P55

1.3K 72 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_In dedication 2 my_ _lovely Family._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 
*_Friends,* *Health* & *Love* ......... _These_ 3 _things_ _don’t come with a_ _price tags, but when we lose then we realize the *COST* ._

🅿 *55*

A kwana na hu'du da auren nasu, da dare suna cikin bacci Teemah taji tamkar ana tashin ta abaccin, ahankali tabu'de idanunta sai kuma taji tsoro ya shige ta karab 'daya, zaune ta tashi afirgice tana rarraba idanu tare da yin salati acikin zuciyarta.

Matsawa tayi jikin Mahmud ta sake kwantawa tare da shigewa cikin jikin sa kamar wata 'yar baby tayi luf amma still sai taji hakan be yi mata ba, jitayi zuciyarta na fisgarta zuwa wani abu daban daya girmi tunanin ta, hakan kuma sai yasa tsoron ta yasake 'karuwa, danne fuskarta ta 'kara yi sosai ajikin katifar haka zalika kafafunta da hannayenta duk ta baibaye su ajikin Mahumd 'din.

Dole tasa Mahmud sai da ya farka daga baccin daya ke yi, yana farkawa kuwa idanunsa ya sau'ka akanta mamakin abinda yasata yin hakan yayi, sai kuma yaji jikinta da 'dan 'dumi ka'dan, tunani yayi ko bata jin da'di ne, 'kila ko zazza6i ke damunta.

Yun'kuri yayi da niyyar tashi sai yaji ta 'kara 'kan'kame shi kamar me tsoron kar ya gudu ya barta, _" Fateemah"!,_
Ya 'kira sunan ta ahankali adaidai kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi.

Teemah kuwa bata amsa ba sai ma 'kara yin luf datayi tana mai 'ko'karin cusa kanta a'kirjinsa.

_" meke damunki ne_ _Fateemah?"_

Shiru ba amsa.

" _Zazza6i kike jine_ ?"
Yasake tambayarta.

Yanzun ma shiru be samu amsar tambayarsa ba.

Mahmud binta yayi da idanu mamakinsa na 'kara yawaita, ganin bazata yi masa magana ba sai ya koma ya kwantar da kansa akan pillow ya barta ayanda ta ke so 'din, yace 'kila sanyi take ji ne shiyasa, dan in bahaka ba yasan Fateemah baza tayi haka ba, tunda ba yau ne farkon ranar da suka kwanta tare ita ba, be wani da'de da kwantar da kansa ba yaji hannunta akan a'kirjinsa tana shafawa ahankali.

Rintse ido yayi tare da fa'din " _innalillahi_ _wa_ _inna ilaihiraji'un, wai meke faruwa_ _ne?,meke damun Fateemah? , kardai ina shiga hakkin  Fateemah azaman mu da ita batare da na sani ba?, amma har yaushe Fateemah tayi wayon da zata san haka?, this is unbelie..........."._

Tunanin sa ya yanke ne lokacin daya ji numfashin ta awajen kunnansa, ga dukkan alamu tayi nisa acikin yanayin da take 'din, dan ko daya 'dan matsar dakansa ma sake biyo shi tayi da nata kan da azama.

Afirgice ya mi'ke da 'karfinsa sanadiyyar wani sabon salon daya ji take 'ko'karin yi masa.

Dafe kai yayi tare da zuba mata idanu   yaga yadda hannunta ke yawo akan gadon a inda ya 'daga jikinsa ga dukkan alamu shi take lalu6awa
" _Fateemah!,_
" _Fateemah_ !!........
_Tashi kiji...._ _tashi_ _ki gaya min_ _meya faru, meke damunki?_ Yayi maganar yana me kusanta kansa da kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi da kyau koda kuwa bancin me take yi dole zata jishi.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now