P54

1.2K 71 4
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

⚠ ~NOT EDITED~

_In dedication_
_2 my Famliy_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 
_Nobody wants to hear this but it's true that sometimes the person you want_ _most is the person you are best_ _without._

🅿 *54*

Mahmud shika'dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba, fuskarsa ba yabo ba fallasa lokacin daya ganta ,be yi mata magana ba kawai yasa kansa zuwa ciki itama sai ta bishi abaya ahankali bayan ta tura 'kofar.

Babbar rigarsa yacire ya ajiye sannan yakoma ya kukkule 'kofofin gidam gaba 'daya ya daqo yasameta zaune akan kujera.

Umartan ta yayi da tayi alwala taje tayi ta dawo sai ya mata nuni da dadduma ma'ana ita yake jira.

Ahankali tace masa " _banyi maghrib ba_" dan ita zaton ta sallar isha'i zasuyi.

Kallon ta yayi da mamaki ya ce " _meyasa bakiyi ba tun 'dazun"_?

" _Ni tsoro nakeji Yayah tun 'dazu fah nika'dai ce agidan kuma su Hannah tafiyar su sukayi suka barni"._! Cikin shagwa6a tayi maganar tamkar zatayi kuka.

Shi kuwa sai ya samu ya zauna yace mata ta hanzarta tayi toh dan lokaci na tafiya yace kuma kiyi harda isha'i ma.

Sai data jero sallolinta duka biyu sannan ya tshi ya jasu suka yi wata raka'ah biyu ,sosai yajero musu addu'o'i kusan na mintina ashirin sannan suka shafah zuwa lokacin kuwa Teemah tayi hamma yafi sau a 'kirga idanunta duk sunyi luhu-luhu.

Cemata yayi taje kitchen ta 'dauko plate da cups takawo.

Batayi musu ba kuwa ta tashi taje har wani jiri jiri takeji tsabar baccin daya ci idanunta, babu ma inda tasani acikin gidan ita dan tunda tashigo gidan bata je ko ina ba su Hannah keta shige da ficen su tana kallonsu batare data nemi sanin ko'ina agidan ba.

Ko yanzun ma da ta tashin bata da'de ba ta dawo ta e masa ita bataga kitchen 'din ba. Sai kawai ya 'mi'ke yakama hanyar zuwa itama sai ta bishi abaya, dakamsa yashiga ya 'dauko plate 'din suka dawo parlourn.

Yayi-yayi da ita taci abinci ta'ki ci sai kawai tayi kwanciyarta akan kujerar dake  gefensa tare da yin pillow da 'dan 'karamin throw pillows 'din dake kan kujerun, take sai bacci ya 'dauke ta awurin bada jimawa ba, shima be wani ci abincin ba dan shi'din ma ba ra'ayin cin abincin yake ba dama dan ita ne kuma ta'ki ci dan haka sai ya ture daga gabansa.

'Debe tarkacen yayi gaba 'daya ya mai da su kitchen sannan ya dawo ya tsaya akanta kamar ya tasheta dan ta koma 'daki amma sai ya barta ganin yanda ta saki ranta take baccin cikin kwanciyar hankali ga dukkan alamu akwana kin bata samu wani baccin kirki ba. Sai de duk da haka yana ganin kamar kayan dake jikintan zasu mata nauyi, anyways bari na barta in sun dameta ai dakanta ma zata tashi ta nemi rabuwa dasu.

Komawa bedroom yayi yawo shirin baccinsa sannan ya 'dauko pillow yazo ya jefa akan carpet for d first time arayuwarsa ya kwanta bacci ba akan gado ba.

Duk da sanyin da tiles 'din ke badawa amma haka ya daure ya kwanta awurin dan kawai ya kasance kusa da ita, domin cika amanar aya kar6a baya so hakkinta yafara hawa kanshi tun daga ranar farkon auren su.

CAPTAIN ABBASOnde histórias criam vida. Descubra agora