P10

1.7K 110 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
_Friendy like no_ _other_ .......
( *Mamee Hafsat* *Ndahi) I hrt u baby* *girl* ._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Ego is just like a dust in the eye ….... without clearing the dust you can’t see anything clear........,. *so clear* *the ego* *and see the world.*

🅿 *10*

A dinning ya same su gaba d'ayansu har daddy amma basu fara cin abincin ba har yanzu,da alamu jiransa suka tsaya yi.
Teemah na ganinsa tafara zare idanu tayi k'asa da kanta sarai  tasan tayi masa laifi kuma bata kyauta ba,don babu wanda zai so a kushe masa muhallinsa ballantana ma ita na raini tayi.
Ko kallon inda take ma baiyi ba yaja kujera ya zauna tare da yiwa su daddy barka da gida.

Amsawa sukayi daganan suka yi bismillah auka fara cin abincin su.

Teemah yau kam har mamaki ta bawa iyayenta ganin yanda ta ke cin abincin,ita kuwa cin k'arfin hali ta ke yi,don so take ta riga kowa barin kan table d'in tagudu d'akinta ta kulle kafin yah Abbas ya cafkota.

Kusan duk kaiwa spoon d'inta baki toh sai ta kalleshi,amma ko sau d'aya basu ta6a had'a idanu ba.

Taci abincin yakai rabin plate sannan ta tashi awurin tsam ko sallama bata musu ba.

Babu kuwa wanda yah tankata dan mamakin da ta cika su dashi,Abbas kuwa ko ajikinsa,cin abincinsa yake yi cikin kwanciyar hankali,yi yayi kamar bai san ma da ita awurin ba,koda ta mik'e d'in kuwa k'in d'aga kai yayi ya kalleta, amma tak'asan ido babu abinda ya wuce wa ganinsa,ta k'asan idanu yake ta kallon duk abinda takeyi harta gama ta tashi d'in.

Tashin bata wani dad'e ba shima yaji ya k'oshi hakan yasa ya wa su mummy sai da safe ya wuce abinsa.

Ita kuwa Teemah ruwa ma sai data bi kitchen ta d'auka sannan tawuce d'akin ta da shi,tana shiga kuwa ta danna key tana Hamdala,murna fal cikinta dan tana ganin ai ta tsira.

Ruwan tasha ta ajiye ragowan agefen gadonta,sannan ta d'an rage kayan jikinta,school bag d'inta ta d'auko ta dawo ta hau tsakiyar gadon ta barbaza takardu wai nan karatun Test takeyi,batajima ba ta fara hamma,minute-minute kuwa hamman ke zuwa,tsaki tafar jerawa itama aduk sanda tayi hamman,haushin wannan cin abincin datayi yau sosai d'in nan takeji,
"ai duk wannan mutumin nan ne yasani"
tayi maganar azuciyar ta tare da biyoshi da wata doguwar tsuka.

Takai 1hr tana karatun sannan ta tattare shirgin takardun akan gadon,daga nan tayi addu'a adaddafe ta kwanta.

Washegari tana tashi kuwa sai da tayi sallah kafin taje ta yi wanka,zaman shafa mai tayi bayan ta fito daga bayin,sai da ta gama goge jikinta tukunna ta kai hannu ta d'auko man nata datake shafawa kullum.

"Awsh namanta ashe ban fad'a wa mummy ba"
tafad'i tare da dafe goshi.

Da kyar tasamu tashafa man kasancewar babu ya k'are acikin robar,shiri tayi cikin uniform d'inta,tafito ta nufi d'akin daddynta,dayake daman idan daddy yana gari shi take fara zuwa gaisarwa kafin mummy,gani tayi baya nan,hakan yasa ta fito ta nufi d'akin mummy.

Daddy kuwa tafiyace tasame shi ta gaggawa,tafiyar bazata dan jiya kusan 10:15pm aka k'ira shi,Allah ma yasa yana da passport d'insa ,so tun adaren ya k'ira yayi booking flight,6:30am yabar gidan,kasancewar 10:00am zasu tashi.

CAPTAIN ABBASOù les histoires vivent. Découvrez maintenant