[3/14, 10:26 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
Dedicated to sister Safiyyah😍Allah yabar zumunchi.🤝
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *5*
Tun lokacin da Abbas ya tafi kuwa Teemah bata ta6a mantawa dashi ba,don mafi yawancin lokuta idan ka ta6a ta ko kamata wani abin takance "sai nagaya ka/ki da yayah,koda kuwa amakaranta ne ko gida,harta mummy da Daddy basu tsira ba,suma abu kad'an sai tace sai ta fad'awa yayah dan ita azatonta har yanzu watarana zai dawo.
Mummy bata ta6a kuskuren had'a su awaya ba don acewarta daga ta gwada k'ira mata shi sau d'aya tasan Teemah ta ringa damunta kenan kullum,shiyasa bata ma fara ba,duk da basu fasa waya da ummahn Abbas d'in ba suna wayarsu kusan kullum, haka sometimes mummy kan bata labarin irin rigimar da Teemahn keyi akan rashin ji daga Abbas d'in da batayi ba har yanzu,dariyah kawai kowaccen su keyi daga haka su shashantar da zancen.
Akwai ranar da ta ta6a saka mummy agaba da kuka wai dole suje gurin yayanta,mummy tarasa yazatayi da ita ta ce mata ai alluran nasa bai k'are ba"kuma in yak'are zai dawo da kansa,amma sam ta'ki yadda.ita wai dan dole suje su kawo shi gida,
Haka data dage sai da mummy tayi wayar k'arya ta tambaya awayar ta ce "abbas nake nema?
"Aw baya kusa?
Alluran haryanxu?
Owk toh shikenan inya dawo ace masa Teemahn shi ce ta ke nemansa.
Da mummyn tacire wayar akunnenta sai tace mata
" ai wai bayanan amma alluran ma yakusa ya k'are kuma idan ya k'are zai dawo.
Ai Teemah najin haka tafara dariyah ta fad'a kan cinyar mummyn.
Salati mummy tafara kamar gaske ,
Kai abbas d'in nan bayajin magana ,ashe yawo yatafi abinsa ya kyale angel d'ina agida.
D'ago kai Teemah tayi ta kalli mummyn
"Mummy ke ba yayanki bane?
"A'a Teemah" mummyn tafad'a sannan ta sa hannu ta d'ago Teemah ta tsayar da ita agabanta.
"Mummy yah abbas fah sunansa ke kuma kina ce mishi "Abbas"
Kumatunta mummyn takama duka 6angare biyun tana mata murmushi.
Teemah "Abbas d'ana ne ba yaya na ba.ke kuma kinga ai ke k'arama ce.K'anwarshi ko?
Kai TEEMAH tad'aga wa mummyn tana d'an smiling itama.
"Yauwa my angel
"maza jekiyi home work d'inki ko"
mummy is sleepy"
Da haka mummy tasamu ta kora ta daga wurinta dan tasan inba hakan tayi ba to hirar bazai ta6a k'arewa ba.
Teemah da fara'arta ta fita daga d'akin mummyn ta nufi nata.Yau farin ciki ta keji har aranta don yayah yace zai dawo in allurarsa suka k'are.
Ai kuwa daga ranar tafara lissafin ranar da abbas d'in zai dawo.ita kadai tayi ta ware rana amma kullum shiru ba labarinsa.
"Mummy gobe yayah zai dawo ko"?
Kullun sai tambayi mummyn,amsar mummyn kuwa baya wuce "bansani ba nima Teemah"dan bata so tafiye yi mata k'arya.
ESTÁS LEYENDO
CAPTAIN ABBAS
Ficción GeneralMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...
