P46

1.2K 81 3
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_If you don’t care about what people think about u, you already passed the first step of success._

🅿 *46*

Cikin firgita Teemah ta matsa baya ka'dan tare da furta _" Yah Abbas "_ asaman la66an ta.

Ganin yanda idanuwan sa suka koma tare da irin kallon da yake mata ma ka'dai abin tsoro ne ballantana kuma irin ihun da ya daka mata aka.

'Kasa tayi da idanuwanta da har sun fara 'ko'karin tara ruwa shikuwa sai ya tako ahankali zuwa gabanta tamkar wani abin arziki zai mata sai kuma yasa hannu ya 'dago habarta zuwa sama dolenta ta 'dago kannata batare da taso ba dan ita yanzu tsoro ya Abbas yake bata sak ya juya mata wani irin halitta daban mai abin tsoro.

Rintse idanuwan nata tayi da 'karfi jikin na rawa saboda lokacin da ya 'dago kannata tayi zaton sau'kar mari zataji amma kuma sai taji shiru.

Shikuwa Abbas kallon fuskar tata ya tsaya yi, sosai yaga yarinyar ta rame masa amma be tsaya yabi takan ramar tata ba sai hankalin sa ya tafi ga rintse idanuwan da tayin, haushin hakan yaji, shi tunaninshi tayi hakan ne dan bata so taga ko da fuskar ne while bahaka bane ita ta rufe idanun ne saboda tsoronsa,  tsoron ha'da idao takeyi dashi.


Sake mata fuskartata yayi sai yacigaba da 'kare mata kallo, be kawar da idanun sa daga kannata ba yace _" lover girl !_,  _" kin zaci saurayin ki ne yazo ko"?_

Be jira jin amsarta ba yajuya mata baya ya fara taku ahankali hannunsa 'daya har yanzu na acikin aljihunsa kamar an ce kuma yajuyo, sai ya dawo inda take tsayen ya cira hannunsa yaja hannunta da 'karfi.

Be zame ko'ina da ita ba sai a wajen kujera ya wani jefata da 'karfi ya tsaya akanta yana huci, ita kuwa sai ta kudun dune jikinta wuri 'daya yayin da hawayen da ya taru acikin idanunta 'dazun yasamu damar gangarowa abinsa, ci gaba tayi da zubda hawayen helplessly kanta acikin tafin hannunta.

Sau'kan duka kawai take jira awurin yah Abbas 'din dan zuwa yanzun gaba 'daya ta saduda da wannan alamarin, bata san laifin data yi masa ba, dan ita bata masa laifin komai ba a iya saninta amma ga dukkan alamu ranshi a6ace yake da ita.

Ko kuma cewa da taji akeyi anawa sojoji allura wata'kila gaskiya ne, gashi yau tashiga hannunsa Allah ne ka'dai zai 'kwace ta yau ahannunsa, ahankali cikin kukan ta fara fa'din _" Yah Abbas... dan Allah.....dan Allah kayi ha'kuri, wallahi bazan sake ba, dan Allah karka dake ni, in ka dake ni_ _mutuwa zanyi Yah_ _Abbas........"_

Ahankali take maganar dan in ba akusa da ita kake bama bazaka ta6a fahimtar me take fa'di ba saboda cikin shashsheka tayi maganar.

Shi kanshi Abbas yanda tayi sai da ta bashi tausayi amma sam yakasa jin nutsuwa acikin azuciyarsa, yakasa bawa kansa ha'kuri akan abinda yakeji, aganinsa ai shi rani masa hanakali kawai take shirin yi kamar yanda tasaba abaya, azahiri shikanshi be san laifin data yi masa ba she looks innocent, amma shi aransa ji yake tamkar wani babban laifi tayi masa da babu wanda yata6a aikata masa irin laifin akaf fa'din duniya.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now