💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*~Dedicated to my family~ 🥰
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Never be afraid to help others in their time of need. You never know when you may need that_ _shoulder to lean on_ .🅿 *86*
Muryar ta ciki-ciki tace da Hannah " _har kin dawo_ "?
Hannah dake 'ko'karin shigowa tace " _ehh na dawo ai ban bi gida ba kawai na taho nan, bana ma sam inje ni ta rin'ka kora 'din_ _nan wai ita a dole ina barin ki ke ka'dai a gida_"
Teemah cewa tayi
" _Hmm, gaskiyar ta ne ai Hannah ba 'karya bane....._ "Hannah da sauri ta tare ta da fa'din
" _Ba wani nan naga kona zauna 'din ma baccinki kike sha ki barni ina gadinki, kuma Allah ki daina_ _baccin la'asar 'din nan kin ganki ne yanzun yanda kika zama tamkar mara lafiya fa"_Hannah ce tayi gaba sai Teemah tabiyo bayan tana me fa'din
" _ai ba lafiyar ce dani ba Hannah ko dan ban fa'da miki bane shiyasa, Allah yau ban jin da'di........._ "Maganar tata tsayawa tayi dalilin cafko hannun ta da taji Hannah tayi sai ta nuno takalman data gani a parlourn a mamakance 'kasa-'kasa tace " _ya dawo ne_ ?
Da kai Teemah ta bata amsa alamar " _ehh_ "
Hararar ta Hannah tayi tare da sakin hannun ta, Teemah kuwa sai tayi murmushi.
" _ina yake to_ ?"
Hannah ta tambaya.Teemah ma sai ta bata amsa da fa'din " _d'akinsa_ "
A takaiceHannah sai tace
" _Ki sanar dani cewa mijin ki ya dawo ne mana kika wani barni nake ta zabgawa bacci sharri_ "" _Ke kika sani ai_ "
Teemah tace tare da wucewa cikin parlourn ta kwashi takalman nasa tayi gaba dasu zuwa d'akin sa.Hannah ma d'akin Teemah ta shige da niyyan tattara kayanta ta koma gida tunda ya dawo.
Shigan Teemah d'akin nasa sai ta tarar dashi har yashiga bathroom,
kayan daya cire 'din ta kwashe ta fitar masa da wasu marasa nauyi riga arm less da 3quarter trouser dan taga idan yana gida da ire-iren su yafiya amfani.Fita tayi ta koma wurin Hannah anan ta same ta tana kan ha'da kayan ta.
Turus taja ta tsaya tana kallon ikon Allah, data ga cewa dagaske take yi kaya take ha'dawa sai ta 'dan matso tare da fa'din " _Hannah wai miye hakan kike yi ne dan Allah_ ?"
Hannah bata 'dago ba tace da ita " _inda nafi wayo zan koma ko so kike in zauna har sai mijin ki ya_ _korani kafin in tafi_ ?"
Amsa Teemah tabata da fa'din
" _Ce miki akayi zai koreki? Ko kin ta6a jin ya kori wani ma agidan sa ballantana kuma ke_ ?"" _ke nifah 'kyaleni Teemah gara na ware yafi, ya za'ayi gandamemiya dani kuma in zauna agidan amare_ ?"
Hannah na maganar tana zuge zip 'din akwatin kayanta.Teemah kam tsaki tayi cike da haushi ta koma parlour Hannah ta rakata da murmushi tana murnar yau sai kwana a gida wurin Ummah.
Teemah zama tayi a parlourn ranta duk ajagule, Bata da'de da zama a wurin ba sai gashi shima yafito cikin shigar kayan data fitar masa yana amsa waya.
ESTÁS LEYENDO
CAPTAIN ABBAS
Ficción GeneralMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...