P69

1.7K 116 20
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


_Dedicated 2 my family._

*Bismillahir rahmanir raheem*

_God is the best listener and you don’t need to shout, nor cry out loud. B’coz he hears even the very silent prayer of a sincere heart..........._

🅿 *69*

Yanda yayi maganar atsare dole yasa ta goge hawayen nata ta ringa ajiyan zuciya kawai ahankali.

Hotel 'din da ya kwana anan suka koma yace tajira shira shi yaje ya nema musu flight 'din zuwa Abuja sannan yadawo.

Ummah na zaune a parlour tana kallon wani Hausa Movie kawai taji muryar Abbas nayi mata sallama kamar daga sama.

A mamakance ta amsa sallamar tare da maida dukkan hankalinta gareshi.

Fuskan nan atamke  ya 'karaso ciki Ummah da mamaki take dubansa ganinsa ayau 'din bayan be da'de da tafiya ba, baya ga haka ma tasan yana da uzuri acan, mamakinta ne ya 'karu ganin Teemah ta shigo da sallamar ta itama kanta a'kasa ta 'karaso wajen Ummahn.

" _Ah'ah, Teemah kune tafe_ ?
_Keda waye haka_ ?

Ummahn ta tambaya tana me waro idanu ko zata ga abokin tafiyan Teemahn tare da kamota ta zaunar da ita kusa da jikinta.

Abbas kam 'dauke kai yayi tamkar be san da zancen ba dayaga hakan ma be masa ba sai kawai ya mi'ke ya wuce ciki.

" _Keda waye kuka zo ne Teemah naga shiru har yanzu banga kowa ba_ ?
Ummah ta sake tambayar Teemahn akaro na biyu.

" _Ni da Yayah ne muka_ _zo_ ?
Teemah ta bata amsa ahankali.

Da wuri Ummah tace mata
" _wani Yayahn kenan_ ?

Sai tace
" _Yayah Abbas_ "

" _Abbas dai_ ?
Ummah ta sake tambaya da mamaki.

Kai Teemah ta 'daga mata alamar _ehhh_ .

" _Toh garin yayah haka ta faru_ ?
_a ina kuka ha'du_ ?
_Ko ke kika ce masa zaki zo nan 'din, ina_ _ita Antyn_ _naki_ ?

Shiru Teemah tayi dan bata san wanne daga cikin tambayoyin Ummahn zata fara amsawa ba.

Ganin haka yasa Ummah kam ta fassara shirun da abinda hasashen ta ya bata.

Kafin tayi magana sai ga akwati an shigo da shi wanda kallo 'daya tayi masa ta fahimci cewa na Teemah ne.

Jinjina kai tayi tace
" _lallai yaron nan wato sai da yaje ya taho dake ko,_ _ai dama tun ranar da_ _yaji labarin kina can_ _naga sai wani huhhura hanci_ _yakeyi yana kauda kai gefe ashe shirin da yayi aransa_ _daban_ .
_Zai zo ai yasame ni neh sai naji dalilin_ _hakan_ "

Kallonta ta dawo dashi kan Teemah tace " _maza shiga ciki ki watsa ruwa ki huta kinji Fateemah_ "

Duk wannan dramar Teemah bata ga Hannah ba tun zuwanta Ummah ce tayi mata kwatancen inda 'dakin Hannah yake tace mata Hannahn na ciki.

Koda taje 'dakin  ma bata ganta a'dakin ba motsin ruwa data jiyo abayi ne yasa ta gane cewa tana bathroom, cigaba da tsayuwa tayi kamar me jiran abata umarni, bakomai take tunawa ba kuwa sai Mahmud tare da tausayin Anty dayayi matu'kar tasiri a zuciyarta.

CAPTAIN ABBASOnde histórias criam vida. Descubra agora