💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_Trust is like a paper…....Once it's crumpled, it can't be perfect again…......_
🅿 *49*
Koda daddyn Abuja ya sanar da Abbas sa'kon daddyn Teemah Abbas ji yayi tamkar zuciyarsa zata fita daga 'kirjinsa ta yo waje tsabar yanda bugunta ya 'karu, shiru yayi batare da ya bawa daddyn nasa amsa ba, ha'ki'ka badan daga bakin mahaifinsa yaji maganar ba da cewa zaiyi tsantsar rainin hankali ne yasa aka za6eshi domin yayiwa Teemah wakilcin auren ta, amma sanin daga bakin mahaifinsa yaji da kuma sanin wanda yaza6e shin shiyasa yayi saurin kauda wannan tunanin azuciyarsa,
Hello!.....
Hellloo Abbas kana jina kuwa?....
hel.....Muryarsa asanyaye yace " ina jinka Daddy"!
" aww toh naji shirune shiyasa"!
Daddyn Abuja sake maimaita abinda ya fa'din yayi zaton shi Abbas 'din be ji yace dashi 'dazun ba sai de tunkan ya 'karasa maganar Abbas ya tari numfashinsa da fa'din
" Daddy abubuwane agabana masu yawa wallahi, yanzu ma shirin tafiya nakeyi zuwa Kogi state bani da wannan lokacin"!" toh ya za'ayi kenan"?
Dadyn ya sake tambayarsa.
"Daddy please ka wakilceni ko kuma kasa wani amadadina in babu matsala, zan 'kira Daddy Babban ma nayi masa bayani ""Toh shikenan ba matsala, Allah ya tsare ya rufa asiri"cewar Daddyn, da "Ameen Ameen "Abbas ya amsa masa sannan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar.
Abbas da tsaki ya cire wayar a kunnansa dan ma Daddyn Abuja yariga ya yanke 'kiran badan haka ba babu abinda zai hana shi jiyo tsakin da Abbas 'din yabi bayan wayar dashi.
Baya yakoma ya kwantar da jikinsa tare da 'daga kansa sama yana jujjuya kujerar dayake kai 'din, wani huci yake fitarwa tamkar wani wanda ya dawo daga gudun kilometre.
" kar Allah yasa a 'daura auren in de har sai ni zan bada shi, mthewww"
Ya 'karasa da jan tsaki kana ya sake 'daukan wayar yayi dialling no. tsawon mintina biyu ne ya 'daukesa a maganar yana kammalawa kuwa ya mi'ke tsaye da hanzari yafara rage kayan jikinsa.Wanka yashiga sharp-sharp ya watso ruwa ajikinsa ya fito, shiri yayi cikin kakinsa na sojoji gwanin birgewa, dan ba 'karamin kar6arsa uniform 'din keyiba, kamar kar ya rabu dasu har abada idan yasaka su.
Zama yayi dan saka socks da takalmi, yana gamawa da shirin yafito ya kulle 'dakin ko wayarsa ma be tuna ya 'dauka ba, hularsa ce kawai ya ri'ko a hannunsa ya tafi.
Taku yake cikin ta'kama da 'kasaita duk da cikin hanzari yake tafiyar amma hakan be hana bayyana isarsa afili ba, Abbas 'karshe ne wajen iya tsarawa kansa komai, ciki kuwa harda tafiya be barta abaya ba, musamman idan ya shiryo cikin uniform 'dinsa jiyake tamkar yafi kowa, jin kansa yake kamar bashi ba, alokacin jin kai da miskilancinsa 'karuwa sukeyi sosai.
Ballantana yanda yake samun girma aduk lokacin da ya fito hakan ba 'karamin birgesa yake ba, dan dayawa daga cikin sojojinsu na girmama shi, ciki kuwa harda wa'danda suka girme wa shekarunsa suka kuma fishi da'dewa a akan aikin nasu, shiyasa akowani lokaci yake godiya ga Allah da kuma daya ya tsaya tsayin daka ya jajirce dan ganin ya samu wannan matsayin daya kai 'din ayanzu.
Ko yau 'dinma daya fito daga block 'dinsa hakanne yafaru, dan duk inda ya ha'du dana 'kasa dashi sai de kaga suna 'kamewa suna mishi gaisuwar ban girma, ko kulasu ma bayyi yake wucewarsa dan abin da ke gabanshi ne damuwarsa awannan lokacin, hakan kuwa bazai hana su cigaba da sara masan ba.
Office 'dinsu direct yawuce ya nemi jin batun tafiya Kogi state 'din da aka ce zasu da kuma lokacin da za'a yi tafiyar, aka sanar dashi cewa nan da 2hrs ne tafiyan, da 'kyar ya samu yayi cancelling sunan shi aciki aka maye da wani daban inda da kanshi ya sanar da wancan 'din cewa akwai tafiya nan da 2hrs dan haka ya shirya ya taho kafin lokacin.
Uzuri sosai ya basu kafin yasamu suka cire sunan nashi da shara'din cewa ths is d first and d last da zai 'kara yin irin hakan ya kuma amincewa sannan ya 'kara da neman pass na kwana biyu.
Da yamman ranar ya baro Porthacourt ya sau'ka a Abuja, gidan babu kowa ya samu sai me gadi kawai dan daddyn sama aranar suka wuche kuma dawuri suka tafi, tafiyar motan da zasuyi daga Maiduguri zuwa Damaturu ne yasasu tafiya dawuri dan basu so dare ya same su ahanya saboda dokar da ke wannan yankin alokacin mai tsanani ce.
Kaya kawai Abbas ya canja cikin wani kaftan brown colour bayan yayi wanka tare da gabatar da sallan la'asar dake gabansa daga nan ya fita daga gidan yatafi airport da 'kyar yasamu flight 'din da zashi maiduguri 7:00pm, daga can yashiga gari yarage lokaci tare da ziyartan wani abokinsa.Koda Abbas ya sau'ka a maiduguri hotel ya nema ya yada zango dan bayajin zuwa gidan oga philip wannan karan, duk dama ba'karamin taimakonsa oga philip 'din keyi ba ko ta wajen ha'da shi da driver ma dayake yi, amma wannan karan ya gwammaci ya hau motar haya kawai yafi masa badan komai ba sai dan ji da yakeyi yanajin haushin kowa ma gani yake kowa damuwa ne.
Abbahn Mahmud da shi kanshi Mahmud 'din already sun iso da sauran abokan arzikinsu da suka zo musamman domin halartar 'daurin auren, suma ganin suna da 'dan yawa sai suka taso da wuri cikin sa'a kuwa basu samu matsala da komai ba suka iso akan lokaci kuma lafiya 'kalau, dan har sun riga Daddyn Abuja ma isowa.
Daddy acan wani guest house 'dinsa dake bayan legislative quaters ya sauke su harma da wasu ba'kinsa na nesa da suka samu damar amsa gayyatar daddyn, 'dakuna isassu ne agidan so babu wanda ya takuru da wanzuwar 'dan uwansa anan kowa ya sau'ke gajiyarsa.
Babu wanda yabi ta kan Abbas domin daddy da kansa yayi musu bayanin yanda sukayi da Abbas 'din awanni ka'dan dasuka gabata, zatonsa shi ka'dai ne yasani dan Abbas da zai masa maganan be nuna masa cewa yayiwa Daddynsa bayani ba.
Dukkansu basu damu da rashin sa agurin ba dan sunsan yanayin aikinsa bakamar su bane da su suke sarrafa kominsu yanda suka ga dama.
Mahmud ne ka'dai ya damu da rashin Abbas 'din dan tun safe yake ta trying layin Abbas 'din amma baya samunsa, da farko yayi ta 'kira ba'a 'dauka daga baya kuma not reachable, ko bayan isowarsu ma yayi ta gwadawa amma baya samunsa.
Mahmud bahaka yaso ba, yaso Abbas yakasance tare da shi awannan hidiman dan shike 'kara masa 'karfin gwiwa a kullum.
Amma dayaga be same shi ba dole ya ha'kura da nemansa fatansa de Allah yasa lafiya yake. Sai dai yasa aransa cewa matu'kar Abbas be halacci wurin 'daurin auran nan ba yace da kansa zai je har porthacourt 'din yaji dalilinsa nayin hakan bayan shine yasashi ya amince da auren tun farko.
*****
Washe gari saturday gari na wayewa kowa yafara shirin 'daurin aure.Abbas da safiyar ranar ya iso around 9:30 am, alokacin kuwa shirye shirye yariga ya kankama kowa harkar gabansa yakeyi, ta 'karamar 'kofan dake bayan gidan yashigo dan baya son kowa ya ganshi shi, gaishe-gaishen damuwan nan ma shi baso yake ba, Allah ya taimake shi babu kowa ta bayan hakan yasa cikin natsuwa ya nufi 'kofar dake kitchen wanda ita zata sada shi da ainahin 'dakunan dake cikin gidan.
Koda yashiga ma wasu mata yagani a a palourn kuma ayanda ya lura duk ba'ki ne be wayi ko 'daya daga cikinsu ba dan haka sai yayi wucewarsa ciki ya nufi 6angaren dayayi niyyan zuwa.
👎🏻
_Comment_
_Vote_
_Share_*Salmerh ce* 😍
![](https://img.wattpad.com/cover/183563119-288-k678533.jpg)
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...