P26

1.2K 81 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *26*

Tana k'arasa wankewa sai ta d'age hannunta daga fuskar tasa shima daidai sai ya bud'e idanunsa ya sauk'e su akan madubi, tacikin mirror d'in suka had'a idanu ai kuwa tana ganin yanda yakoma sai taji dariya yakamata.

Hannunta ta d'ago ta rufe bakinta dashi wani shape da goshinsa yacire ne yasa takasa rik'e dariyar tata sai ta juya kawai da gudu tabar bayin.

Bata zame ko'ina ba sai a d'akinta tana shiga kuwa ta tura k'ofar ta danna lock.

Dariya tayi taci abinta harda rik'e ciki.

Abbas kansa shima dariyar taso kamashi amma sai kawai ya maidata murmushi ya k'yale dariyar, haka ya k'urawa mirrorn idanu yana kallon kansa yanda Teemahn ta sauya mar kamanni, ita kawai yake hangowa lokacin da ta ke shafa masa cream d'in gani yake kamar yanzu ta ke yi masa hakan, sai kawai ya lumshe idanunsa bai dad'e ba ya kuma bud'esu.

Tunanin yanda zai je agyara masa kan nasa ne yafad'o masa, take sai yaji ba dad'i jiyayi ransa na so ya 6aci akan hakan, amma sai ya danne 6acin ran nasa,  taimako d'aya Allah ya mata dan dama he is about to leave kuma dole kafin ya tafin sai yayi aski, amma badan hakan ba yace " hmm"
kawai sai da yakai hannu ya na shafa kannasa kafin yace " yayarinyar nan ta gama raina ni wallahi dole inkoya miki hankali".

Tashi yayi yafara rage kayan jikinsa dayake daman bai cire su ba d'azun.

Sai da yayi wanka kafin ya fito daga bayin d'aure da towel yana tsane ruwan dake jikinsa.

Shiri yayi dolensa cikin captan mint green yasa hula ya daidaita ta da kyau ta rufe gurbin kannasa sannan ya fice daga gidan ya nufi barbing saloon d'in dayafi kwanta masa arai domin a gyara masa 6arnar da Teemahn tayi masa.


*****
Teemah ce kwance ad'akinta akan gado sai kwasar dariya take harda hawaye, ko tayi niyyan bari amma sai taji sabuwar dariya na k'ara zuwa mata seconds-seconds take sake jin wata dariya na kamata, cikin dariyar take fad'in " kad'anma kagani ai tunda dai ni kace zaka sa agaba kam sai dai mu zuba mu gani".

Juyi tayi ta kifu agadon sai tunanin yanda suka kwashe da Leemah yazo mata a washegarin  ranar daya hanata zuwa birthday.

Har kusan fad'a suka so yi da ita dan tagama saka ran Teemahn zata je sai kuma taga shiru ga shi kuma babu waya a hannun Teemah balle tak'irata sai hak'an ya k'ona ran Leemah sosai.

Haushin mitan da Leemah ke wa Teemah ne aranar ya had'u da haushin da yah Abbas ya k'unsa mata sai kawai ta fara yiwa Leemahn masifah  toh dayake Leemahn itama ba baya bace wurin magana sai suka dinga yi atsakaninsu da k'yar suka yi shiru sai da Fauzee(class representative d'insu) tace zata had'a su da Uncle d'insu (Uncle Hasheem) kafin sukayi shiru dayake suna jin tsoronsa sosai.

Har kuwa kusan kwana uku sukayi basuyin magana da junansu kafin daga baya suka zo siluka shirya kowa ya huce.



Shiyasa ko yanzun data masa hakan kokad'an batayi dana sani ba acewarta tunda itama yana had'ata fa'da da mutane gara ta rama.

Wunin ranar kuwa kaf d'insa acikin d'akinta tak'arasa shi dan k'in sake fitowa waje tayi dan ma kar su had'u da shi yaci k'aniyarta ko kuma ya had'ata da mummy.

Batama san ya fita agidan ba dan hatta islamiyah ma yau k'in kulawa tayi da al'amarinsa, Mummy cema data ga shirun yayi yawa ga kuma lokacin islamiya har ya wuce bata ga gilmawarta ba shine tazo ta bubbuga mata k'ofar, amma sai tak'i bud'ewa tace da mummyn wai kanta naciwo ne sosai shiyasa bata fito ba tanaso tayi bacci ne.

Mummyn dataji haka sai tace mata "toh Allah ya sauwak'a" sai kawai ta juya ta koma d'akinta.

8:02 pm

Abbas bai dawo gidan ba sai da dare yana shigowa kuwa yawuto parlourn domin ya gaida mummy kasancewar tun gaisuwan safe da yayi wa mummyn  basu kuma k'ara had'uwa da ita ba.

Yana gab da shiga parlourn sai wayarsa tafara ringing, dakatawa yayi da tafiyar sannan yaciro wayar ya duba mai k'iran nasa Saleem ne abokinsa wanda sukayi course tare dashi sai ya tsaya awurin yayi receiving k'iran.

Teemah na daga cikin parlourn suna zaune da Mummy sai taji ringing d'in wayarsa daga waje aikuwa ta wani razana hatta mummy sai data tsorata da yanda tayi d'in, da gudu ta tashi tayi d'aki batare da ko mummy tayiwa magana ba.

Abin ya d'aure kan mummy sosai yau Teemahn na yin wani abu kamar marar gaskiya ta kasa gane inda gakan kuma ya dosa, ko d'azaun da k'yar tasamu tafito bayan sallar maghrib sai da mummyn ta kusan 6ata ranta kafin tafito daga d'akin ahkan ma tana wani d'ar-d'ar da kalle-kallen gefe.

Shikuwa d'an dakali yasamu aga hanyar shigowan parlourn ya jingina sannan yasamu damar amsa wayar da kyau saboda wata gajiya yake ji sosai.

Duk magana ce sukayi da Saleem d'in akan komawarsu wurin aiki dake k 'ara k'aratowa, bayan sun kammala da wayar ne ya dawo ya shiga cikin parlourn da sallama abakinsa.

Mummyn ce ta amsa masa sallamar ta sa dan tuni Teemah kam ta ware d'akinta.

Sai da suka gaisa kafin mummy take tambayarsa ko akwai abinda ya had'a au da Teema ne dan ta lura da ita kamar tana d'ari-d'ari da shi.

Shi kuwa bai 6oye mata ba ya sanar da ita abinda Teemahn tayi masa yau d'in kaf bai 6oye mata komai ba.

Salati mummyn tasanya da jin abinda Teemahn tayi fad'a tafara bayan ta kammala da salatin kamar ta ari baki.

Daga k'arshe kuma sai fad'an yadawo kan Abbas d'in shima dan acewarta shi yajawo har hakan ya faru ai tana lura da shi bata ta6a ganin ya hukunta Teemahn ba duk da irin iskancin data ke masa".

Shiru yayi yan jinta sai da ta dasa aya kafin yafara bata hak'uri dak'yar kuwa ta hak'ura bayan ta hak'uran ne yasake rokon ta akan karta yiwa Teemahn komai dan Allah ta bar shi da ita zaiyi maganinta kafin yawuche.

'Kin kulashi tayi kawai ta kauda kanta gefe hakan ne yasa Abbas yagane ba k'aramin 6aci ran mummy yayi ba da jin maganar nan.

Har sai yaji yana dana sanin sanar matan da yayi ma.

Hira yafar kawo mata sama kamar yadda ya saba saboda shi daman kalaman bakinsa kad'an ne.

Mummy kuwa daga " uhmm ko ehh "
Bata k'ara wani abu akai saboda tagama fahimtar shi so yake abin yawuce dan yaga ranta ya 6aci shi adole ya kauda zancen.

Haka yayita d'an surutunsa yagama dayaga ba response mai kyau sai ya yi mata sallama ya wuce d'akinsa.

Washe gari da safe...............




_Vote, comment and_ _share pls_🤞🏻



*Salmerhn ku ce* 😍

CAPTAIN ABBASDonde viven las historias. Descúbrelo ahora