💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated_
my family😍~*2nd 2d LAST PAGE*~
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_Wishes are always granted but you just have to wait for the perfect time._
🅿 *93*
Da sassarfa ta k'arasa inda yake tsayen ta rungume shi daga 'daya gefen sa ta saki wani kuka.
Shiru Abbas yayi kawai duk da kukan da take yi 'din amma bai bi takai ba sai ya dawo da idanun sa kan fuskar Babyn yana kallo tsawon da'ki'ku fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan ya 'dan juyo da kansa 6angaren da take a kunne ya ra'da mata " what's wrong kuma?, why ar u crying ko kina taya yaron ki kukan ne?"
Teemah 'dagowa tayi ta jijjiga mai kai, sai ya 'dage gira 'daya yana kallon ta yace " to shi'din kuma kukan me yake yi? Me yasa me shi?"Kwa6a baki tayi tace " Wai fa yunwa yake ji...ni..ni kuma..maman tun 'dazu zafi yake min tsoro nake ji".
Abbas cewa yayi " Haba! haba!!, tsoro kuma kike ji?, kika iya haifan shima balle wannan, come on zo muje ki gwada bashi in gani yanzu"
Yayi maganar tare da 'karasawa cikin 'dakin, itama Teemah a hankali ta biyo bayan sa tana fa'din " Allah Yayah da zafi fah, ni gaskiya bazan iya ba".Sai yace " ka'dan zaki bashi ba da yawa ba kinji?"
Da haka ya 'karasa bakin gado ya tsaya yana jiran isowar ta, daya ke a 'darare take bin bayan san so sai bata 'karaso da wuri ba.
Tana isowa sai yayi mata nuni da bakin gadon, Teemah kam a tsorace ta zauna tana matse 'kwalla.
Shi da kansa yasa mata yaron a cinyar ta tare da dai-dai ta mata shi inda yanayi yake fa'din " ke ko tausayin sa bakiji ne?, kuma ma idan ke da kika haife sa baki bashi ba to waye zai bashi? in kuma kin daina son shi ne sai ki gaya min inje in kyautar shi wa wata wacce zata kula dashi da kyau, hakan yafi ko?Ya 'karashe yana kallon cikin idanun ta dake cike taf da 'kwalla.
Wani hawayen ne ya sake gangaro mata jin abinda ya fa'da sai ta share da 'dayan hannun ta tana sake rungumar yaron zuwa 'kirjin ta.Abbas hannun sa ya kai bayan ta yana bu'de mata Zif yace " Ni ina can kin barni da tunanin zaki iya haihuwa ko kuma akasin haka, ban sani ba ashe ke kam kina nan kina ta yiwa Baby na rowa ko?"
Sai yanzun ta bu'di baki cikin shagwa6a tace
" Ni fa ba rowa nayi masa ba"
Abbas jinjina kai yayi yace " to naji bashi in gani in dagaske ne...kin gama ai har ya gaji da kukan ya ha'kura dan haushi".Kallon sa tayi itama fuskar sa har ta dawo ja saboda rikicin kukan da yayi yanzun, a hankali ta 'daga rigar ta sama Abbas ya taya ta ri'kewa sai ta ciro maman dake saitin babyn, ya cika sosai ita kanta tana jin nauyin sa har tsoron ta6awa take yi ma.
Juyowa tayi ta kalli Abbas tare da marairaice fuska zatayi magana ya tare ta da fa'din " Zahra please......."
Tace " ni fa Allah zafi yake min"Abbas shima sai yace " ai zafin sai janye miki in ba haka ba fashewa zaiyi kin fi son haka ko?"
Jijjiga kai tayi sai yasake fa'din ".....ka'dan zaki bashi to kinji y'an matan Yayah?"
Sai ta 'daga kai sama a hankali.
Sai da ta sake 'dago babyn tare da ran'kwafawa saboda saman da maman nata yayi, da taimakon sa ta samu ta sanyawa babyn a baki, yana kamawa kuwa sai ta cije baki ta jinginu da jikin Abbas dake ta gefenta, 'ko'karin cirewa ta farayi dan zafin sosai yake ratsa ta har kan ta, Abbas na ganin haka sai yayi saurin zira hannun sa yana shafa mata saman a hankali yana jero mata "sorry sorry.. sorry babe, so sorry momma...."
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...