P67

1.2K 89 3
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


*Bismillahir rahmanir raheem*

_Every moment of life is a step towards death......._

🅿 *67*

Ahankali suka fito daga cikin 'dakin tamkar wa'danda basu so suyi tafiyar, kawunan su duk na kallon 'kasa.

Anty ne tafara tambayar su " ya jikin nasa ? yasamu yayi bacci ne?
Ta jero tambayoyin nata ajere.

Abbas ne yayi dauriyar yin magana dan shi kam Umar yana daga bayan Abbas 'din yana faman share hawaye.

" _Muje akaiku gida_ "
Abbas yafa'da idanuwan sa na kallan gefe, sosai mutuwar Mahmud 'din ya bige shi, acikin idanuwansa ka'dai zaka gane hakan.

Anty ne ta hango Umar daga baya ka'dan da Abbas yana faman share hawaye take ta maida hankalinta gurinsa tace.

" _Umar me ya samu Mahmud kake kuka?,nunfashinsa ya tsaya ko_ ?.

Ganin Umar be tankata ba kuma be 'dago ya kalleta ba yasa ta furta " _Nashiga uku na Mahmud ya rasu Munnira_ "
Tayi maganar tare da 'dora hannu akanta, sai luuu ta zube a'kasa sumammiya.

Tsawon mintina ashirin kafin ta farfa'do inda ta tsinci kanta kwance agadon asibiti, farko idanuwan ta akan Teemah ya fara sau'ka dake gefenta azaune tayi tagumi ta 'kurawa gadon idanu, yayinda Munnira ke zaune agefen gadon da Antyn take kwance itama tayi shiru.

Ita da Munnira ne kawai a'dakin su Abbas kuwa na can suna preparation na tafiya da gawa.

Anty na farkawa ta gansu zaune jigum-jigum ai sai kawai tasa kuka wanda kukan nata ya sa suka farga da cewa ta dawo hayyacinta.
Cikin kukan take fa'din
" _Dagaske ne Mahmud 'dina yarasu ko Munnira_ ?
_Dagaske ne yarona_ _ya tafi ya_ _barni_ ?

" _Yi ha'kuri Anty dan Allah ki daina kukan nan haka nan, addu'ah zakiyi masa kinji_ "

Cewar Munnira dake 'ko'karin tallafota .

Teemah kam binsu kawai take da idanu bata san me zata furta ba sam.

Sai da aka wuce da Mahmud gida kafin Umar yaturo driver yazo ya koma dasu Anty gida, kafin nan kuwa gidan harya fara cika da mutane.


Abbah ne yace a 'dan jinkirta masa ka'dan yazo yaga gawar 'dansa da idanuwansa hakan yasa aka 'daga jana'izar Mahmud 'din sai zuwa bayan sallar juma'ah.

Kafin hakan kuwa jama'ah da yawa sun iso daga 6angarori da dama, ciki harda su Daddyn Abuja, Ummah, da su Daddyn Teemah mutanen Dubai, Abbah ma ya iso tuntuni inda ganin gawar 'dansan kwance yasa yakasa ri'ke zuciyarsa sai da ya share hawaye kusan sau uku amma be tsawaita ba dan yasan kukan bashida wani amfani koka'dan ga dukkan mamaci.
Amma shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa , 'dansa 'kwaya 'daya tak daya keso kamar ranshi amma yau gashi kwance agabansa da gawa, wanda yafishi ya amshi abinsa, Allah ka jikan Mahmud ka haskaka masa 'kabarinsa, nasan beyi gaggawa ba muma kuma ba jin kiri mukayi ba.

Dayake Ummah tariga su Mummy isowa yasa Teemah tunda taga Ummahn ta tafi ta lafe ajikinta tayi shiru gaba 'daya koman ta ya tsaya mata cak hatta tunani bata iyawa sai de idanuwa da take faman rarrabawa ko rintse idanu bata son yi saboda tana rintse idanun sai taga Yayah Mahmud nayi mata murmushi lokacin dayake kwance a hospital, hakan yasa ta 'kin rintse idanu koka'dan.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now