💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*👎🏻
Wannan page 'din naku ne 'yan group *CAPTAIN ABBAS FANS 2* Allah sosai nake jin da'din Comment da conversation 'dinku ina matu'kar jin da'di, koda ace my ka'dai nake dashi nasan labarin CAPATIN ya isar, wannan page 'din naku ne kuyi yanda kuke so dashi..
🥰*Bismillahir rahmanir raheem*
_Never expect things to happen. It’s better to feel surprised than to feel_ _disappointed_ .
🅿 *81*
Rausayar da kanta tayi gefe tana kallon shi, Abbas baya son taga kamar yana matsa mata ne dan haka sai yace " _owk, zan barki kiyi amma make sure that mura na kamaki ba sassauci Anty nurse zan'kira ta ringa yi miki_ _injections har sai muran ya tafi...kin yarda_ ?
Tana jin haka ta karya mai kafa'da alamar bata yadda ba.
Abbas sakin ta yayi tare da nuna mata hanya yace
" _Toh oyah go inside!_ "Dolen ta ta shigo ciki tana 'kun'kuni 'kasa-'kasa, shima Abbas take mata baya yayi bayan ya rufe 'kofar.
Teemah 'dakin ta ta wuce cikin fushin an hanata wanka inda tana komawa 'dakin ta hau cire kayan dake jikinta dan sun ji'ke sosai.
Sai da ta cire su gaba 'daya kafin ta nemi towel ta 'daura ajikin ta sai ta shiga bathroom 'din ta ta cika bathtub da ruwa ta shige ciki afili ta furta " _in ka hana wancen ai baka isa ka hanani shiga wannan ba, mutun_ _kullum sai de ya hanaka rawan gaban hantsi.....abu ka'dan sai ya wani ce injection! Wannan da ace shine yake yin alluran ai da anshiga uku nasan da kullun sai ya min goma ko.biyar dan mugunta! "_
Ta 'karshe da jan tsaki daga 'karshe.Abbas ma a parlour ya zauna inda ya 'dau lokaci yana amsa waya sai da ya gama kafin ya wuce ciki dan watsa ruwa be ko sake bi ta kanta ba.
Teemah kuwa ta jima cikin ruwan hankalinta kwance sai da ta fara jin hanjin ta na motsi ne sannan ta fita aruwan tayi wanka mai kyau tafito.
Koda ta fito sai ta tsaya kuma ta 'debi wayarta dana Mahmud ta zauna bakin gado, layin Umar ta nema cikin wayar marigayin ta'kira shi lokacin 'karfe sha 'daya ta wuce sosai 11:42am.
Umar yayi mamaki sosai data 'kirashin ya kuma ji da'di musamman dayake shima Maman Amal na yawan damunsa
akan batun Teemah.
Nan yayi mata al'kawarin zai ha'da su da zaran ya koma gida.Cikin hanzari ta shirya tare da kwaso wayoyin harma dana Mahmud saboda sauri ta fito dan nemawa cikin ta dake 'kugin neman agaji mafita.
Turus taja ta tsaya ganin babu komai akan dinning, bata 6ata lokaci ba sai ta wuce 'dakin sa ta same shi yana sa kaya shima.
Bata damu da yanayin dayake ba ta isa wurinsa ta ha'de goshi ta ita adole tana fushi dashi tace " _Yayah nifa yunwa nake ji kuma banga komai a dinning ba_ "!
Be kalleta ba yace " _Ya za'ayi kenan_ ? _dama nace a daina kawowa ne saboda bakya ci....._ "!
Da sauri ta tare shi da fa'din " _inaci mana bagashi yanzu ma ina jin yunwa ba_ "
Kwafa yayi yana kallon da ta gira a'dage jin yanda tayi maganar, cikin salo yace da ita
" _Harda fa'da ne kuma_ ?Baki ta tura gaba ta kauda kanta tace " _Ni ba fa'da nayi ba ai yunwa nake ji ne shiyasa_ "!
![](https://img.wattpad.com/cover/183563119-288-k678533.jpg)
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...