💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
Luv story😍
By
*Salmerh MD*💫 *DA BAZAR MU* *WRITER'S ASS* 💫
We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all....... *DA BAZAR* *MU MUKE* *TUN'KAHO.*
Dedicated to
*Safiyya Aliyu wakili*
(Masoyiyar asali)... marubuciyar
*MASAUQIN SO* da
*SHI NAKE JIRAH* ....on point.......
Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi
(AMEEN SUMMA AMEEN)👏🏻*Bismillahir* *rahmanir raheem*
🅿1
'Yan makaranta naga suke ta wucewa da alamar tashin su kenan daga makarantar,
daya ke yara qanana ne shiyasa mafi yawancinsu kafin ma su tashi ake zuwa zaman jiran daukan su,
wanda inka duba zaka ga motoci ne awurin suka fi yawa sai da tsirarun 'yan adaidaita,
wasu kuwa daba nisa ne dasu ba sae suke qarasawa da qafafunsu da alamar sun riga sun gane hanyar gidan dakansu basai anmusu jagora ba,
kadan daga cikinsu kuwa musamman ake xuwa dan aqarasa dasu gida koda qafan ne
,hakan yana nuni dacewa ba'a so ne suka mo hanyar
gidan su kadai......Wata yarinya ce nagani atsaye bazata wuce shekara takwas ba,tsaye take da lunching box din ta kalar pink mai kyau ahannu.....
Atsayenta ta ke bata da alamar motsawa ko ina ga dukkan alamu itama jira take azo atafi da ita gida,
Har yara sun fara watsewa sae kuwa naga wani kyakykyawan yaro matashi ne wanda bazai haura 15 yrs ba yazo tabayanta ahankali ya lalla6o karab yarufe mata idanu,
Kokadan banga alamar razana atattare da ita ba sai ma dan dariya data yi irin nasu na yara.
sannan tadago hannun daman ta ta saita hannun daya rufe mata idon dashi ta sa ke mar mintsini mai shiga jikitake ya bude mata idanun sannan yafara yarfe hannu
Kai ,
kai,
kai
"Haba ke kuwa dan Allah yafada kamar zaiyi kuka.
Dariya tafara yi masa tana qara kallonshi.
"Gaskiya yarinyar nan muguntarki ta shahara
Wama ya koya miki irin wannan abin ne dan Allah."
Ya fada yana qara kallon cikin idanunta
Da alamar mintsinin yashige shi sosaiKamo hannunta yayi daniyar su fara tafiya,zuwa gida don yasan daman bayaga dariyan toh ba magana zata sake yimar ba
Al'adarta kenan ita inde tamar mugunta toh sae de tayita dariya amma ko me zai fada bata ta6a bashi amsar maganrsa
Mu wuce gida toh"
yace da itaNa kusan yin maganinki ae badae ni kike rainawa ba.
ah ah yayah
Bakai ne karufe min ido ba"
sai yanzun ta budi baki tayi magana tana me turo bakin gabaToh dan na rufe miki ido sae akace kuma ki gutsure min fatata?
Kalli fah yanda kika yimin!
fuskar tausayi tayi dan ganin gurin yayi jaa sosai
Sorry yayah
bazan sa ke ba!!Kima sake kiga wanda zai ringa dawo da ke gida.
Yitayi kamar zatayi kuka,ta tsaya da tafiyar
Miye kuma ya faru?
Bakai bane?
Toh yi haquri taho abinki daddy's angel kinga yau akwai rana,muyi sauri muje gida kar rana ya dafa mu.
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...