P8

1.8K 114 1
                                        

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
_my family_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Never let the experiences of your past bring harm to your future. Remember, your past can’t be altered and your future just doesn’t deserve the punishment.


🅿 *8*

Teemah kuwa tun fitar ta d'azun bat k'ara fitowa ba,bacci ne yad'auketa bayan tagama dariyar muguntar ta,ita adole in anbarta wai taga babba yanan kuka,"kai daddy ya iyah purnishment tafad'a cikin dariyar,nima fah haka mummy take min inna yi mata laifi,gashi nima yau daddy yarama min,Horhh daddy kabiya ni wallahi"

Haka tayi ta sumbatu ita kadai,har tafara jin bacci,takuwa kwanta tayi baccinta bayan tacire doguwar rigar dake jikinta.

Ba ita ta tashi ba sai kusan la'asar,tashi ta yi ta watsa ruwa tare da d'auro alwala.

Sai da tayi sallar kafin tashirya cikin uniform tafito taahiga kitchen neman abinda zata ci,duk ba wani abin kirki taciba,amma ita tana ganin hakan yafi mata akan ta zauna taci abincin.

Koda tagama kale kalen nata a kitchen d'in d'akin mummy taje,bata samera a parlourn ta ba,hakan yasa ta wuce bedroom d'in mummyn,sallah tasame ta ta nayi,amma azaman tahiya take,ganin haka yasa tawice gaban mirror tana k'ara gyara fuskarta da kyau.

Tacikin mirrorn ta hanago mummy ta yi sallama,ganin hakan sai ta baro wajen datake tsayen ta taho ga mummyn,
"Mummy natafi islamiyah"

Kallonta mummyn tayi batare data yi magana ba dan bat so ta yanke azkar d'in datakeyi,sai d'an yatsanta data d'aga ta nuno Teemahn dashi tana d'an juya shi kad'an.

"Mummy bacci ne fah ya d'auke ni shiyasa na makara'?" Tafad'a da d'an ta6e baki alamr shagwa6a dan tasan ma'anar hakan da mummyn tamata.

Jijjiga kai mummyn tayi kawai tare da d'auke idanta daga kan Teemar.

Ganin hakan yasa Teema ficewa daga d'akin,dan mummy ta gama sallamarta.

Waje tayi tanufi cikin gidan,tana fita kuwa tafara kwalla wa Habibu k'ira,shima yanaji ya taso da d'an saurinsa ya iso inda taken dan wajen da ake parking motocin gidan ta nufah ita.

"Y'ar gidan daddy ganinan ya akayi"

Cewa tayi
"yauwa malam habibu ka kaini makaranta mana, yau na makara wallahi"

baki yakama sannan yace "ta6,
"kinga kuwa babu key awurina,shiga ki kar6o key saiki zo mutafi dawuri"

Kallonsa tayi sannan tace "toh ina na wurin naka"?

"Wannan bak'on ne yafita dashi."Ya bata amsa.

"Wai yah Abbas kake nufi?"Tasake tambayarsa.

"Oho ai bansan sunansa ba."Zaro ido yayi kamar wanda yaga wani abin tsoro
"Kar dai wannan shine Abbas d'in gidan nan"ya yi tambayar yana kallonta.

"Ehh wai shine inji mummy"itama ta bashi amsa.

"Baki habibu ya sake kamawa cikin tsananin mamakin gani wannan murd'ad'd'en ne wai Abbas,ta6d'i"

CAPTAIN ABBASМесто, где живут истории. Откройте их для себя