa, balle ma ba wata maganar kirki sukayi tsakaninsu ba inya wuci aikin bada umarni.

Da ikon Allah kuwa lafiya lau suka isa, Abbas saka drivern yayi ya yi tu'ki a high speed shiyasa suka isa dawuri, kuma cikin kariyar ubangiji babu wani abin da suka ha'du dashi ahanya wanda yake ba daidai bane.

Da shigarsu cikin garin Maiduguri sai suka wuche gidan ogansa me suna Oga philip, suna yin horn me gadi ya bu'de musu 'kofa.

Ko zama Abbas beyiba ya fara shirin tafiya inda ya fito oga Philip bai so hakan ba amma Abbas yace ana nemansa ne shiyasa, dolen oga Philip ya barshi yagama kintsawa yafito, lokacin 'karfe hu'du kusan da rabi na yamma 4:28pm , sallama yayi musu tare da godiyah sosai saboda Oga philip mutun ne daya cancanci ayi masa godiya, tun farko Allah ya ha'da jininsu da Abbas tun farkon ha'duwarsu awurin wani course dasuka je bada jimawa ba, yana shiyake kula daduk wani abu dayashafi Abbas 'din ko kuma zai taso ta 6angarensa yakan yi 'ko'kari sosai wajen ganin ba'a samu wata matsala ba.

Duk sau'kan da  Abbas zaiyi a maiduguri toh Oga philip ne ke bashi masau''ki ko a agidansa ko kuma wani gidan daban, shiyasa ko wannan zuwan ma da yayi sai ya sau'ka agidansa, bashi da matsala komai,inkuwa yaji an'kira sallah baya 6ata lokaci yake isa masallacin dayake akwai akusa dasu,  kuma daya sanar dashi cewa yana so yaje damaturu amma yace bazai kwana ba aranar zai dawo sai Oga philip 'din yace " toh ba matsala daganan ya ha'dashi da driver suka kama hanya suka zo damaturun atare,  yakuma ce da drivern yakula da tu'ki da kyau dan kawai saboda Abbas 'din.

Yanzun ma sawa yayi aka 'kara kai Abbas 'din airport yakuma binshi da fatan alkhairi.

Bai 'kira kowa ba aranar sai mummy ya mata sallama awaya dayake itan basu ha'du ba lokacin da zai tafi shiyasa ya 'kirata yace mata ya wuche Porthacourt.

Sai dai kuma tun lokacin da yatafi ya bar Teemah a tsaye yakejin be kyauta mata ba harma dashi kansa, sai yake jin dama ya tsaya ya kar6i leave awurin aiki kafin ya taho 'din da yasan komin yaya de zai 'dan yi kwana biyu, da zaiyi irin wannan tafiyar ba.

Amma yazaiyi hakan ma ba laifi tunda yagama abinda yakawo shi dama burinsa yaganta kuma yagantan, wannan ma satan hanya yayi shiyasa and baya son tun ba'aje ko'ina da fara aikin ba ya fara samun problem dasu shiyasa yatafi aranar batare da ya ko tsaya sun yi gaisuwar kirki da su daddyn ba dan ma kar ya shiga cikin lokacinsa.

*DAMATURU, YOBE* *STATE*

Koda fitan Teemah a'dakin direct 6angaren mummyn ta nufa dan cika umarninta, mummy kuwa bata bi bayanta ba sai ma kujera dataja tayi zamanta, su Abbah nagama cin dinner suka sha hirar yaushe gamo da kuma tuna baya da yayan nata wannan karon faran-faran batare da wani damuwa
ba.

CAPTAIN ABBASTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang