P13

1.3K 72 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

  masoyan_ _CAPTAIN ABBAS. Kusani ina yinku irin sosai sosai d'innan,Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Free your heart from any hatred. Free your mind from any worries. Live simply. Give more. Expect less.

🅿 *13*

Da malaman suka ji ya fad'i haka sai suka ce toh  shikenan daman hakkin addini ne kuma dan gudun siga hakki ake son sauk'e shi,amma tunda yace haka shikenan,Allah ya k'ara musu hak'urin rashin dasu kayi,amma duk da haka sai sunji daga bakin manyansa tukunna,wasu daga cikin y'an uwan baban haushi sosai sukaji dan aganinsu Yusuf bak'aramin bak'in ciki yayi musu ba,amma da sukaji za'a tambayi manyansa sai suka d'an ji dama-dama dan sun zaci za'a samu sa6anin harshe ne.

Sai dai basu yi sa'a ba,dan da aka tambayi ummahn suma cewa tayi

" _a'a yanda idonta yaga jinin Baban ya zuban nan ko da sun kar6i kud'in gani zasuyi kamar jinin baban suka fansar,tsautsayi da k'addara ai abokan tafiyar dukkan wani halitta ne,babu wanda ya isa ya gujewa k'addararsa,Allah ya riga da ya rubuta inda ajalinsa yake kenan dan haka su basu da wani abin fad'a fatansu kawai Allah yah kyautata makwancin Baban"
Ummah tana hawaye take wannan maganar,kusan kowa dake zaune agun sai da ya share hawaye,duk da zuwa yanzun abin yad'an bar zuk'atansu,sun riga da sun dangana tsakaninsu da Baban yamzu addu'a ce kawai.

"Allahu akbar",

"Allahu akbar"

"Allahu akbar"

Babban malamin dake zaune agun ne  yafad'i hakan tare da jijjiga kansa,d'ago wa yayi ya kalle su gaba d'aya sannan yaci gaba da cewa

"Hak'ika wannan kad'ai baiwa ce da Allah ya riga ya halicci ahalin wannan gidan dashi,kalamanku su suka bayyana hakan,ga dukkan alamu ba wani k'arfi ne daku ba amma wannan furucin naku yah tabbatar mana da cewa wadatar zuci abokiyar tafiyar ku ne,Allah kad'ai kuka dogara dashi,Hak'ik'a agurin Allah ku masu arzik'i ne da yardarsa,Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi ya kyautata rayuwarku gaba d'aya daga yanzu har yaumul sa'a.

"Ameen-Ameen"!
sauran dake gurin suka amsa masa dashi,amma kowa jikinsa ya matuk'ar yin sanyi.

Sake kallon Ummah yayi dake faman goge hawaye tun d'azu,sannan yace
"Kuyi hak'uri insha Allahu mutuwar malam hutu ce agare shi muna mishi fatan alkhairi insha Allahu,malam mutum ne da kowa yaji wannan mutuwar tashi ta matuk'ar ta6a zuk'ata da yawan gaske,amma dukkan mu yazama mana dolene muyi hak'uri,addu'a itace gatansa ayanzu"

Babban malamin ne yasake juyowa ga ragowar ahalin Baba yasake tambayarsu,suma da wuri suka amince sai bakinsu yazama d'aya dukkansu.

Da haka taron yawatse amma har aran Alhaji Muhammad ji yayi ya kasa hak'uri da wannan lamari ji yake bazai iyah kyalesu a haka ba
amma bai yi magana awurin ba yadai bar abinsa aransa ne kawai.

Dangin Baba kuwa haushinsu k'aruwa yayi akan nada, ji suka yi kamar su rufe ummah da duka lokacin da ta ke nata bayanin,koda aka zaga yo kansu da tambayar kuwa suma dan dolensu suka amince badan ransu yasoba,dan de kar aga zak'ewa da zilamar su ne,shiyasa basu canja baki ba,tunda bau wanda yasan meke acin ran su sai kowa ya yabawa wannan zu'ri'a ta mariga yi masu sanin ya kamata da girmama k'addarsu, inka d'auke mutune biyu dasuka kasance su d'in k'anne ne ga Baba,Mal.Hadi da mal.kallah sune kad'ai suka yi maganar datake har cikin zuciyarsu ne badan komai ba sai dan saboda Allah kawai, amma saura daga ciki duk bada son ransu suka amince ba,dansu aganinsu a irin yanayin talaucin da suke ciki kud'in ba k'aramin taimaka musu zaiyi ba,basu sani ba ashe irin kud'in nan baya kawar da buk'atar mutum dan tafiyah yake kamar ana hure shi,daga k'arshe ma karasa ya akayi ne ma yak'are gaba d'aya,inkayi wasa da tunani kawai zai barka,amma bansani ba kodan basuga yadda k'arshen d'an uwan nasu yakasance bane shiyasa tsoron rayuwar bata shigesu ba,domin kafin su iso har an sada baba da makwancinsa na har abada.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now