P92

2.9K 140 10
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_A *true friend* sees d 1st tear, catches d 2nd one nd stops d 3rd.....they ar not d ones who ar there when it's convenient only...... *True friends* ar also there when it's not...Hold a true friend nd don't ever let them go coz *True friend* comes just once in a lifetime._ 🤞🏻

🅿 *92*

Abbas ma bai fiya barin ta tana shan za'ki ba saboda an gaya masa cewa hakan nada illah musamman ga mai ciki irin ta.

Koda ya koma office kuwa baya yin cikakken 1hr ba tare da ya 'kira yaji lafiyar ta ba.

Matan blocks 'din su ma na nan-nan da ita musamman saboda karamcin Abbas a wurin su.
Bata aikin komai sai yi masa girki, duk kuwa da cewa tana son yi 'din amma Abbas hana ta yin komai yake yi sai dai wani lokacin ta saci jiki tayi idan taga baya nan.
Amma da kansa yake yin komai a gidan.

Matan block 'din su ma da yake yawancin su manyan mata ne so sai suke tausayin ta da ganin 'kan'kantar ta, su kansu duk ranar da sukayi katari da ita ta 'dauki tsintsiya hana ta suke yi.

Cikin ta na da wata bakwai sannan ta sanar da Hannah a chat dan sosai zuciyar ta ta kasa daure rashin sanar da Hannah labarin cikin, duk iya 'ko'karin da ya kamata tayi amma ranta yakasa sakewa, inda suna cikin chat tace da ita " Hajiya ki fara shirin raino fa dan Matar Yayah nada ciki har na tsawon wata bakwai"

Hannah kam wasa ta 'dauki abin dan haka sai itama tace " wacce matar Yayahn kenan kike magana? Kinsan ai ni bansan ya 'kara yin aure ba".

Teemah bata ba ta amsa ba sai kawai ta 'kirata video call tana murmushi ta nuna mata cikin.

Hannah mamaki, murna da farin ciki gaba 'daya sai suka hanata magana ta bu'de baki kawai tana kallon ta. Teemah ma kallon t take yi sai dai ita murmushi ne akan fuskar ta mai sanyi.

Hannah nuna ta tayi tace wai dagaske ciki ne a jikin ki?"

Teemah cikin ta k'ara nuna mata tace " ga zahiri kuwa kina gani Hajiya"

Hannah ihun murna ta sanya tare da tashi ta nufi wurin Ummah tana 'kwala mata 'kira.

Da sauri Teemah ta yanke 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya tana dariya.

Taso ta 'kyale Hannah kawai sai dai taga suprise 'din baby kamar yanda take ganin take-taken Yayah, amma sai ta kasa jurewa saboda sam bata ga dacewan ace har tana da cikin daya kai ciki amma Hannah bata da labari ba.

B'angaren Hannah kuwa tana isa wurin Ummah ta dago wayar tana fa'din " Ummah kalla kiga abin mamaki, Fateemah na da babban ciki tace min har ya kai 7months....."
Gani tayi Teemah bata kan layi sai ta sake gwadawa amma baya tafiya, ta kira voice call shima akace mata switch up.

Ummah kuwa gaba 'daya hankalin ta ta tattara ta mayar kan Hannah jin ta kusan samun jika, ganin Hannah na jan tsaki ne yasa ta tambayar ta " meya faru?"
Sai Hannah tace " Wallahi Ummah kinga tayi disconnecting call 'din kuma na 'kira baya tafiya"
Ranta duk a jagule tayi maganar ga dukkan alamu bataji da'din hakan ba.
Ummah cewa tayi " amma kin tabbatar cewa cikin na ajikin ta?"
Sai tace " Allah dagaske ciki ne Ummah ai ta nuna min kuma tace har 7month......"

CAPTAIN ABBASTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang