P82

2.1K 175 20
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~Dedicated 2 all *CAPTAIN ABBAS COMMENTER'S* na nesa dana kusa, ha'ki'ka kuna sani nisha'di marar iyaka~. 🥰

*Bismillahir rahmanir raheem*

  _it takes just 3 seconds 2 say i luv u, 3hrs trying to explain it, nd it takes a whole life time to prove it_ .

🅿 *82*

Wani sabon towel ya 'dauko ya shiga bayin dashi a hannunsa, Teemah naganin sa sai ta juya da sauri tana gunguni 'kasa-'kasa.

Kan kafa'dar ta Abbas ya ajiye towel 'din yana murmushi ya juya shima yafita a hankali aransa yake ayyana " _banda shirmen ta miye kuma yarage harda wani 6oye jiki_ ?

A hankali tafito bayan ta 'daura towel 'din, kamar wata me tsoron taka 'kasa take tafiyar, sosai takejin zafi aduk lokacin data motsa jikin ta musamman yanzu da take 'daga 'kafafu tana tafiya sai take jin wani sabon azaba na ratsata, kasa jurewa tayi sai tasaka kuka tana tafiyar tana kuka, Abbas ma sai ya tsaya kallon ta domin ya nemi tallafa mata amma ta'ki sanadin haka ma sai ta 'kara volume 'din kukan nata.

Bata tsaya ba ahakan ta nufi hanyar barin 'dakin, sau 'daya ta kalli gadon sai taga ya janye bedsheet amma bai sa wani akai ba, ta6e baki tayi ta nufi hanyar 'dakin ta, Abbas kam still da idanu ya rakata dan a wannan halin yasan ko yace zai dakatar da ita ma ba sauraran sa zatayi ba nd shima dakansan ji yayi baida guts 'din tsareta a wannan lokacin ban dama sabon so da 'kaunar ta gami da tausayin ta da suka sake cika masa zuciya bayajin komai shiyasa ma ya 'kyale ta kawai.

Bayi ya kai bed sheet 'din daya cire da niyyar wankewa amma tun kafin ya kai ga wankewan yajiyo muryar ta.

Tafiyan ce ta gagare ta bayan har ta isa parlour ma sai ta zauna tare da sakin sabon kuka tana 'kiran sunan Mummy.

Da sauri ya 'karaso inda take shima ya zauna agefen ta yana tambayar ta meke faruwa.

Cikin kuka ta bashi amsa da fa'din tagaji ne kuma 'kafanta ma ciwo yake yi mata.

Koda ya nemi ganin inda ke ciwo a 'kafan nata kuma sai ta'ki ta nuna masa sai ma fa'dawa jikinsa datayi tare da sakin wani kukan.

Da kansa ya fahimci inda keyi mata ciwon musamman da yaga ta'ki nuna masa wurin sai yaji tausayin ta sosai, hannu yasa yana bubbuga bayan ta ahankali kamar yarinya 'karama yace " _daina kukan haka kinji, laifin Yayah ne ko_ ?

Kukan ta taci gaba dayi amma tana 'dan 'kara rage masa 'karfi da haka har yasamu tayi shiru sai yasa hannu ya 'dauke ta da niyyar maida ta 'dakinta, Teeemah kam cike da rigima take fa'din " _bana so ni ka barni ba ruwana dakai......._ "

Be kula ta ba har se daya dangan tata da 'dakinta kasancewar nasa gadon ba'a gyare yake ba.

Koda ya kwantar da ita kuwa zama yayi agefen ta tare da ran'kwafo da kansa kusa da fuskar ta, fuskar sa na kallon nata yasa hannun sa cikin nata ya sarke su wuri guda nata, 'dayan kuma yasa kan fuskar ta yana 'kara goge mata hawayen dake gangarowa ka'dan-ka'dan tare da tallafan kuncin ta yace
" _Stop crying owk...... ko kin fiso ki ringa 'daga min hankali_ ?
Shiru tayi bata bashi amsa ba illah hawaye.

CAPTAIN ABBASOnde histórias criam vida. Descubra agora