P15

1.4K 74 0
                                        

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍

Dedicated to all masoyan CAPTAIN
ABBAS.

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Words are seeds. They land in our hearts. Be careful what you plant and careful what you say. You might have to eat what you planted one day.

🅿 *15*

Anty ne ma ta d'anso ta kawo musu wani mishkila kad'an dan fara cewa tayi wai

"ai Kabirun ya girmewa Khadijan sosai ta yaya za'a ce shi zai aureta"

aganinta ai bai dace ba hakan.

Babu wanda ma yabi takanta a maganar tata duk dama basu san manufar maganar tata ba,Yah yusuf ne ma yad'an nuna mata cewa ai ba haramci aciki,tunda annabi ma yayi hakan kuma ba'a haramta mana ba,so bata da hujjar da zata ce hakan ba dacewa bane tunda bawai Kabirun ya shiga sahun dattawa bane,har yanzun sa amatsayin matashi yake"

Taji haushin k'in kar6ar maganar da akayi,amma dolenta ta hak'ura tayi shiru.

Ba awani d'au dogon lokaci ba aka yi bikin,sosai yah yusuf yayi k'ok'ari wajen ganin ya siya mata duk abubuwan buk'ata tare da sa hannun Alhaji muhammad amma bai yi da sanin 'yar sa ba daga shine sai yusuf d'in suka sani,ahakan ma saida ya gargad'esa akan kar ya sake yaji labari koda abakin y'arsa ne,sosai yusuf yake yabawa da karamcin wannan bawan Allah,bashi da abin rama amsa illah yayi ta masa fatan alkhairi har karshen rayuwar
shi.

Bayan angama bikin ne kabiru ya d'auki matarsa yakai ta Gomben gefen iyayensa da 'yan uwansa.

Anty kuwa sai bayan bikin Khadijan sannan ta san muhimmancinta da amfaninta agidan,dan sosai tafara shan wahala da aikin gidan,ga kuma yaronta da tun tashin sa Khadija ce ke kula dashi,yanzu kuwa abu ya dawo kanta,sai abin ya taru ya mata yawa ga rashin sabo,ga shi sam bata san k'azanta sai ta rasa yadda zatayi da rayuwarta,wuni take akan k'afarta amma still bata gane kan gidan,sai da aka samo mata mai aiki kafin gidan ya saitu mata.

Cikin hakan Allah ya d'aga kasuwancin Yah yusuf shima yazama tsayayye da kansa amma da taimakon Kabiru dansu sun san kan kasuwancin sosai,kan kace me sun zama manyan 'yan kasuwa sosai kud'i ya zauna musu.

Tunda Anty taga Khadija na shirin kamota a komai sai tafara jin k'yashi aranta,sosai take jin Kishin khadijan,dama tun farko bata so Khadijan ta auri Kabiru ba aganinta ai ya fi k'arfin aurenta shiyasa takawo suka lokacin bikin amma b samu nasara ba.

Taso da wani daban aka samu aka aura mata dan ta samu damar takasu amma sai hakan bai yiwu ba.

Son zuciya sai ya kaita ga fara
Shige-shige,amma Allah bai bata ikon cutar su ba,taso ne tashiga tsakanin auran kKhadija da mijinta amma sai Allah ya karesu da karewarsa.

Shekarar Khadija uku da aure sannan ta haifi,'danta namiji sunyi farin ciki sosai musamman dayake tad'an d'au lokaci bata haihu ba sai wannan karan,amma dayake kana naka ne Allah kuma na nashi,tun kan ayi suna yaron yakoma ga mahallici,Khadija tasha ruwan hawaye dan tana da jarabar son 'ya'ya tana murna tasamu nata kuma sai Allah ya kar6e abinsa,dakyar Kabiru ya taushe ta ta hak'ura ta dangana.

Ashekarar kuma Kabirun ya kafa cibiyar kasuwancinsa acikin garin damaturun jihar yobe,zama sai ya so ya gagare shi kullum yana cikin tafiye-tafiye.

CAPTAIN ABBASDonde viven las historias. Descúbrelo ahora