💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Wannan shafin naku ne masoyan_ *_cApTaIn_ _AbbAs* _wanda na sani da wa'danda bansani ba, a duk inda kuke *SALMERH*_ _na jinjina muku_ .😍
~*LAST PAGE*~💯
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_U ll never find luv if what u ar seeking is perfection.....cuz d best qualities we have ar d ones we never see.....d worst qualities we have ar d ones we always see_ .
🅿 *94*
Sati 'daya da komawar su suka nufi Dubai inda suka yiwa Mummy diran mikiya, bazata kawai ta gansu da mamaki dan batayi zaton haka ba.
Yanayin yanda ta saki baki da ganin sun yasa suka kwashe da dariya Teemah har da ri'ke ciki taje ta rungume ta gudu tana fa'din " mu 'din ne de Mummy ba mafarki kike yi ba".
Murmushi Mummy tayi tace " kun shammace ni ne ai shiyasa"
Daddy kam daya gansu kar6an lil Mahmud yayi a hannun Mummy yana fa'din
" Masha Allah yaro har yayi wayo yace da Mummy ta bashi abokinsa su gaisa yasan cewa yana da babban aboki.
Kusa da Abbas yaje ya zauna da babyn a hannun sa ya kamo kunnan Abbas yana ja tare da fa'din wai dan yayi familyn kansa shine ya manta da shi ko a wayar ma bai fiya 'kiran sa ba sai sa'in da yaga dama....."
yana yin yanda Abbas ke neman agajine ya saka Teemah murmushi Daddy kuwa ya'ki sakin shi sai ji sukayi yace
" Daddy Annur fa na kallo kuma zai min dariya".
Sakin kunnan nashi Daddy yayi suka 'dan dara gaba 'daya, sai Daddy ya 'daga Annur sama yana 'dan jujjuya shi yana murmushi, shima Annur idanun sa na kan Daddyn kamar wanda yana gane kamar sa ne, Daddy albarka ya ta sanyawa yaron tare da yiwa mai sunan sa addu'ah kana yace daga yau ya samu aboki tunda Abbas ya 'kisa.Su Teemah kam na ganin Mummy ai sai shagwa6a ta dawo sabuwa fil, kacokam 'dawainiyar Annur ta tattara ta barwa Mummy, ita kam sai dai zuwa yawo da Abbas suje can suje nan har mantawa take yi da tana da yaro ma a gida, kwanaki ka'dan ne kawai suka fita dashi da yake ma bashi da rigima sosai indai a 'koshe yake baya kuka shiyasa ma take barin sa hankalin ta a kwance.
Satin su biyu a Dubai sai suka dawo inda suka sau'ka a Lagos gidan Anty ya barsu shi kam ya tafi hotel, duk da Abbah ya nuna rashin jin da'din sa akan hakan amma Abbas bai ce da shi komai ba dan shi haka kawai yake jin nauyin Abbah fiye da yanda yake jin na Daddy ma, har gani yake tamkar Abbah shine Father in-law 'din nasa ma, Anty ce de har yanzun ya kasa sabawa da ita da ma halayyar ta, kallon ta yake yi a komai yana ganin tamkar gaskiyar ta ka'dan ce a kullum.
Sun ziyarci gidan Umar ma inda iyalan sa suka yi matu'kar farin ciki da hakan tarba mai kyau suka samu daga wurin Maman Amal inda suka rin'ka yabon kyan Baby Annur da yaran ta, har ji suke tamkar Fateemahn kar ta tafi.
Abakin Anty suke jin labarin irin muguwar cutar infection 'din da ya ci 'karfin Anty chiddy ya ri'ke harda 'kafafun ta hatta tafiya ma bata iyawa a yanzun, mijin ta ma wai ya koreta daga gidan sa saboda asirin da ta tayi masa duk sun samu matsala hankalin sa ya dawo jikin sa kamar kowa, basu ma san inda take ba a halin yanzun.
Teemah kam yanzu ko sunan matar ma bata 'kaunar tunawa gode wa Allah kawai take yi da bai bawa Anty Chiddy nasara akan ta ba ta cimma burin ta, tasan ba dan ikon Allah ba da yanzu itama ta zama wani abu daban " Alhamdulillah" kawai take ta nanatawa tare da tuno rayuwar ta na baya, sai hawaye ya gangaro mata, fakan idanun su Anty tayi ta goge shi Abbas ne ka'dai ya lura da ita amma bai hana ta ba kawai ya 'kura mata idanu.(Allah ubangiji kayi katanga da sharrin shai'dan kasa mufi 'karfin zu'katan mu AMEEEN).

STAI LEGGENDO
CAPTAIN ABBAS
Narrativa generaleMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...