P51

1.2K 77 3
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 

A moment of patience in a moment of anger saves a thousand moments of regret.

🅿 *51*

'Kasa Teemah ta maida idanunta batare data yi niyyan yi masa magana ba dan rawar da jikinta keyi ma ka'dai ya isheta ba sai ta 'kara da wata damuwar ba sanadiyyar ganowa datayi cewa Abbas din zahiriyya ne ba mafarki ba, bugu da 'kari ma ita babu wanda ya ta6a ha'da jikinta dashi tunda take hatta da Abbas da Mahmud ada iya kacinta dasu surutu ne na fatar baki, amma sai taga Yah Abbas 'din yau kamar bashi ba tsoro ta keji sosai dan batasan yau kuma da wacce kalar masifar yazo ba, 'kila yau kan zaneta zaiyi tunda ranar ma bata yi magana bama ya daka mata uban tsawa ballantana yau da tayi masa dogon surutu.

Agogon hannunsa ya kalla sai yaga lokaci ya 'danja dan haka sai ya raba jikinsa da nata, hannu yasa a aljihu ya ciro wani 'karamin case ya bu'de hannunta ya sanya mata shi ahannun ya kuma rufewa.

Sai ya saketa ya juya da sauri ya nufi 'kofah taku 'daya ana biyu sai ya dakata cak ya tsaya amma be juyo ba yana kallon 'kofan yace " _ina miki fatan alkhairi arayuwar auren ki Fateemah"._

Be sake juyowa ya kalleta ba kawai ya sa kai ya fita daga 'dakin ita kuwa tsaye tayi kawai ta bishi da idanu har ya 6acewa ganin ta, kawarta da ke kwance agadon da tun 'dazu ta ke kallon ikon Allah sai ta taso da saurinta ta iso wurin Fatiman," _Fateema wai meke faruwane waye wannan 'din,? shine mijin naki ,? shi zaki aura ?"_
Ta jero mata tambayoyin 'daya bayan 'daya da buri, samun amsarsu daga bakin Teemah.

Yayin da ko kallon kirki bata samu daga Teemahn ba ta dai ka'da mata kai alamar kawai alamar _"a'a"._

Kwafah yarinyar tayi yarinyar sannan ta sake fa'din _"meaning"_!!!

Shiru Teemah tayi kamar ma bada ita yarinyar keyi ba.

Data ga haka itakuwa sai kamo kafa'dar Teemahn da nufin dawo da attention 'din Fateeman zuwa gareta.

Teemah dan haushi sai ta dallah mata harara take takuma juya kanta da nufin _kin_ _dameni_ sai taci gaba da kallon 'kofar da ya fita 'din ji take tamkar zata ganshi yasake dawowa.

Yarinyar bata damu ba sai ma wasu tambayoyin data sake bin Teemahn da shi.
" toh wanene shi naji yana cewa fatan alkhairi ko minene dai namanta, dan Allah ki fa'da min waye shi ?
Tafa'da tare da dawowa ta fuskanci Teemah
dan ita harga Allah bata san shi ba bata ta6a ganinsa bama ' kawar Fatima ce da suka ha'du lokacin sunje yin wani programme a (Y C A) Yobe Childrens Academy, bata ma san ina yarinyar tasamu labarin bikin ba shine harta wani zo da sassafe ita adole me 'kawa, dan ita Teemah bata gayyaci kowa ba, 'kawayenta na makarantar su ma duk zuwan kansu ne Teemah 'kin yin gayya tayi wai bata son damuwa, mummy tayi-tayi da ita harta gaji gaskiya ba laifi Teemah akwai taurin kai, akan hakan Mummy takan ce mata " mutum fah  rahama ne Teemah ko su ka'dan ne ki daure ki kai musu invitation card 'din ai zasuji da'di"
Teemah azuciyarta cewa take " sun da'de basuji da'din bai ndai har se naje na gayya toh su ne"
dolen mummy ta ha'kura ta 'kyaleta kawai akan ra'ayinta, dama ita Mummyn so takeyi Teemah tasamu masu 'debe mata kewa amma tunda ta'ki sai mummyn ta kyaleta.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now