💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated_
_2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Sometimes we must get hurt in order to grow, we must fail in order to know, sometimes our vision clears only after our eyes are washed away with tears.
🅿 *12*
Washe gari kuwa Abbas da sassafe ya fice agidan,ko da Teemah tayi shirin makaranta ma sai dai kud'in adaidaita mummy tabata, ranta ma baya son hawan adaidaitan amma babu yanda zatayi tunda Habibu bayanan.
Haka taje ta tari adaidaita ya kaita makarantar,koda aka tashima haka tadawo,amma sai bata dawo dawuri kamar yanda tasaba dawowa kullum ba,koda tadawo d'in kuwa zube wa mummy tayi ajiki da fitina wai kanta na ciwo saboda tsayuwan data yi abakin titi dan jiran adaidaita,gakuma gari akwai zafin rana sosai.
Haka mummy yau kam tayi ta biye mata,dan gaskiya ta d'an tausaya mata ganin yanda duk tayi sanyi.
Ranar ko islamiyah ma batajeba,sai da aka nema mata panadol tasha tayi bacci kafin nan ta warware.
Wasegari ma ba taje makarantar ba,k'in zuwa tayi,ganin haka yasa d following day
Mummy ta kaita ta kuma d'auko ta,next kuma ta tafi a napep Abbas ne yakawota gida.Kwanan daddy biyar ya dawo,Abbas ne yaje har maiduguri ya d'auko sa zuwa gida,dayake daman tafiyar ba wata qasa bace yaje, lagos ya tafi batun kasuwancin su da suke yi kusan atare shi da yayan mummy,tare ma ake sauk'e musu kaya,yayan mummyn acan yake da zama shida iyalansa.
Dawowar daddyn Teemahn ne yake sanar musu cewa ai Mahmud (d'an yayan mummyn) anan zai zo yayi service d'insa kuma nan da two days zai iso,nextweek zasu shiga camp.
Mummy dataji wannan batun kawai sai ta fara hawayen farin cikin zata ga jinin d'an uwanta bayan tsawon wasu shekaru,babu wanda ya hana ta kukan dan daddy ne kad'ai yasan dalilin kukan nata,Abbas da Teemah kam babu abinda suka sani dan haka suka zuba mata idanu,Abbas mamaki yake yi akan dalilin kukan nata daga jin zasuyi bak'o..............kodai.......kodai.......
Teemah kam dataga mummynta na kuka,da farko itama tsayawa tayi kallon mummyn amma daga baya itama sai ta fara kukan dan bata ta6a kallon mummy tana zubda ruwan hawaye ba tunda tayi wayo.
Mumm ganin da tayi y'arta na taya ta kukan sai ta yi k'ok'arin dakatar da nata hawayen,tana murmushi.
Janyo Teemah tayi ta rungume ta kiyi shiru,ki daina kuka kinji,kukan farin ciki nakeyi Teemah cikin ikon Allah bayan wasu tsawon shekaru zanga wani daga cikin danginah,Teemah jinin d'an uwana,maganar take tana murmushi amma still hawayenta bai daina zuba ba,kana ganin yanayinta zaka gane tana cikin wani irin yanayi ne marar misaltuwa.
Daddy ma ido ya zuba mata yana k'ara jin tausayinta acikin ransa.
Sallar la'asar ne ya tada su awurin,Daddy da Abbas suka wuce masallaci,Teemah kuma da mummy kowa ta nufi d'akinta.
Kafin isowar Mahmud d'in mummy akullum annurinta k'aruwa yake yi,komai tana yinsa cikin walwala da farin ciki,da ka ganta kasan annurin daya ke kwance asaman fusakrta har cikin zuciyarta yake,musamman yau daya kasance suna saka ran isowarshi agobe.

YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...