P60

1.3K 79 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Indedication to all muslim Ummah..... brothers and sisters in islam_ *HAPPY EID'EL* *KABEEER* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 
_Ability is what u’re capable of doing, motivation determines what u do, and attitude_ _determines how well_ _u do it._

🅿 *60*

Da yamma Mahmud yadawo gidan kamar yanda yasaba dawowa a mafi yawan lokuta, kallo 'daya yamata ya fahimci bata cikin hayyacinta duba da yadda idanunta suka 'kan'kance suka kuma yi ja tare da yin luhu-luhu, ga kuma fuskarta ma data nuna alamun kumburi 6aro-6aro musamman saman idanunta.

Da ta bu'di baki kuwa tayi masa barka da dawowa sai gaba 'daya yanayin nata yasake rikita hankalinshi, domin muryarta ma adashe take da 'kyar ta harha'do maganan ta furta masa.

Tambayarta yayi abinda ke damunta cikin kulawa tare da ri'ko hannayenta zuwa kusa dashi.
'Kasa tayi da idanunta ta kasa furta masa komai, sai ma wani sabon kuka daya kubce mata.

Arikice yajata ya ha'de ta da jikinsa ya rungumeta tare bubbuga bayanta ahankali, shikanshi ji yayi hankalinsa ya tashi tsoronsa 'daya kar Fateemah tafara gajiya da zama da shi ayanayin da yake ciki ne, abinda kawai tunaninsa yabasa kenan dan haka sai yabarta ajikinsa tayi ta kukanta son ranta harta gaji tayi shiru tafara sau'ke ajiyan zuciya.

Sai a lokacin Mahmud ya 'dagota daga jikinsa ya zuba mata idanu yana sake karantar yanayinta.


" _me yasami Fateemah na ?,pls sanar dani me aka miki, waye ya ta6a minke ?_ 'daya bayan 'daya ya jero  tambayar ta sa cikin natsuwa wanda hakan yasamo asali daga karyewar da zuciyarsa tayi shikanshi jinsa yayi gaba'daya yayi laushi ganinta awannan yanayin, baya so hasashensa ya kasance gaskiya, domin in har hakanne yasan tashin hankalinsa yazo kenan.

Kanta ta komar kan 'kirjinsa tayi shiru domin aha'ki'kanin gaskiya ita bata san me zata ce dashi yasa meta ba.

_" please Fateemah ki sanar dani damuwarki kinji I'm always here 4u, nima hankalina_ _yakasa kwanciya,  zargin kaina nakeyi akan duk wani abinda ya sameki_ _nakan rasa sukuni nima pls daure ki sanar dani kinji"_

Yanzun ma shiru tayi masa sam bata da niyyan bashi amsa ko labari dangane da abinda yafaru tsakaninta da Anty. Ko dan kasheta data ci alwashin yi akan hakan, ita kuwa ba mutuwar take tsoro ba ayanzun dan akan wannan 'kazamin aikin da suke son tayi tanaji gara mutuwan yafiye mata sai de ahalin yanzu bata so mutuwa ta risketa batare data san ainihin meke faruwa da iyayenta ba, tanaso taji daga garesu taji meyasa ta daina samunsu awaya kuma suma suka daina nemanta suka manta da ita, abinda ke gabanta kenan awannan lokacin.

Ahankali cikin sanyin murya ta furta " _Yayah_ !"

Sai ya amsa mata da irin yanayin data ambace san da fa'din
_" Na'am matar_ _Yayah"!_

Murmushi maganar tasa yasata jin ya kwaikwayi kalar muryarta sai ta 'kara yin luf akan 'kirjin nasa ta lumshe idanunta sannan taci gaba da fa'din " _Mummy da Daddy na sun manta dani ko_ _Yayah_ ?

'Dagota yayi daga kan 'kirjinsan da sauri sai yace mata  _" waya gaya miki Mummy sun manta dake,?  Mummy kullun idan muka yi waya sai tace in gaisheki hakama_ Daddy shima yake fa'damin kullum"

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now